Yadda batun takarar Tinubu tare da Kashim ya fara jefa APC cikin ruɗani

Asalin hoton, Presidency
Batun tazarcen shugaba Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima a matsayin mataimaki ya fara jefa jam'iyyar APC cikin ruɗani bayan abin da ya faru a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a shiyyar arewa maso gabas.
An samu ruɗani a taron da shugabannin yankin suka gudanar a ƙarshen mako a jihar Gombe bayan da shugabannin jam'iyyar APC na ƙasa suka ambaci shugaba Tinubu shi kaɗai a matsayin wanda za iyi wa APC Takara a zaɓen 2027 ba tare da ambatar mataimakinsa ba Kashim Shettima.
Matakin ya haifar da yamutsi a zauren taron, lamarin da ya sa har ta kai ga ba wa hammata iska a taron wanda ya ƙunshi shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje da gwamnonin yankin na jam'iyyar APC da ministoci da tsaffin gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar.
Tun kafin taron akwai zargin da wasu ke yi cewa jam'iyyar na yin wani yunkuri na sauya Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi takara da shugaba Bola Tinubu domin neman wa'adi na biyu a zaben 2027.
Alhaji Adamu Yahaya jigo a jam'iyyar APC a jihar Yobe ya ce an samu hargitsi tsakanin mahalarta taron na shugabannin APC a yankin arewa maso gabas.
"Rashin faɗan sunan Kashim shi ya tayar da fitana, kuma har shi shugaban jam'iyya bai ambaci sunansa ba, kuma dama akwai zargi ana son a sauya Kashim kuma ganin yadda shugaban jam'iyya ya faɗi Najeriya sai Tinubu ba tare da Kashim ba, shi ne ya fusata wasu," in ji Alhaji Adamu.
Ya ƙara da cewa: "An yi ta lurar da shugaban jam'iyyar ta APC cewa ya faɗi sunan Kashim amma bai faɗa ba, lamarin da ya kai har aka fara jifarsa da robobi da wasu da kujeru har sai da jami'an tsaro suka fitar da shi a zauren taron."
Wasu jiga-jigan jam'iyyar na APC a yankin arewa maso gabas na ganin a wajen taron ne ya kamata a nun awa mataimakin shugaban ƙasar ƙauna, kasancewar a yankinsa ake yin taron da nufin tabbatar da goyon baya ga takarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
"Muna ganin tafiya ce aka faro ta mutum biyu, da shugaban ƙasa da mataimaki, don haka su biyu ya kamata a mara wa baya," a cewar Alhaji Abdulmalik Mahmud, tsohon gwamnan jihar Bauchi, ɗaya daga cikin mahalarta taron.
Cikin wadanda suka fusata a wajen taron har da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, jihar da mataimakin shugaban kasar ya fito.
Gwamna Zulum ya tashi ya gabatar da jawabi a fusace, yana cewa "su za su zaɓi Tinubu ne da Kashim,"
Jawabin gwamnan jihar Borno da na sauran jiga-jigan APC na yanki, ya tilasta, an amince da Tinubu da Kashim a matsayin yantakarar APC a zabe mai zuwa, maimakon amincewa da Tinubu shi kadai.
Tuni aka shiga yanayi mai kama da yaƙin neman zabe a Najeriya duk da cewa saura shekara biyu wa'adin gwamnati mai ci ya kawo karshe.
Me hakan ke nufi a jam'iyyar APC
Masana na ganin irin wannan hatsaniya da aka fara gani a jam'iyyar APC ba ta zo da mamaki ba.
Masanin kimiyyar siyasa, Farfesa Abubakar Kari, ya ce dama akwai wasu a cikin jam'iyyar da suke da'awar a sauya Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da shugaba Tinubu a zaben 2027.
"Galibin wasu a yankin suna tare da Kashimn Shettima, amma akwai wasu da suke son a musanya shi, amma duk wani yunƙuri na cewa a musanya shi, zai tayar da ƙura a jam'iyyar," in ji Farfesa Kari.
Masanin y ace irin abin da ya faru a taron masu ruwa da tsaki na APC a shiyyar arewa maso gabas, manuniya ce ga jam'iyyar APC cewa duk wani yunƙuri na sauya Kashim Shettima na iya jefa jam'iyyar cikin matsala musamman a yankin.
A watan Mayu ne shugabannin APC a shiyar arewa maso yammaci da suka kunshi gwamnoni da shugabannin jam'iyyar na kasa da jihohi da 'yanmajalisar tarayya da kuma ministoci da jiga-jigan jam'iyyar su ma suka jaddada goyon bayansu ga shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Duk da cewa kawo yanzu shugaba Tinubu bai fito ya ce zai nemi wa'adi na biyu ba amma masana na ganin yadda 'yansiyasaa suka bige da batun zaɓe tun a yanzu, babban ƙalubale ne ga dimokuradiyya da kuma ci gaban Najeriya.











