Me mara wa Tinubu baya a 2027 da gwamnonin APC suka yi ke nufi?

Tinibu

Asalin hoton, Bola Tinu/X

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Alhamis ne gwamnonin jam'iyyar APC suka bayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗn takara tilo da za su mara wa baya a kakar zaɓen 2027.

Gwamnonin sun yi hakan ne a taron ƙoli na jam'iyyar karo na farko da aka yi a fadar shugaban ƙasa.

Gwamnan jihar Imo, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma ne ya miƙa buƙatar goyon bayan shugaba Tinubu, inda gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani kuma ya mara masa baya.

Daga baya kuma gwamnan ya miƙa tambayar ga taron gwamnonin domin jin ra'ayinsu, inda masu amince da buƙatar suka yi rinjaye.

Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano, CAS ya ce goyon bayan shugaba Tinubu da gwamnonin suka yi na nufin abubuwa guda uku:

APC ta rufe ƙofa

Tinubu

Asalin hoton, STATE HOUSE

Bayanan hoto, Bola Tinubu tare da jiga-jigan jam'iyyar APC jim kaɗan bayan ayyana shi a ɗantakara da gwamnonin APC suka yi

Gwamnonin sun amince da rufe ƙofa a cikin gida cewa Tinubu ne mutumin da za su zaɓa.

"A wannan kusan za a iya cewa gwamnonin sun rufe ƙofar goya wa dyk wani mutum da ke son yin takara da Bola Ahmed Tinubu. Kuma hakan na nufin gwamnonin za su yi duk abin da za su iya musamman bisa la'akari da ƙarfin da gwamnonin ke da su a jihohinsu.

Gwamnoni na da tasiri faɗa wa masu zaɓe da ake kira 'delegates' abin da ake son su zaɓa." In ji Kabiru Sufi.

To sai dai Malam Sufi ya ce a zaɓen 2023 al'amura sun sauya inda ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam'iyyar LP, Peter Obi ya samu jihohi da dama duk da cewa bai samu goyon bayan gwamnoni ba.

"Za a iya cewa sai an yi zaɓen ko kuma idan an tunkari zaɓen ne za a iya gane hakan a yanzu. Amma a baya dai musamman daga shekara ta 1999 2019, a wannan lokacin an tabbatar da cewa gwamnoni na da ƙarfin da idan suka ce suna yi to mutum na iya kai gaci. Haka idan suka ce ba sa yi mutum na iya kai wa ga nasara." In ji malam Kabiru Sufi.

Gwamnonin APC na tare da Tinubu

Malam Kabiru Sufi ya ce matakin da gwamnonin suka ɗauka ya fito da irin goyon bayan da shugaba Bola Tinubu yake da shi a tsakanin gwamnonin na APC wanda abu ne mai muhimmanci a tsarin siyasa.

"Kusan jihohin na tare da shi ɗari bisa ɗari kuma hakan na nufin da wuya gwamnonin su yi wani abu daban da abin da shugaban ƙasar ke so." In ji Malam Sufi.

Jam'iyya mai mulki ta APC dai na da gwamnoni guda 22, inda jam'iyyar PDP mai hamayya ke da gwamnoni 11 sai kuma jam'iyyun AFGA da LP da kuma NNPP ke da gwamna guda ɗaya kowacce.

Ƙalubale ga abokan hamayya

Malam Sufi ya ce goyon bayan gwamnonin na aike wa da wani muhimmnin saƙo ga masu hamayya walau dai a cikin gida ko kuma a wajen jam'iyyar.

"A cikin gida hakan ya nuna idan ƙarfinsu ya fi ƙarfin mai son kara wa da Tinubu to sai ya haƙura tun yanzu.

Ina ganin zaɓi ya rage wa abokan hamayya na cikin gida da na waje da su zauna su yi duba na tsanaki dangane da zaɓukan da aka yi a baya sai su fito da dabarun kauce wa shirye-shiryen gwamnoni domin cin zaɓe." In ji Malam Sufi.