Ko gwamnonin APC sun yi azarɓaɓin goyon bayan Tinubu gabanin 2027?

Tinubu

Asalin hoton, Bola Tinubu

Lokacin karatu: Minti 3

Masu sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya na ganin cewa gwamnonin APC sun saɓa doka wajen goyon bayan takarar Tinubu a 2027.

A ƙarshen mako ne dai gwamnoni da jagoron APC a yankin arewa maso yammacin Najeriya, suka yi wani taro a Kaduna, inda suka bayyana goyon bayansu ga takarar Shugaba Tinubu a 2027.

Farfesa Kamilu San Fagge mai sharhi kan ala'muran siyasa, kuma malami a jami'an Bayero da ke Kano, na ganin cewa abin da gwamnoni da jagororin APCn suka yi ya saɓa wa dokokin zaɓen ƙasar.

Ya ce lokaci bai yi ba da ya kamata a fara al'amuran da suka sfai yaƙin neman zaɓen kakar zaɓe mai zuwa.

Tuntuni dai aka fara shiga yanayi mai kama da yaƙin neman zabe a ƙasar duk da cewa saura shekara biyu wa'adin gwamnati mai ci ya kawo karshe.

Wani mataki da masu suka ke ganin baiken jagororin siyasar yakin arewacin ƙasar.

Jamilu Aliyu Charanchi, shugaban gamayyar mutanen arewacin Najeriya ta CNG.

"Batun 'yanbindiga kullum ƙamari ya ke yi, abu babu kyau amma a ce tun yau mutanen da ake ganin sun san darajar yankinsu, su ne suke wannan maganar.

"Wannan ya nuna babu 'yansiyasar arewa da ke yin abu ɗan Allah ko ɗan al'umma. Bukatarsu ce kawai a gabansu."

Me doka ta ce kan yaƙin neman zaɓe a Najeriya?

Dokar zaɓen Najeriya ta yi tanadi game da lokacin da ya kamata a fara yaƙin neman zaɓe a hukumance.

''Za a fara yaƙin neman zaɓe, kwana 90 gabanin ranar gudanar da babban zaɓen ƙasar''.

Haka kuma za a rufe yaƙin neman sa'o'i 24 kafin fara kaɗa ƙuri'a, kamar yadda dokar zaɓen ƙasar ta yi tanadi.

'Siyasar koɗa ubangida'

Shugabannin APC a shiyar arewa maso yammaci da suka kunshi gwamnoni da shugabannin jam'iyyar na kasa da jihohi da 'yanmajalisar tarayya da kuma ministoci da jiga-jigan jam'iyyar a taron da suka gudanar a kaduna a ƙarshen mako sun ce sun jaddada goyon bayansu ga shugaba Tinubu ne saboda manufofinsa na alheri kuma wanda suke ganin zai samar da sauyi mai dorewa ga 'yan Najeriya.

To amma masana kimiyar siyasar Najeriya irinsu Farfesa Kamilu Sani Fagge na ganin siyasa ce kawai ta koɗa ubangida don samun shiga kuma irin wannan gaggawa ta saba wa dokokin zaɓen Najeriya.

"Gaskiya akwai siyasar banbaɗanci kowa na neman samun shiga da karɓuwa saboda gwammati ta mara masa baya a zaɓe mai zuwa.

"Zan ce na gaskiya an karya kaidojin zaɓen Najeriya, saboda a bisa doka sai kwanaki 150 kafin zaɓe ake kamfen.

"Amma wani abun mamaki tun ba a je ko ina ba ana kamfe a kaikaice.

Mene ne ra'ayin shugaban kasa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To duk da cewa kawo yanzu shugaba Tinubu bai fito ya ce zai nemi wa'adi na biyu ba amma Masani kimiyar siyasar Farfesa Kamilu Fage ya kara da cewa yadda 'yansiyasaar suka bige da batun zaɓe tun a yanzu, babban kalubale ne ga dimokuradiyya da kuma ci gaban Najeriya.

"Demokuradiyyar Najeriya har yanzu ba ta samun gindin zama ba, wadanda aka zaba basa mayar da hankali wajen yiwa mutane aiki sai batun neman tazarce", in ji Kamilu Fagge.

"Kuma yadda suke yin abu kamar karfi suke son nuna wa al'umma."

A yayin dai da zaben na 2027 ke kara karatowa, takarar shugaban kasa batu ne da zai ci gaba da jan kali tsakanin yankasar.

Musamman a wannan lokaci da kusan za a iya cewa da wuya gari ya waye a Najeriya ba tare da ƴan siyasa daga jam'iyyun hamayya sun sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ba, walau dai a matakin tarayya ko kuma jihohi da ƙananan hukumomi.

Sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC da ya fi bai wa ƴan Najeriya mamaki a baya-bayan nan shi ne na tsohon ɗantakarar mataimakin shugaban ƙasa na babbar jam'iyya mai hamayya ta PDP, kuma tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Efeanyi Okowa tare da gwamnan jihar mai ci, Sheriff Oborevwori.

Bugu da ƙari, jam'iyyar mai mulki na cigaba da karɓan sabbin masu sauya sheƙa daga jam'iyyar hamayya ta PDP da NNPP.