Ra'ayi Riga: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya 03/05/2025

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Lokacin karatu: Minti 1

Ranar Ma'aikata ta Duniya rana ce da ake tattaunawa kan gwagwarmaya da sadaukarwa da ƙalubalen da ma'aikata suka fuskanta a baya da ma wadanda suke fuskanta

A wannan karon bikin ya zo a daidai lokacin da ma'aikatan Najeriya suke ƙorafin ƙarancin albashi da sauran wasu matsaloli.

Shin wane irin hali ma'aikatan Najeriya da wasu ƙasashe maƙwabta suke ciki?

Waɗanne irin matsaloli suke fuskanta?

A ina suke gani akwai sauran gyara?

Waɗannan da ma wasu batutuwan suna cikin abubuwan da muka tattaunawa a shirin Ra'ayi Riga na wannan makon.