Nawa za a cire muku ƙarƙashin sabon farashin amfani da ATM a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Babban bankin Najeriya ya ƙara kudin da yake caji a duk lokacin da ƴan ƙasar suka yi amfani da tsarin cire kuɗi ta na'urar ATM.
Farashin cirar kuɗin yanzu ya tashi daga naira 35 zuwa naira 100.
CBN ya sanar da wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken 'Sauyin kudin da ake caji na amfani da ATM', kuma sabon sauyin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayun 2025.
Bayanin da ke cikin sanarwar ya kuma nuna cewa idan mutum ya yi amfani da na'urar ATM wadda ba a jiki ko cikin banki take ba, to za a caji mutum ƙarin naira 500 baya ga naira 100 ta farko.
Ƙarin naira 500 ɗin zai tafi ne zuwa ga wanda ya samar da na'urar, kasancewar ba a cikin banki take ba.
Sannan za a sanar da mai amfani da na'urar game da wannan naira 500 da za a cire a lokacin da yake ƙoƙarin cire kuɗin.
Me ya sa CBN ya yi ƙarin?
Babban Bankin Najeriya ya ce ya yi ƙarin ne domin cike giɓin ƙarin kuɗaɗen tafiyar da al'amurar kamfanoni.
"A matsayin martani ga tashin farashin kaya da kuma buƙatar da ake da ita ta inganta tsarin na'urorin cire kuɗi na ATM da ayyukan banki, Babban Bnakin Najeriya ya yi ƙarin kuɗin da ake cirewa lokacin da aka yi amfani da ATM, kamar yadda yake a sashe na 10.7 na ƙa'idojin da CBN ya gindaya ga bankuna da sauran ma'aikatun da ke hada-hadar kuɗi," in ji sanarwar ta CBN.
Najeriya dai na fama da matsalar tashin farashin kayan masarufi cikin shekarun nan, wanda ake ganin ya samo asali ne daga matakan da gwamnatin Najeriya ta ɗauka a ɓangaren tattalin arziƙi.
Gwamnatin Bola Tinubu ta kawo sauye-sauye da dama a harkar kuɗi na ƙasar, kamar barin kasuwa ta tantance darajar takardar kuɗin ƙasar da kuma kundin sauya fasalin ɓangaren kuɗi na ƙasar.
Haka nan gwamnati na ƙoƙarin ɓullo da sabbin tsare-tsare a ɓangaren tarawa da raba kuɗaɗen haraji, wanda yanzu haka ke a gaban Majalisar Dokokin ƙasar.
Wannan ba shi ne karo na farko da Babban Bankin na Najeriya ke yin ƙarin kuɗaɗen amfani da na'urar cire kuɗi ta ATM a ƙasar ba.
A shekara ta 2014, bankin ya ƙara kuɗin cirar kudi ta ATM daga naira 50 zuwa naira 65.
A shekarar 2019 kuma CBN ya sake sauya tsarin inda ya tashi daga cajin naira 65 idan mutum ya cire kuɗi ta ATM fiye da sau huɗu zuwa naira 35, wanda shi ne ake amfani da shi har zuwa wannan lokaci.










