Hanyoyi biyu da za ku nemi haƙƙinku idan banki ya zare muku kuɗaɗe

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Najeriya masu ajiyar kuɗaɗe a wasu bankunan kasuwancin ƙasar na ta faman kokawa kan yadda suka ce ana cirar musu kuɗaɗe daga asusun ajiyarsu ba tare da izinisu ba, kuma babu wani ƙwaƙkwaran bayani dagan bankunan.
Wasu da muka zanta da su sun ce lamarin na ƙoƙarin kassara harkokin kasuwancinsu da na yau da kullum.
"Na je wurin mai sana'ar POS na ciri kuɗi amma jim kaɗan sai na ji ana ta zare mini kuɗi inda aka cire fiye da miliyan biyu. Na koma wurin mai POS shi ma sai ya ce min an zarar masa. Da na je bankina sai suka ce matsalar intanet ce kuma za su duba." In ji wani mai ajiya a banki mazaunin jihar Sokoto.
Misis Agnes wadda mai gidanta ya rasu kuma take fafutikar ɗaukar nauyin ƴaƴanta a Abuja, ta bayyana yadda lamarin ya shafe ta.
"Ina zaune kawai na ji saƙo a wayata. Ina dubawa sai na ga bankina sun cire min naira 58. Na je na yi musu bayani sai suka ce min wai kodai na yi sakaci da katin cire kuɗina wani ya yi amfani da shi ko kuma na ci bashin banki.
"Na ce musu ni ban ci bashi ba. Har yanzu ba su dawo min da kuɗina ba."
A baya-bayan nan, wasu bankunan kasuwanci a ƙasar suka sanar da cewar suna fuskantar matsaloli a harkokinsu na intanet, inda suka nemi afuwar abokan hulɗarsu game da wahalhalun da suke fuskanta na cire kuɗi a asusu.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Babban Bankin Najeriya CBN ya bai wa masu hulɗa da bankuna tabbacin cewa kuɗaɗensu "babu gara babu zago".
Hanyoyi biyu na kai ƙorafi
Sashen kula da koken masu hulɗa da bankuna na CBN, ya lissafa wasu hanyoyi da suka kamata masu ajiya a banki za su iya kai kokensu idan aka samu irin wannan matsala domin neman haƙƙinsu.
Ga hanyoyin da CBN ya lissafa a shafinsa na intanet kamar haka:
- A fara tuntuɓar banki: Babban bankin na Najeriya ya ce a 2011 ya umarci kowanne bankin kasuwanci a faɗin ƙasar ya buɗe sashen sauraron ƙorafe-ƙorafen jama'a. Dole ne mutum ya kai ƙorafin nasa ga bankin nasa, inda ake sa ran za a magance matsalar a cikin mako biyu ko ƙasa da haka.
- Rubuta ƙorafi ga CBN: Bayan makonni biyu, idan bankin naku bai ɗauki wani mataki mai gamsarwa ba to sai a dangana ga sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na CBN ɗin.
Ta yaya za a rubuta ƙorafi zuwa CBN?
Shafin ya yi bayani dalla-dalla kan hanyoyin da suka dace a bi wajen rubuta masa ƙorafi.
Cikinsu akwai rubuta saƙon imel ga wannan adireshin [email protected]. Ko kuma rubutacciyar wasiƙa ga wannan adireshin (Director, Consumer Protection DepartmentCentral Business District, Abuja).
Dangane da yadda za a aike da rubutacciyar wasiƙa kuma, shafin ya zayyana cewa masu ƙorafin za su iya kai wasiƙar da suka rubuta zuwa hedikwatar CBN da ke Abuja, ko kuma a kowane reshen babban bankin a faɗin ƙasar.
Sashen ya nemi masu ƙorafin da su fayyace ƙorafinsu a wasiƙar tasu, inda ya ƙara haske dangane da abubuwan da ya kamata wasiƙar ta ƙunsa kamar haka:
- Suna
- Adireshi
- Lambar tuntuɓa
- Adireshin imel
- Sunan banki
- Lambobin asusu da suka haɗa da lambobin sirri
- Bayani kan lokacin da aka cire muku kuɗi
- Yawan kuɗin da aka zare muku
- Shaidar cire muku kuɗin
- Shaidar da ke nuna an kai ƙorafi banki kafin kai wa CBN

Asalin hoton, Getty Images











