Yadda wasu bankuna ke cirar kuɗaɗen ƴan Najeriya ba izini

A baya bayan nan yan Najeriya da dama na ta kokawa game da wannan matsala

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ..
Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya masu ajiyar kuɗaɗe a wasu bankunan kasuwancin ƙasar, sun koka kan yadda suka ce ana cirar musu kuɗi daga asusun ajiyar kudin su ba tare da izinisu ba, kuma babu wani ƙwaƙkwaran bayani dagan bankunan na su.

Wasu da muka zanta da su, sun ce lamarin na ƙoƙarin kassara harkokinsu na yau da kullum da na kasuwanci.

A baya-bayan nan dai wasu bankunan kasuwanci a ƙasar suka sanar da cewar suna fuskantar matsaloli a harkokinsu na intanet, inda suka nemi afuwar abokan hulɗarsu game da wahalhalun da suke fuskanta na cire kuɗi a asusu.

Sai dai da alama har yanzu babu wani ƙarin haske da aka yi wa wadan aka cirarwa Kudaden ba tare da izinin mai ajiya ba.

Wata mata mai suna Misis Agnes Egbugbe, da ke ajiya a wani bankin kasuwanci, a Abuja babban birnin Najeriyar, , ta yi ƙirarin cewar sama da wata ɗaya kenan da aka zare mata kuɗi a asusun ajiyarta da ke daya daga cikin bankunan kasar.

Ta ce, ta yi ta bibiya tsakanin bankin na ta da bankin na daban, wanda aka ce mai yiwuwa daga can ne matsalar ta samo asali, amma har yanzu ba a iya mayar mata da kuɗinta ba.

"A ranar 30 ga watan Agusta, sai kawai na ga sako a wayata cewa an cire min N58,750, ba tare da izinina ba. Abin ya faru ne a ƙarshen mako. Ranar Litinin na garzaya bankina don yin koke, bayan na yi musu bayani sai suka fara cewa da ni to Uwar gida ko kin ci bashi ne, a wani wuri? Na ce musu a'a" inji ta.

Sai dai ta ce daga bisani sai bankin nata ya tura ta wani banki, suka ce za su rubuta musu takarda, sannan suka ce ta je reshen bankin da ke Zone 4, wanda a nan ne suka sanar da ita cewar bankinta ne ya ki fada mata gaskiya, amma suna da masaniyar abin da ya faru.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi ma wani mai ajiya a wani bankin na da ke garin Sokoto da ke arewa Maso yamamcin Najeriya, Anas Ɗan Nayaba, ya ce tun a watan jiya ya fara samun matsala da bankinsa.

Ya ce a wani lokaci ya duba manhajar asusunsa kawai sai ya ga an cire masa kuɗi har naira miliyan biyu da dubu dari biyar.

A cewarsa "Na je cirar kuɗi a wajen mai POS dubu hamsin,, wanda bayan na koma gida sai na ga an ƙara cirar min kuɗi, har sau uku, nan take na koma, don ina zargin ko ya aikata rashin gaskiya, ina zuwa sai na tarar da wani shi ma, yazo da irin korafina. Anan ne me POS ɗin ya ce shi ma haka wani ya turo masa kudi amma ya ga an janye. Shi ne na je bankina na koka suka ce ga takarda na rubuta koke na, sannan suka ce da ni dukkan abin da aka cirar mun za a dawo da shi".

Haka kuma ya ce bayan ya rubuta takardar ne ya duba manhajar bankinsa, inda ya ga an sake zare masa naira miliyan biyu da rabi, kuma ba a turo masa wani sako na cewar an ciri kudin ba.

Sai dai duk kokarin da BBC ta yi na ji daga hukumar kula da ajiyar kuɗaɗe a bankunan kasuwancin Najeriya ta NDIC da babban bankin Najeriya kan lamarin hakanmu bai cimma ruwa ba.

Masu ajiyar banki kamar Anas Ɗan Nayaba a Nijeriya, za su ci gaba da zura ido cike da fargaba domin samun gamsasshiyar amsa daga hukumomi kan abin da ya faru da kuɗaɗensu, a yankin da ake ta bam baki ga miliyoyin mutane game da fa’idar kai ajiyar kuɗi, banki.