Sharuɗɗa shida na yin sulhu tsakanin al'umma da ƴanbindiga a Katsina

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyoyi da al'ummu a arewacin Najeriya na ci gaba da shiga tsakani domin tattaunawa da ƴanbindigar da ke addabar yankuna da manufar kawo ƙarshen hare-harensu da ke ci gaba da tagayyara arewacin ƙasar.
Ƙaramar hukumar Matazu ta bi sahun ƙananan hukumomin jihar 8 da ke sulhu da ƴanbindigar a jihar ta Katsina, sakamakon abin da wasu ke cewa gazawar gwamnati.
Wata ƙungiyar da ke jagorantar sulhu da yan bindiga a jihar Katsina ta bayyana irin matsayar da suka cimma da wani kasurgumin dan fashin daji a zaman sulhun da suka yi a yankin Matazu.
"Shi wannan ɗan bindiga shi ne ya nemi zaman sulhu da al'ummar garin na Matazu saboda burin zaman amana a tsakanin al'ummomi. Ya ce yana da aƙalla ƴanbindiga 1,228 a ƙarƙashinsa" in ji ɗan ƙungiyar.
Ya kuma lissafa wasu sharuɗɗan da ake tattaunawa a kai kamar haka:
- Dakatar da hare-hare a nan take ba tare da ɓata lokaci ba: Wannan na ɗaya daga cikin sharuɗɗan da al'ummar gari suka miƙa wa ƴanbindigar.
- Ajiye makamai: Al'ummar yankin da wakilcin gwamnatin ƙaramar hukuma sun buƙaci cewa dole ne ƴanbindigar su ajiye makaman da ke hannunsu. Mazauna yankin sun ce ganin irin makaman da ke hannun ƴanbindigar da ke da tayar da hankali.
- Sakin duk wanda ke hannun ƴanbindiga: Shi ma wannan sharaɗi da al'ummar garin Matazu suka gindaya cewa kafin cimma sulhu to dole ne ƴanbindigar su saki dukkannin mutanen da ƴanbindigar suka kama walau dai ƴan ƙaramar hukumar Matazu ko kuma ƴan wani garin.
- Mutunta yarjejeniya: Al'ummar garin na Matazu sun nemi ƴanbindigar da su mutunta yarjejeniyar dakatar da hare-hare kasancewar akwai wuraren da ƴanbindigar ke kai hare-hare bayan kuma an kammala cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
- Hukuma ta hukunta wanda ya saɓa doka: Wannan sharaɗi ne da su ƴanbindigar suka bayar a lokacin yarjejeniyar zaman lafiya inda suka nemi da barin hukuma ta hukunta duk wanda aka samu da laifin karya yarjejeniyar maimakon jama'a su ɗauki doka a hannunsu.
- Shiga cikin al'umma: Ƴanbindigar sun nemi da a rinƙa ƙyale su su ma su shiga cikin al'umma kamar kowa ba tare da ƙyama ko kyara ba tunda sun rungumi zaman lafiya.
Ko ana samun nasara a sasancin?
Shugaban kamfanin Beacon Consulting, Malam Kabiru Adamu ya ce ana samun sauƙi, amma a cewarsa, "na wani ɗan lokaci ne kuma akwai sauran rina a kaba."
"Idan ka duba ƙaramar hukumar Birnin Gwari, kusan shekara ɗaya ke nan ba mu ga masatalar ba kamar yadda muke gani a baya. A da ko da rakiyar jami'an tsaro ana kai hari, amma yanzu ana iya bin hanyar zuwa Birnin Gwari, kuma an buɗe kasuwanni ana cinikayya, sannan manoma sun koma gonaki, don haka idan dai don biyan buƙata ne na wani ɗan wani lokaci, lallai za a iya ce an samu."
Sai dai ya ce inda matsalar take ita ce, "mu masana muna tunanin abin da zai biyo baya ne, matakan da ya kamata a ɗauka na rage aibin da ke tattare da wannan sasanci, gaskiya ba mu ga an ɗauka ba. Yana iya yiwuwa a samu sauƙi na ɗan lokaci, amma matsala ta dawo a gaba."
Dr Kabiru ya ce yawaitar sasanci na iya halasta aikata laifuka, domin a cewarsa, "wasu za su ga cewa idan ba makami suka ɗauka ba, ba za a saurare su ba, wannan kuma hatsari ne ga ƙasa. Na biyu kuma ganin cewa masu laifi ne ake wa alfarma, wanda aka yi wa laifin kuma ba sa samun alfarma," in ji shi, wanda ya ce hakan matsala ce.
Ƙananan hukumomi da aka yi sasanci a Najeriya
- Matazu - Jihar Katsina
- Jibiya - Jihar Katsina
- Ɓatsari - Jihar Katsina
- Safana - Jihar Katsina
- Kurfi - Jihar Katsina
- Faskari - Jihar Katsina
- Ɗanmusa - Jihar Katsina
- Musawa - Jihar Katsina
- Ƙankara - Jihar Katsina
- Birnin Gwari - Jihar Kaduna











