Wane ne Anthony Joshua, ɗan damben duniya da ya yi hatsari a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa fitaccen ɗan damben nan na Birtaniya, wanda asalinsa ɗan Najeriya ne, Anthony Joshua ya yi hatsarin mota inda mutum 2 suka mutu.
Mr Joshua ya tsallake rijiya da baya da ƙananan raunuka, a hatsarin da ya faru a kan babban titin Legas zuwa Ibadan a kudu maso yammacin Najeriya, sannan tuni aka fara gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin motar.
Hotunan da aka yaɗa a intanet sun nuna Joshua mai shekara 36 cikin motar da ta yi raga-raga, kafin daga bisani a fito da shi.
Ya dai kawo ziyara Najeriya inda yake da dangi, bayan doke abokin karawarsa Jake Paul a wasan da suka kara a farkon watan nan.
Mutum biyu sun rasu

Asalin hoton, Federal Road Safety Corps
Hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya ta ce hatsarin ya rutsa da mutum biyar dukansu maza, "biyu sun rasu, guda uku sun ji rauni suna asibiti."
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ƙara da cewa an ceto Anthony Joshua da ransa, amma ya ji raunuka, sannan "yana asibiti ana duba lafiyarsu."
Wani ɗan uwan Anthony Joshua da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana wa BBC cewa sun kaɗu da samun labarin hatsarin.
"Muna fata ya samu sauƙi cikin sauri, sannan muna jaje ga iyalan waɗanda suka rasu," in ji shi.
Me ya haifar da hatarin?

Asalin hoton, Federal Road Safety Corps
Hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya ta tabbatar da hatsarin tare da cewa suna gudanar da cikakken bincike.
Sai dai hukumar ta ce bincikenta na farko-farko ya nuna cewa akwai alamar motar Jeep ɗin ta yi gudun wuce ƙima ne.
"Ita Jeep ɗin baƙa (wadda su Anthony Joshua suke ciki) ne take tafiya da gudun wuce ƙima, sai ta yi ƙoƙarin ratse, inda aka rashin sa'a ta ƙwace, ta je ta bugi babbar motar da ke ajiye a bakin titi."
Wane ne Anthony Joshua?
An haifi Anthony Oluwafemi Olaseni Joshua ne a ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 1989.
Danginsa sanannu ne a Sagamu kuma tushensu ya ɗauki shekaru da dama a wannan yanki.
Kakansa shi ne Daniel Adebambo Joshua, attajiri ne da ke kasuwancin gidaje, kuma ɗan kasuwa ne wanda aka yi imanin cewa ya samu sunansa na karshe ne sakamakon rikiɗa da ya yi zuwa addinin kirista.
Daga baya sai Daniel ya tura ɗaya daga cikin ƴaƴansa Isaac Olaseni Joshua zuwa Birtaniyya domin yin karatu, kuma daga ƙarshe ya auri wata mata ƴar ƙasar Ireland wacce ta dawo tare da shi zuwa Najeriya inda suka haifi ƴaƴa bakwai.
Sai ɗaya daga cikin yaran wato Robert wanda kuma shi ne uba ga Joshua da ƴar uwarsa Jenet, ya auri Yeta Odusanya, ita ma daga Sagamu.
Sunansa na tsakiya shi ne Olaseni da aka sanya masa domin girmama kakansa. Don haka shahararsa a fagen wasanni ta sake ɗaga sunan dangin nasu, ba ma a ƙauyen kawai ba, har ma da ƙasar baki daya.











