Chelsea ta dauki Benoit Badiashile daga Manaco

Chelsea ta dauki dan wasan bayan Manaco Benoit Badiashile kan kwantaragin shekara bakwai da rabi.

Badiashile mai shekara 21 ya kwashe shekara biyar a gasar Ligue 1 ta Faransa tare da Manaco, kuma ya buga mata wasa 135.

Dan wasan bayan, wanda ya fara bugawa Faransa a babban matsayi a watan Satumbar da ya wuce a wasanta da Australia, ya koma Chelsea ne kan kudi fan miliyan 35.

“Ina matukar farin cikin tsintar kaina a Chelsea. Zan ji dadin bugawa kungiyar wasa,” in ji Badiashile.

“Ban san yadda zanji ba idan na bude idanuna na ga magoya baya na ihu a gasar da ta fi kowacce a fadin duniya.”

Dan kasar Faransan ya buga gasar zakarun turai ta Champions da Europa a Manaco, inda ya buga mata kimanin wasanni 150 a duka gasar.

“Muna farin cikin zuwan dan wasa Benoit Chelsea,” in ji shugaban kungiyar Todd Boehly.