Ana bincike kan gobarar da ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira a Bangladesh

Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a Bangladesh na bincike kan abin da ya janyo wata gagarumar gobara a sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya, lamarin da ya raba mutane 12,000 da wurin kwanansu.
Babu hasarar rayuka amma gobarar ta kona tantuna fiye da 2,000 sannan ta kama ci ganga-ganga, in ji wani jami'i.
'Yan sanda na binciken lamarin a matsayin abin da aka aikata da gangan, kuma tuni aka kama wani mutum da ake zargi.
Sansanin da ke kudu maso gabashin Bangladesh shi ne sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya.
Galibin musulman Rohingya su miliyan daya ne a cikin sansanin wadanda suka tsere daga Myanmar saboda gallaza musu.

Asalin hoton, STR/EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
A ranar Litinin mutane suka koma sansanin domin ganin irin ta'adin da gobarar ta yi.
"Tantuna 2,000 sun kone sannan 'yan asalin Myanmar su 12,000 ba su da wajen kwana," in ji Mijanur Rahman, kwamishina 'yan gudun hijira na Bangladesh.
An kashe gobarar cikin sa'o'i uku amma masallatai 35 sun kone da kuma ɗakunan karatu 21 a sansanin.
Sansanin 'yan gudun hijirar ya kasance matsugunin musulmin Rohingya wadanda hukumomi a Myanyar ke gallaza mawa.
'Yan Rohingya ba su da yawa a kasar ta Myanmar mai miliyoyin mabiya addinin Budda.
Tun a shekara ta 2017, 'yan Rohingya suke zauna a kasar Bangladesh a matsayin 'yan gudun hijira.













