Abin da ya sa mata ke yawan ɓarin ciki lokacin tsananin zafi

Zubaida

Asalin hoton, Khurshid Aman

‘’Na rasa 'ya'ya biyu wajen ɓari a shekaru uku da suka wuce. Rasa jariraina ta wannan hanya na da zafi sosai, abun na da ciwo’’ a cewar Zubaida.

Matar mai shekaru 30, na zaune ne a wani waje mai nisan kilomita 30 arewa da biranen da suka fi ko ina zafi a doron duniya. Jacobabad ke nan, da ke lardin Sind na Pakistan.

"A lokuta biyun, ungozomominmu na gargajiya ne ke taimaka mini'' kamar yadda Zubaida ta shaida wa BBC.

"Lokacin da na rasa jariri na biyu a bara, na sharbi kuka babu kakkautawa har tsawon kwanaki biyu."

Mijinta Abdul Aziz ya ce sai da lokacin haihuwar matarsa ya wuce ba tare da ta haife ba, daga bisani dan ya mutu a ciki.

Ranta ya dugunzuma matuka, ta yi ta tunanin cewa watakila ba za ta sake haihuwa ba, na yi ta lallashinta, su ma 'yan uwa da dangi sun yi ta lallashinta domin ta rungumi kaddara.

Ya kara da cewa Jacobabad na daya daga cikin wuraren da suka fi tsananin zafi a duniya musamman a lokacin hunturu, yanayi na kai wa maki 50.

Yanayin zafi da ɓari

Zubaida

Asalin hoton, Khurshid Aman

Wani rahoto da aka wallafa a mujallar lafiya ta British Medical Journal a baya-bayan nan ya nuna cewa yanayi a yankin na haifar da bari da haihuwar 'yan tayi bakwaini.

Sai dai masu binciken basu iya gano yawan tsananin zafin da ka iya yin illa ga 'ya’yan da ba a haifa ba.

Zubaida ba ta nemi taimakon da ya kamata ba lokacin da ta gamu da wannan matsala a baya, abin da ya sa ba za a iya cewa ga abun da ya haifar mata da hakan ba.

Likita

A yanzu, tana neman taimako daga Dakta Khurshid, domin ganin ta sake samun damar samun haihuwa.

Likitar ta ce samun matsala wajen haihuwa abu ne da ya zama ruwan dare a wannan wuri, kuma tana karuwa a lokacin bazara.

Ta fito ne daga Jacobabad kuma ta yi aiki a can kusan shekaru arba'in. Kuma ta taimaka wajen haifar dubban ‘ya’ya, amma kuma ta ga ‘ya’ya da yawa da aka haifa cikin matsala a tsawon lokacin da ta kwashe tana aiki.

Bayan da ta yi ritaya daga aikin gwamnati, yanzu Dakta Khurshid tana gudanar da nata asibitin.

Ta ce wasu mata da suka haihu sun rasa nauyinsu, babu kwari a jikinsu, saboda gamuwa da matsaloli wajen haihuwa.

Ta ce akwai ungozomomi da yawa da ke taimaka wa mutane wadanda ba su da wata kwarewa.

Tsananin zafi da yawan ɓari

mata na wanke fuska

Asalin hoton, Khurshid Aman

A wannan shekara, masu bincike na Jami'ar California sun buga sakamakon wani bincike a kan yawan ɓari, da kuma haifar jarirai da matsala a kasashe 14 masu karamin karfi da matsakaita, da suka hada da Angola, da Benin, da Burundi, da Habasha da Haiti, da kuma Malawi.

Sauran kasashen sun hada da Nepal, da Najeriya, da Philippines, da Afirka ta Kudu, da Tajikistan, da Gabashin Timor, da Uganda, da kuma Zimbabwe.

Masu binciken sun ce sun gano cewa hadarin haihuwa yana karuwa ga mata masu juna biyu da ke fama da yanayin zafi.

Ya kuma kara da cewa an samu karuwar hadarin mutuwar jarirai.

Sai dai duk da shaidar da ta nuna cewa tsananin zafi na shafar lafiya, duk da haka Jacobabad na da kayan aikin dakile wannan matsala ta tsananin zafi.

Mijin Zubaida Abdulaziz ya ce duk da haka akwai bukatar kara asibitoci da injinan samar da lantarki domin su rika aiki a lokutan da aka dauke wuta.

Ta yaya zafi zai haifar da ɓari?

Mata da miji

Asalin hoton, Reuters

Hukumar lafiya ta Burtaniya ta ce a lokutan zafi, ana samun bari, da haihuwar yara da matsaloli, domin zafin na shafar wata hanyar jini tsakanin jariri da mahaifiyarsa yayin da yake cikinta.

Sannan zafin na haifar da rikicewar yanayin jiki, kamar yadda hukumar ta ce.

Haka kuma zafin na shafar kwayoyin halittu, in ji Dr Sindana Ilango

Sauyin yanayi na nufin karuwar yanayin zafi

ana wa yaro wanka

Asalin hoton, Khurshid Aman

Wani mai bincike a Amurka ya bayar da shawarar samar da wasu na'urorin gargadi a kan yanayin da zafi ka iya kaiwa domin bai wa mutane damar daukar matakan da suka kamata.

A shekarar 2020 ne rahoton farko na Majalisar Dinkin Duniya kan ɓari ya nuna cewa akalla yara miliyan daya da dubu dari tara aka rasa ta hanyar ɓari a wannan shekara kadai ta 2019.

Kusan jariri daya ke nan cikin kowacce dakika goma sha shida a Pakistan kaɗai.

Kyakkyawan fata

mace da jariri

Asalin hoton, Reuters

Idan muka sake komawa Jacobabad, Dakta Khurshid, ta ce an samu ci gaba a asibitocin da ke karkashin kulawar kananan hukumomi, da kuma mata ke zuwa wajen kwararru domin samu kulawa.

Bayan ta tuntubi likita, Zubaida yanzu ta kaucewa fita da rana.

Bata san me ya haifar mata da tata matsalar ba, domin haka take kauce wa duk wani abu da ka iya janyo mata cikas, a kudurinta na sake samun wata haihuwa.

A cewarta muna fatan ta hanyar kiyayewa za mu sake zama iyaye a nan gaba.

Yanzu tana yawan ci, da kuma shan kayan marmari, kuma tana zaman ta a gida.

‘’Ina fatan Allah Zai sake ba mu wani dan, za mu yi murna matuka’’ in ji mijinta Aziz.