An kama 'yan matan da suka cire hijabansu yayin wani bikin wasanni a Iran

Asalin hoton, AFP
Jami'an 'yan sandan Iran sun kama wasu 'yan mata saboda sun cire hijabinsu yayin wani wasa motsa jiki.
An yi bikin ne a birnin Shiraz da ke kudancin kasar.
Cikin waɗanda aka kama har da wadanda suka shirya bikin wasannin.
Wani bidiyo da ya nuna yada aka yi bikin wasannin mai suna Go Skateboarding da ya ja hankulan daruruwan dubban masu hulda da shafukan sada zumunta.
A karkashin dokar kasar Iran da aka kafa bayan juyin-juya halin 1979, tilas mata su sanya hijabin da ya rufe kawunansu da wuyansu baya ga rufe gashin kansu.
Kafofin yada labarai na kasar sun ce 'yan sanda sun kama mutum 120 saboda ana tuhumarsu da aikata laifuka.
Laifukan da ake tuhumarsu sun hada da shan giya da rawa tsakanin maza da mata da kuma cire hijabi yayin bikin wasannin.














