Matan da tsadar rayuwa ta tilasta musu yin 'karuwanci' a Iran

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Amir Nategh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
"Ina jin kunyar abin da nake yi, amma wane zaɓi nake da shi?" a cewar Neda, wata wacce aurenta ya mutu a Tehran.
Tana aiki ne a wani shagon gyaran gashi da rana, amma da daddare ta kan fita yawon karuwanci ne, inda take sayar da jikinta don a sadu da ita ba da son rai ba sai don neman abin buƙatar rayuwa.
"Ina kasar da ba a san darajar mata ba, tattalin arzikin ya tabarbare, kudin komai na daɗa ƙaruwa a kullum," ta ci gaba da cewa "ni bazawara ce, kuma dole na kula da ɗana.
Ana samu a karuwanci, kuma a yanzu ina kokarin sayen karamin gida a garinmu. Wannan shi ne wani abun takaicin rayuwata, don kuwa tamkar ina sayar da ruhina ne.''
A 2012, Iran ta sanar da wani shirin daƙile karuwanci, amma a cewar rahoton ma'aikatu masu zaman kansu da masu bincike, adadin karuwai kullum ƙaruwa yake yi.
Masu ra'ayin riƙau na addini a Iran sun daɗe suna musanta cewa ana karuwaci a Iran.
Mahukunta na ganin karuwanci a matsayin wata hanya da kasashen yamma ke amfani da ita wajen ɓata zukatan matasa da kuma aibata mata da fadawa tarkon maza marasa mutunci.
A wasu bayanai da ba na mahukunta ba yara na ta shiga karuwanci. Wasu ƙididdiga daga ma'aikatu masu zaman kansu sun bayyana cewa a 2016 kananan yara masu shekaru 12 na karuwanci.
Wata ma'aikata mai zaman kanta (Aftab Society) ta ɗauki nauyin yi wa mata masu maye magani.
A 2019 an kiyasta cewa akwai karuwai sama da 10,000 a babban birnin kasar kuma kashi 35 masu aure ne.
A cewar Amir Mahmoud Harrichi, Farfesa a fannin walwalar jama'a a Jami'ar Tehran, adadin mata masu karuwanci ya ninku sau biyu a Tehran.
Duba da yanayin rashin aiki ga mata a Iran da kuma rashin daidaiton jinsi, ya tilasta wa mata da yawa da ke zaune cikin talauci faɗa wa karuwanci don samun kudi.
Ko da yake aikin na zuwa da manya-manyan haɗurra.
''Maza na da masaniya kan cewa karuwanci laifi ne a Iran kuma ana matukar hukunta mata, don haka suna amfani da wannan damar,'' a cewar wata mai yin karuwanci daga lokaci zuwa lokaci wadda daliba ce a Jami'ar Tehran.
"Sau da yawa yana faruwa da ni idan sun yi amfani da ni sai su ƙi biyana kuma ba ni da halin kai su ga hukuma."
Mahnaz ta ce rayuwa a Tehran na da tsada kuma yin wasu ayyukan ba zai samar mata isasshen kudi da za ta biya bukatunta ba.
'Auren jin dadi'
Biyo bayan juyin juya halin Musulunci na Iran a 1979, sabuwar gwamnatin ta kashe karuwai da dama tare da rufe duka gidajen karuwan, a wani yunkuri na halarta auren mata na wani lokaci wanda aka fi sani da auren mutu'a.
Abubuwan da suka kawo ruɗu su ne tsayin lokacin da auren zai dauka da kuma kudaden da za a biya matan.
A karkashin mulkin Shi'a a Iran an halasta auren mutu'a kuma ba a dauke shi a matsayin karuwanci ba.
Ana ta auren mutua'a a Mashhad da Qom garuruwa masu tsarki wanda yan shi'a a duk fadin duniya ke zuwa don bauta.
An nuno wa wasu faya-fayan bidiyo a shafukan sada zumunta mazan Iraq suna neman zina, inda mahukunta suka musanta cewa auren mutu'a suka yi.
A yanzu akwai kafar intanet da ke samar da auren muta'a a Iran, wanda suka hada da Telegram da WhatsApp, wani abu da kungiyar ta ce da amincewar gwamnati take aikin.

Asalin hoton, Getty Images
Wani abu da ya haddasa tsadar rayuwa a Iran da kuma karuwar karuwanci shi ne takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Iran din ka batun shirin makamin nukiliya kasar.
Tun shekarar da ta gabata hauhawar farashi a Iran ya karu da kashi 48.6. Rashin aikin yi ya karu, su kuma wanda suke aiki ba a biyansu da kyau.
A kan wannan fage an kuma samu karin maza da ke karuwanci saboda kudi masu shekaru tsakanin 20 zuwa 35.
Wani sabon abu na maza masu karuwanci na ci gaba da karuwa a mayan biranen Iran.
''Ina samun abokan ciniki na ta shafukan sada zumunta,'' ya ce. ''Yawancin matan na tsakanin shekaru 30 zuwa 40 ne. Na taba samun mai ciniki dake da shekaru 54.
Suna nuna min kulawa tare da biyan kudi mai tsoka kuma ina kwana a gidansu.
Kamyar ƙwararren Injiniya ne amma da alamu bashi da nasibi a fanin da ya karanta.
Ya ce: "Ina matukar son zama Injiniya, amma ban samu aiki ba."
"Akwai wata yarinya da nake matukar so amma ba za mu iya yin aure ba ganin ba ni da aikin yi. Ba na alfahari da abinda nake yi na karuwanci don samun kudi.
Hakika ina jin kunya, amma kuma shi ne hanyar samun kudina don ina ƙasar da wahala kawai zan iya hangowa nan gaba."
An boye sunanyen wadanda ke karuwanci a wannan aiki.











