Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza

...

Asalin hoton, reuters

Shugabannin Afirka sun yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna tsakanin Isra'ila da Gaza, su dakatar da kazamin faɗan da ya barke a ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da kungiyar Hamas ta Falasɗinu ta kai wani harin ba-zata.

Baki dai bai zo ɗaya ba a matakin da ƙasashen suka dauka game da rikicin inda kasashen Zambia da Kenya da Ghana suka yi Allah-wadai da Hamas, tare da nuna goyon baya ga Isra'ila.

Yayin da Sudan da Djibouti da Afirka ta Kudu suka bayyana goyon bayansu karara ga Falasdinawa.

Duk da yake, Isra'ila ta bunkasa harkokin diflomasiyyarta a yankin Gabas ta Tsakiya a cikin shekara goma, da kuma shirin da wasu kasashen Afirka suka yi na mayar da ofisoshin jakadancinsu zuwa birnin Kudus daga Tel Aviv.

Isra'ila ba ta da cikakken goyon baya a Afirka a wannan sabon rikici.

Tarayyar Afirka ta fada a wata sanarwa cikin harshen Faransanci da Ingilishi cewa tashe-tashen hankulan na da nasaba da "ƙin kare hakkin al'ummar Falasdinawa, musamman na kafa 'yantacciyar ƙasa mai cin gashin kanta".

“Shugaban ya yi kira ga bangarorin biyu cikin gaggawa, su kawo karshen hare-hare ba tare da wani sharaɗi ba, tare da komawa kan teburin tattaunawa don aiwatar da ƙa'idar kafa ƙasashe guda biyu da za su zauna kusa da juna da kare muradan Falasɗinawa da al'ummar Isra'ila."

Shugaban Tarayyar Afirka, Moussa Faki ya kara da cewa.

A baya, Isra'ila ta nemi shiga tarukan Tarayyar Afrika, a matsayin mai sa ido, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna su koma kan "masalahar kafa ƙasashe guda biyu" a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 7 ga Oktoba, inda ya ce ya ji baƙin cikin tashin hankalin.

Museveni dai ya karbi baƙuncin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a 2016 da kuma a 2020, a kokarinsa na kyautata alaƙa tsakanin kasashen biyu.

Shugaban na Uganda ya kuma shiga tsakani don daidaita alakar da ke tsakanin Isra'ila da Sudan a shekarar 2020.

...
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana goyon baya ga al'ummar Falasdinawa, yayin da faɗa ya sake rincaɓewa.

"Sudan na bibiyar al'amura kan rikicin da ya barke a halin yanzu a kasar Falasdinu. Sudan ta sake sabunta goyon bayanta ga tabbatar da 'yancin al'ummar Falasdinu na samun 'halastacciyar kasa.

Tana kira da a bi kudurorin kasashen duniya da kuma kare fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba." kamar yadda shafin Facebook na kamfanin dillancin labaran Suna ya ruwaito.

Afirka ta Kudu ta yi kira a tsagaita bude wuta nan take.

"Yankin na cikin matsananciyar bukatar ingantaccen tsarin samar da zaman lafiya wanda zai gabatar da kiraye-kirayen na dumbin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya a baya, na ganin an cimma masalahar kafa ƙasashe guda biyu." kamar yadda Dirco ya fada a shafinsa na Facebook ranar 7 ga watan Oktoba.

A halin da ake ciki kuma, Najeriya ta yi gargadin cewa "zagayowar tashe-tashen hankula da ramuwar gayya da ta'addancin da ake fama da shi a halin yanzu zai yi tasiri ne kawai da ci gaba da dagula lammura, da jefa fararen hula cikin wahala, waɗanda ke da alhakin kowane rikici".

Shugaban ƙasar Kenya William Ruto kuma ya bukaci bangarorin da ke rikici da juna, su sassauta gaba yayin da ake ci gaba da "samun asarar rayuka".

"Kenya tana mai da hankali a kan cewa babu wata hujja ko kadan a kan ayyukan ta'addanci, wadanda ke zama babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasashen duniya."

"Dukkan ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi abin kyama ne, kuma laifi ne maras dalili ba tare da la'akari da wanda ya aikata ba, ko kuma dalilinsa," in ji shugaban a shafinsa na X.

Ministan harkokin wajen Zambiya Stanley Kakubo ya goyi bayan Isra'ila a wata sanarwar da ya yi Allah-wadai da hare-haren Hamas.

"Muna yin Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan a kan Isra'ila, waɗanda suka haifar da asarar rayuka, ba tare da wata shakka ba, muna yin tur da duk wasu ayyukan ta'addanci da tashe-tashen hankula.

Kkuma muna ci gaba da jaddada wajabcin bin hanyoyin diflomasiyya don magance rikice-rikicen ƙasashen duniya." in ji ministan.