Takarar Biden na cikin garari bayan ya kamu da cutar korona

Biden

Asalin hoton, .

Shugaban Amurka, Joe Biden na fuskantar sabon matsin lamba kan haƙura da takara, bayan gwaji ya tabbatar yana ɗauke da cutar korona.

A ranar Laraba ne Fadar gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwar cewa shugaban mai shekara 81, ya nuna alamun cutar.

Sakatariyar yaɗa labaran shugaban, Karine Jean-Pierre, ta ce an yi wa shugaban riga-kafi kuma da alamun sauƙi.

Ms Jean-Pierre ta ce shugaban zai killace kansa a gidansa da ke Delaware yayin da zai ci gaba da gudanar da "duka harkokinsa".

Likitan shugaban, Kevin O'Connor, ya ce Mista Biden na fama da matsalar numfashi da zubar majina da tari, inda tuni ya fara shan magani.

Daga baya shugaban ya gode wa ''masu yi masa fatan alkairi'' ta shafinsa na X, inda ya ce ''zai ci gaba da yi wa Amurkawa aiki'' yayin da yake ci gaba da samun sauƙi.

Tun da farko an ga shugaban ƙasar na jawabi ga magoya bayansa ba Las Vegas a wani taron gangamin yaƙin neman zaɓe, daga baya ya soke jawabin da ya tsara gabatarwa cikin dare.

Sau biyu dai a baya gwaji na tabbatar da cutar kan shugaba.

'Yan Democrats na son Biden ya haƙura da takara

A baya-bayan nan shugaban na fuskantar kiraye-kiraye daga manyan 'yan jam'iyyarsa kan ya haƙura da takara saboda shekarunsa da kuma rashin kataɓus a muhawarar da ya yi da ɗan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump.

Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa manyan 'yan jam'iyyar Democrats biyu a majalisar dokokin ƙasar - shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan ƙasar, Chuck Schumer da shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan ƙasar Hakeem Jeffries - sun gana da shugaban asirce domin bayyana masa damuwarsu game da takarar tasa.

Ita ma tsohuwar kakakin majalisar wakilan ƙasar, Nancy Pelosi, rohotonni sun ambato ta tana shaida wa shugaban cewa ba zai iya doke Trump a zaɓen watan Nuwamba ba.

Biden na ƙoƙarin farfaɗo da farin jininsa

Shugaban ƙasar, na ƙoƙarin farfaɗo da farin jininsa tsakanin 'yan ƙasar, tun bayan zaɓen 2020 lokacin da ya kayar da Donald Trump.

Farin jinin shugaban ya sake raguwa bayan rashin kataɓus a muhawararsa da Donald Trump a watan da ya gabata.

Tuni dai takarar shugaban ƙasar ta gamu da cikas tsakanin 'yan wasu majalisar dokokin jam'iyyarsa, inda da dama ke kiran shugaban ya haƙura da takara saboda matsalar yawan shekarunsa.

Kusan 'yan siyasar Democrats 20 ne kawo yanzu suka buƙaci shugaban ya haƙura da takara a makonnin baya-bayan nan, ciki har da ɗan majalisar daga jihar California, Adam Schiff, wanda ya ce yana cike da shakku in shugaban zai iya doke Donald Trump a zaɓen.

Cikin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta BET, Shugaba Biden ya ce zai duba yiwuwar haƙura da takara ne kawai idan ɗaya daga cikin likitocinsa ya ba shi shawarar hakan bisa ''sharaɗin lafiya''.