Wane ne ya fi nuna bajinta a muhawara tsakanin Biden da Trump?

Asalin hoton, CNN
Joe Biden da Donald Trump sun caccaki juna a muhawara ta farko mai zafin gaske da suka gudanar kan wanda yafi cancanta yayi nasara a zaben shugaban kasa na 2024.
Mutanen biyu sun tattauna kan batutuwa da dama kama daga, batun zud-da-ciki, da tattalin arzikin kasa da harkokin ketare. Sun kuma zage juna tas, da zarge-zarge da nunawa juna yatsa.
Kafin muhawarar ta yammacin Alhamis, Amurkawa da dama na nuna damuwarsu akan shekarun Joe Biden da kuma koshin lafiyarsa.
Kuma ko a yanzu wannan muhawarar ba ta sauya wannan tunani nasu ba, face sake dulmiyar da mutane cikin tunanin cancantar Biden a wannan kujerar.
Shugaban ya shiga filin muhawarar da rashin karsashi, yana magana yana hardewa. Yawanci ba a ma fahimtarsa.
Ana tsaka da muhawarar, kwamitin gangamin yakin neman zabensa suka sanarwa ‘yan jarida cewa shugaban na fama da mura – a kokarin fahimtar da mutane kan dalilan da suka sa muryarsa ta sauya.
To babu shaka haka na isa kasancewa gaskiya, amma babu mamakin neman uzuri ne.
A tsawon mintoci 90 da suka shafe ana tafka muhawara, kusa a zaune Joe Biden yake a kan kujera. Akwai ma lokacin da kamar ya rinka manta abin da zai ce, haka kuma ya rinka maimaita wasu abubuwan da ba a bukatarsu.
Tsohuwar daraktar yada labarai ta Mista Biden, Kate Bedingfield a lokacin wata tattauna da CNN bayan kammala muhawarar, ta rinka sukar shugaban da bayanai kan yadda abubuwa suka kasance tana cewa hakan bai kamaci Joe Biden ba.
Ta ce abin da aka so ya tabbatarwa duniya shi ne yana da karfi da cikakken lafiya, wanda hakan ya gaggare shi.
A lokacin da muhawarar dau zafi mai tsannai, an jiyo Mista Biden na kai waTrump hari a kokarin sauya alkabilar tattaunawar. Lamarin da ya tunzura tsohon shugaban ya rinka mayar da martani masu zafi da caccakarsa.
Wasu abubuwa da suka fito a wannan muhawara su ne batun tattalin arziki da baki ‘yan ci-rani – wanda kuri’ar jin ra’ayi ke tabbatar da cewa Amurkawa sun fi yarda da tsare-tsaren Donald Trump.
Trump din da ba a saba gani ba
Tsohon shugaban ya fi nuna kamun kai da da’a a lokacin muhawarar. Ya yi kokarin kaucewa duk wani yanayi ko dabi’u da suka yi tasiri a makamancin wannan muhawara da suka gudanar a shekara ta 2020, kuma ya rinka juya maganganunsa yana kai wa Mista Biden hari da habaici a duk lokacin da ya samu dama.
Ya rinka dauko batutuwa da kare hujojjinsa da wanke kansa, amma Mista Biden ya gaggara ci masa ko kare kansa.
Da aka koma batun zub-da-ciki, nan take, tsohon shugaban ya ce wannan batu akwai tsatsaura ra’ayi irin na ‘yan Democrats a ciki, Ya ce babu gaskiya kan cewa Democrats na goyon-bayan zubda ciki bayan haihuwa.
Batun zub-da-ciki abu ne da ya jima da ake yiwa kallon kalubale ga Trump da jam’iyyarsa ta Republican tun bayan kai batun kotun koli a 2022. Amma Mista Biden bai yi hubbasa wajen kare kai da kawo hujoji masu karfi da zasu gamsar ba.
‘Ban yi badala da fittaciyar mai haskawa a fina-finan batsa ba'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A lokacin wata tattaunawa jim kadan bayan kammala muhawarra, Mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris tace da farko shugaban ya dan nuna sanyi jiki da rauni, amma daga karshe ya nuna bajinta.
Kodayake wasu za su ga kamar tayi hakan ne domin jadadda kwarin-gwiwa, amma zance na gaskiya Mista Biden ya dan yi kokarin inganta salon amsoshinsa kafin a kammala muhawarar.
Akwai lokacin da Mista Biden ya yiwa Donald Trump fata-fata kan zargin alaka da mai shirin batsa Stormy Daniels, sannan yace tsohon shugaban nada hallaye irn na maguna.
Sai dai Trump ya mayar da martani cewa; “Ban yi badala da mai fitowa a shirin batsa ba”.
A wani bangaren kuma Trump ya kasance ba shi da manyan hujojjin kare kai kan harin da aka kai ginin majalisa a ranar 6 ga watan Janairu. Yayi kokarin juya abun da daura laifi da zarge-zarge kan shugaba Biden, wanda shi ma bai raga ba domin ya tsaya tsayin-daka tare da kafa hujojji masu karfi.
Sannan tsohon shugaban yaki yarda tare da kaucewa duk wai yunkuri na amsa cewa ya amince da sahihancin zaben Amurka na 2024.
Me zai faru nan gaba?
Wannan muhawara ta sha bamban da wanda aka saba gani a baya, ana iya cewa tawagar Biden sun samu abinda suke so. Dalili kuwa shi ne sun yi kokarin ganin mutane sun mayar da hankali a kan Trump a wannan lokaci, da kuma tuna abubuwan da ya aikata da hargitsi a zamaninsa na mulki.
Sai dai a yanzu batun zai karkata ne kan salon amsoshin Mista Biden a wannan muhawara maimakon tunanin abubuwan da Trump ya aikata a baya.
Sannan wani abu da tawagar Biden ke kauracewa a muhawarar shi ne samun lokacin da dan takararsu zai farfado. Wannan ne kawai abin da suke gani zai basu natsuwa bayan abin da duniya ta shaida a daren Alhamis.
A watan Agusta mai zuwa, Democrats za su gudanar da babban taronsu, inda za su yi kokarin sake bijiro da wasu tsare-tsaren da ake fatan za su bai wa Biden dama a karo na biyu.
Sannan za a sake wata muhawarar a cikin watan Satumba, idan hakan ya tabbata to shi ne zai bai wa Amurkawa alkibila kafin rannar zabe a watan Nuwamba.
Amma ‘yan democrats da dama na tunanin yadda karawar a karo na biyu za ta kasance, shin hakan zai sauya tunanin da ake da shi kan Mista Trump? Sannan akwai wadanda ke ganin ya kamata a soma tunanin wanda yafi dacewa da wannan kujerar.
Kwamitin gangamin yakin neman zaben Biden na da wata biyu da rabi domin lafar da wannan kura. Kuma za a sha gwagwarmaya idan har aka kai gabar da Democrats za ta bukaci sauya dan takara.
Da BBC ta yi tambaya kan yiwuwar maye gurbin dan takarar shugaban kasa ga kwamitin yakin neman zaben Bide, sai mataimakin kwamitin ,Quentin Fulks, ya nuna a yanzu babu wannan maganar.
Martaninsa na nuna cewa “Shugaba Biden ne zabin Democratic, sannan Shugaba Biden zai lashe wannan zabe,”.
Idan Mista Biden ya iya tattaro kan al’umma a ‘yan kwanakin da suka rage masa, babu mamaki a ga sauyi. Donald Trump shi kansa na nunawa duniya cewa dan siyasa na iya fadawa matsala kuma ya fito da karfinsa nan gaba.
Bayan muhawarar daren Alhamis, ‘yan democrats da dama sun shiga cikin yanayi na shaku da rashin tabbas kan nasararsu a zaben Nuwamba.












