'Watanmu uku babu intanet a yankunanmu'

Asalin hoton, getty image
Al'ummar wasu garuruwan arewacin Zamfara da ke Najeriya, na ci gaba kokawa akan katsewar Internet a wasu yankunansu tsawon wattani uku ba tare da sanar da su dalilan da ya sa hukumomi suka ɗauki matakin hakan ba.
Al'ummar kananan hukumomin Kauran Namoda da Shinkafi da Zurmi da kuma Birnin Magaji, sun ce rashin intanet din ya jefa su cikin tsaka mai wuya.
Mazauna wadannan yankuna sun ce rashin intanet din ya sanya ala tilas suna tsallakawa zuwa yankunan makwabtansu kafin su samu intanet don biyan bukatunsu.
Kwamared Abdulrazak Bello Kaura, shi ne sakataren watsa labarai na kungiyar kula da ci gaban Kauran Namoda, ya shaida wa BBC cewa, da farko matsalar ta fara da rashin iya kiran waya sai mun je har Gusau, sannan zamu iya kiran waya.
Ya ce,"To daga baya sai aka dawo ana iya kiran waya, daga nan kuma sai intanet y afara daukewa, ya zamana bama iya siyan data ballanata mu yi abu da ya shafi amfani da intanet da wayoyinmu na salula ko kuma kwamfuta."
"Ba ma iya komai sai dai mu je shagunan da ke amfani da intanet wanda suke siya don yi sana'a wanda anan idan kaje kudin da zaka biya don tura wani sako ko amfani da intanet din ta sun a wani kankanin lokaci na da yawan gaske." In ji shi.
Kwamared Abdulrazak Bello Kaura, ya ce "Wannan matsala ta rashin intanet din ta tilastawa matasa da dama barin gari domin su je ci gaba da harkokinsu na kasuwanci da suke amfani da intanet,"
Ya ce," Matasa musamman mata da ke amfani da intanet wajen tallata wasu kaya da suke sayarwa, yanzu komai ya tsaya cak, kuma hakan ya kara haifar da matsin lamba da damuwa da talauci a tsakanin al'ummarmu."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sakataren watsa labarai na kungiyar kula da ci gaban Kauran Namodan, ya ce "Mun yi kira ga shugabanninmu tun daga kan gwamna da sanatoci da 'yan majalisar tarayya da shugabannin kananan hukumominmu, amma har yanzu babu wanda ya ce mana uffan."
Babangida A A Dogo, daga karamar hukumar Zurmi a jihar ta Zamfara, ya shaida wa bbc cewa, suna kira ga gwamnatin jiharsu da duk wani mai ruwa da tsaki da su taimaka a duba wannan matsala a magance musu ita.
Ya ce," Yanzu an riga na shiga yanayi na zamani ba a iya rayuwa sai da waya, to zarar an samu matsala da ta shafi wayar to akwai damuwa da kuma fuskantar asara."
Ko da BBC ta tuntubi babban mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai ga gwamnan jihar, Mustapha Jafaru Kaura, dangane da wannan matsala ta daukewar intanet a wasu yankuna na arewacin Zamfarar, y ace gwamnati ta nuna rashin dadinta kan wannan matsala kuma tuni aka aike da takarda ga hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC.
Ya ce," Ko da aka aike da takardar NCC ta ce sojojin Najeriya ne suka umarci kamfanonin da ke kula harkokin intanet kan su yanke intanet din a wadannan yankuna saboda dalilai na tsaro."
Mustapha Jafaru Kaura, ya ce," Wannan abu gaskiya ya gurgunta tattalin arziki da zaman takewa da kuma jin dadin al'ummomin wadannan yankuna kai ni ma har da ni saboda na fito ne daga Kauran Namoda."
" Mu fa ba wata sanarwa da jami'an tsaron Najeriya suka fitar akan batun za a dauke intanet a wadanann yankuna, don haka jama'a su ci gaba da hakuri domin gwamnatin jihar Zamfara na kokari domin ganin an dawo da intanet a wadannan yankuna."In ji shi.











