Ko ya kamata gwamnatocin Afirka su dakatar da TikTok?

Matashiya

Asalin hoton, Getty Images

A jerin wasiƙun da muke samu daga ƴan jaridar Afirka, ɗan jaridar Kenya Waihiga Mwaura ya duba ko ya kamata gwamnatocin Afirka su shiga jerin masu nuna damuwa a kan Tiktok.

Da alama ana samun ƙarin damuwa a wasu sassan duniya game da kafar sada zumunta ta Tiktok.

Gwamnatoci a ƙasashen Yamma sun fara ɗaukar matakai musamman idan aka zo ga batun tsaron muhimman bayanai, amma hukumomi a Afirka ba su fitar da isassun bayanai a kai ba, zuwa yanzu.

Manhajar ta samu karɓuwa sosai a duniya, kuma haka abin yake a wannan nahiyar.

Yadda mutane ke shafe lokaci suna duba bayanai a shafin, da tsarin ka'idojin tunkarar matsaloli ko 'algorithm' da ke tunkuɗo wa ma'abota shafin abubuwan da suka fi son gani, yana ƙara jan hankalin mutane.

Nan da nan kuma daƙiƙa ke juyewa zuwa mintuna har a shiga sa'o'i.

Wani rahoto na Reuters Institute Digital News na shekara ta 2022, ya nuna Afirka ce babbar kasuwar Tiktok, inda ake samun ƙarin matasa da ke amfani da shi domin samun sabbin labarai.

Kafar sada zumuntar mallakar wani kamfani mai alaƙa da China, ByteDance a yanzu tana samar da tallafi da kuma fage ga masu wallafa bidiyo a sassan Afirka waɗanda suka fara samun muryar bayyana ra'ayoyi.

Suna ƙalubalantar labaran yau da kullum game da nahiyar, da kuma gabatar wa duniya wani sabon ra'ayi.

.

Asalin hoton, KILI PAUL

Bayanan hoto, Masu amfani da Tiktok 'yan ƙasar Tanzaniya, Kili da Neema Paul sun zama shahararru a ƙasar Indiya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai, an bayyana damuwa a wasu sassan duniya game da tsare-tsaren manhajar da suka danganci tsare sirri.

Tiktok a baya-bayan nan yana fuskantar suka, daga ƴan majalisar dokokin Amurka da suka yi wa shugaban kamfanin Shou Zi Chew ruwan tambayoyi.

An mayar da hankali kan zargin cewa gwamnatin China na iya samun bayanan sirrin masu amfani da kafar waɗanda Tiktok ke adanawa.

Ba kawai Amurka ce ke da irin wannan damuwar ba - ƙasashe da yawa a yanzu suna haramta amfani da shafin tare da sauran shafukan sada zumunta a wayoyin ma'aikatan gwamnati saboda rashin matakan tsaro na kare bayanai.

Amma gwamnatocin Afirka ba su ce komai ba. Babu wata ƙasa a nahiyar da ta ɗauki mataki a kan Tiktok.

Da yake magana da wasu ƙwararru a nan Kenya, akwai tunanin cewa yayin da tsaron bayanan sirri, ya zama wani batu, bai kamata a mayar da hankali a kan Tiktok ba.

Kennedy Kachwanya, shugaban ƙungiyar mawallafa ta Kenya (Bake) ya tuna mana zarge-zargen da kamfanin Cambridge Analytica da ke da mazauni a Burtaniya ya yi game da bayanan masu amfani da shafin a Kenya don taimaka wa wajen murɗe sakamakon zaɓe a 2013 da 2017.

Kamfanin wanda a yanzu ya durƙushe ya ce a 2018, an ɗauke shi a matsayin kamfanin tallace-tallace, kuma yana amfani da shafukan sada zumunta domin taimaka wa abokan hulɗarsa yin nasara.

'An tattauna batun Cambridge Analytica sosai a Amurka da Birtaniya amma abin da suka yi a Kenya, misali, ba a taɓo batun ba a zaɓen 2013," in ji Mista Kachwanya.

"Ina jin cewa Kenya da Najeriya su ne wuraren gwaji a wajensu kafin a yi amfani da su a Amurka da Burtaniya."

A wajensa, zarge-zargen da Cambridge Analytica ke iya yi, ya nuna yadda kamfanoni ke iya amfani da bayanan masu mu'amala da shafin, ko dai don kasuwanci ko katsalandan ga tsarin dimokuraɗiyya, ko taimaka wa tsaron ƙasa.

Akwai kuma zarge-zargen cewa kanun labaran masu adawa da Tiktok na bayyana damuwa cewa abokan gogayyarsa na rasa kasonsu na kasuwa.

James Wamathai, shi ma daga Bake, na ganin sa ido a kan Tiktok ya samo asali ne daga farfaganda da zuzutawar da Amurka ke yi.

Ya ce "Kamfanonin Amurka na tattara ƙarin bayanai inda ya ce hankalinsu ya tashi saboda da alama sun kasa goga kafaɗa da Tiktok".

Akwai wata fargabar game da bai wa masu amfani da shafin tsaro da kuma yiwuwar ganin abin da bai dace su gani ba.

Gift Mirie, wani mai kula da kamfanin fasahohin zamani da ke Nairobi wanda kuma yake kula da fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta, ya bibiyi zaman da majalisar dokokin Amurka ta yi da shugaban Tiktok.

Ya yi mamaki yadda shugaban kamfanin ɗan shekara 40 ya iya bayar da bayanai game da abubuwan da manhajar ke yi.

Mun ga yadda matasan Afirka ke saurin shiga wani abu da ake tashen yinsa a shafin - mene ne matsayarsu a wannan shirin kare tsarin 'algorithm'" kamar yadda Mista Mirie ya tambaya.

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban TikTok Shou Zi Chew ya yi wa 'yan majalisar Amurka bayani game da matakan kare matasa Amurkawa, amma ko ina makomar sauran matasan wasu sassa?

A wannan makon ma, an ga yadda wata ƙungiyar yan Senegal da ake kira Restic ta yi kira ga kamfanin ya taimaka wajen taƙaita abubuwan da matasa za su iya gani.

"Abin takaici, abubuwan da ke Tiktok suna kasancewa na tashin hankali ne wasu kuma abubuwan da ke cikin manhajar sun saɓa wa al'adunmu a nan Afirka," kamar yadda Moustapha Diakhate na Restic ya shaida wa shirin Focus on Africa na BBC.

"Muna son lallai mu ga yadda za mu kare ƴaƴanmu da ke mu'amala da wannan manhajar."

Duka waɗanda na yi magana da su, suna ganin ya kamata a fifita tsaron bayanai da samun kariya a intanet - ba tare da la'akari da inda babban kamfanin sada zumuntar da ake magana a kai yake ba.

Bayanan da masu amfani da shafin ke bayarwa kyauta, ana iya amfani da su wajen tallace-tallace. Amma a inda bai kamata ba, ana iya amfani da bayanan wajen aikata mugun nufi.