Manhajar intanet biyar da gwamnatin Najeriya ta yi gargadi kan sauke su

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa a Najeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar kan amfani da wasu manhajoji na inatanet a wayoyinsu da na’urar kwamfuta.
Sashen tsaro na hukumar Nigerian Communications Commission (NCC) ya ce ya gano wasu tagogi (extension) biyar na burauzar Google Chrome masu cutarwa, abin da ya jawo gargaɗin ke nan.
“Mutanen da ke amfani da waɗannan tagogi (extensions) ba su san irin hatsarin da ke tattare da su ba wajen satar bayanai,” a cewar kakakin NCC, Reuben Muoka game da lamarin.
Waɗanne manhajoji ne?
NCC ta ce manhajojin na bin sawun masu amfani da su a duk inda suka shiga a intanet kuma su kai rahoto.
Hukumar ta ce sashenta na harkokin tsaron kwamfuta ne suka gano hakan bisa haɗin gwiwa da tawagar bincike ta McAfee.
Manhojijn su ne:
- Netflix Party wit 800,000 downloads
- Netflix Party 2 wit 300,000 downloads
- Full Page Screenshot Capture Screenshotting wit 200,000 downloads
- FlipShope Price Tracker Extension wit 80,000 downloads
- AutoBuy Flash Sales wit 20,000 downloads
NCC ta ce an sauke manhajojin sau fiye da miliyan 1.4, waɗanda ka iya haifar wa da mutane matsala.
Wane irin haɗari manhajojin ke da su?
“Manhajojin masu haɗari na bin sawun masu amfani da su a shafukan kasuwanci na intanet sannan kuma su sauya fasafilin zaɓin mutum wato cookie,” a cewar Mista Muoka.
“Abin zai bayyana ne a matsayin wani adireshin waje. A hankali, masu manhajar za su samu wani ɓangare na kuɗin da mutum ya yi sayayya da su a intanet.”
Ya ƙara da cewa duk da Google ya goge tagogin (extension) daga shagon Chrome Web Store, abu ne mai wuya ya iya goge dukkan masu cutarwar.
Shawarar da suka bayar ita ce ga masu sauke tagogin Chrome su tabbatar cewa sun lura da kyau kafin su yi hakan.
Hanyar da za ku guje wa manhajojin:
- Goge dukkan tagogin daga burauzarku da hannunku
- Akwai buƙatar ma’abota intanet su kula da irin motsin da waɗannan tagogin ke yi
- A kula da izinin da kowace manhaja ke nama don neman su yi aiki a kan wani shafi na intanet kafin mutum ya sauke ta
Mene ne tagogin Google Chrome (Google Chrome extensions)
Tagogin Google Chrome ko kuma Google Chrome extensions manhajoji ne da ake saukewa a kan waya ko kwamfuta da ke sauya yadda burauza ke aiki.
Burauza na nufin manhajar da ake amfani da ita wajen ziyarar shafuka a intanet - Chrome ɗaya ce daga cikinsu.
Hakan ya ƙunshi ƙarawa ko sauya fasalin burauzar Chrome don sauƙaƙa amfani da ita.
Sukan ba da taimako kamar toshe tallace-tallace, da manhajoji kamar na tantance ingancin hoto.











