Fargaba game karɓar kuɗi don ba da shuɗin maki a Twitter

Elon Musk

Attajiri Elon Musk na ci gaba da jaddada matsayarsa ta fara karɓar dala $8 kan duk waɗanda ke son a maƙala masu shuɗin maki a dandalin sada zumunta na Twitter.

Cikin sauye-sauyen da ya bijiro da su bayan saye dandalin kan dala biliyan 44, Mista Musk ya ce "abu ne mai muhimmanci a yaƙi zamba".

A yanzu ana bayar da shuɗin maki akasari kyauta, wanda akasari ake bai wa manyan mutane da kamfanoni.

Matakin zai sa a kasa gane majiyoyi managarta, a cewar masu sukar sa. Mista Musk wanda shi ne mafi arziki a duniya, ya ce waɗanda suka biya kuɗin za su samu zaɓi a wurin mayar da martani (comment) da wurin neman ƙarin bayani, sannan rabi za su rinƙa gani na yawan tallace-tallace.

"Iko a hannun al'umma! Shuɗin maki dala $8 a wata," kamar yadda biloniyan ya wallafa a Twitter, yana mai sukar tsohon tsarin tantancewar.

Ya ce yana so ne ya rage dogaron da Twitter ke yi da tallace-tallace duk da cewa wasu kamfanoni sun nuna damuwa game da ɗorewar tallan a Twitter ƙarƙashin mulkinsa.

General Motors - abokin hamayyar kamfaninsa na Tesla mai ƙera motoci masu amfani da lantarki - ya ce zai daina yin tallan a dandalin.

'Masu shi ba za su biya ba, masu biya ba su cancance shi ba'

Shafin Elon Musk a Twitter

Asalin hoton, Getty Images

A wani saƙon daban kuma, Musk ya ce: "Zuwa ga masu ƙorafi, ku ci gaba da ƙorafi amma sai an biya dala $8."

Sai dai Nu Wexler, tsohon shugaban hulɗa da jama'a a harkokin ƙasashe na Twitter, ya ce biyan kuɗi domin samun shuɗin maki zai sa a kasa gane labaran ƙarya.

"Yayin da ake fama da yaɗa labaran ƙarya, tantancewa (shuɗin maki) ɗaya ce daga cikin hanyoyi da 'yan jarida, da masu bincike, da sauran jama'a ke amfani da ita wajen fayyace labaran bogi da kuma marasa inganci," kamar yadda Mista Wexler ya faɗa wa shirin BBC na Today.

"Idan ka fara ba da hayar shuɗin maki, zai zama abu mai wuya a iya gane labaran boge da kuma samun masu inganci."

James Fallows, wani mai yaɗa labarai, a Amurka ya ce ya ce ba adadin kuɗin da za a biya ne yake jawo ƙorafi ba, "abin da za a karɓi kuɗin saboda shi ne".

"Karɓar kuɗi na wata-wata: ba matsala, domin a cire talla: ba matsala, domin mutum ya samu maɓallin gyara saƙo: ba matsala," in ji shi.

"Amma shuɗin maki? Mutanen da suke shi ba za su biya ba, mutanen da suke biya ba su cancanta ba."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kazalika, shahararren ɗan jaridar Zimbabwe Hopewell Chin’ono ya tambayi Musk game da yadda za a gane waɗanda suka cancanci shuɗin makin idan aka ce sai an biya kuɗi.

"To, idan duk wanda yake da dala $8 zai iya samun tantancewa (shuɗin maki), ta yaya za a bambance waɗanda ke buƙatarsa saboda tsaro da kuma masu son sa saboda alfahari?

"Na zaci ana bayar da shi ne saboda aikin da mutum yake yi ba wai domin zai iya biya ba. Babu sauran inganci ke nan ko?"

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Tsohon tsarin da Twitter ke bi na tantancewa ko bayar da shuɗin makin ya haɗa da cike fom wanda aka tanada ga waɗanda ake yawann yi musu sojan-gona kamar taurarin fina-finai da ƴan siyasa da ƴan jarida.

Hikimar ɓullo da shuɗin maki

Kamfanin ya ƙaddamar da tsarin a 2009 bayan ya fuskanci matakin shari'a, inda aka zarge shi da gazawa wajen daƙile masu yin sojan-gona.

A cewar wani rahoton jaridar Guardian, akwai shafuka masu shuɗin maki kusan 400,000 a Twitter ya zuwa 2021.

Sai dai Mista Musk na fuskantar babban ƙalubale yayin da yake yunƙurin sauya alƙiblar harkokin kasuwancin Twitter, wanda bai samu wata riba ba a tsawon shekaru.