Abin da ya sa wayoyinku ke zafi da yadda za ku magance matsalar

Asalin hoton, Getty Images
Shin kakan zauna ka yi tunanin me ya sa a yawan lokuta idan kana amfani da wayarka ta salula, kwatsam sai ka ji ta fara daukar zafi - watakila ko kana wasa da ita ko kuma kana karantu?
Wayar takan rage sauri ko kuma batirinta ya nuna ya kusa karewa. Kana daga cikin mutanen?
A yanayi na zafi, mutane na fitar da zufa sosai, sai dai sabanin dan adam, wayoyin salula ba sa fitar da zufa, hakan yana da kyau ga wadanda ke rike da wayoyinsu amma ba shi da kyau ga wayoyinmu.
Saboda haka, me ya sa wayoyin salula ke rikidewa lokacin zafi kuma me ya kamata ku yi?
Idan ana yanayin zafi, injin waya kan rage sauri
Kamar yadda muke rasa samun sukuni lokacin yanayi na zafi, haka zai iya kasancewa ga injinan wayoyin salula, musamman ga wata na’ura da ke jikin wayar da kuma ke taimaka masa aiwatar da abin da ake so.
"Abin da ke cikin wayar da kuma ke taimaka masa wajen yin aiki, yakan dauki zafi,’’ a cewar Dr Roz Wyatt-Millington, wata babbar malama a sashen Nazarin Injiniya na kayan laturoni da ke Jami’ar Leeds Beckett a Birtaniya.
"Sannan lokacin da wayar salula ke daukar zafi, injinta zai yi kokarin tsayawa daga aiki domin kar ya yi zafi, daga baya kuma sai ya rage karfin intanet na wayar,’’ a cewarta.
Ta kuma ce an kera kayan laturoni ne domin aiki a kan ma’aunin zafi na selshiyos 35.
Daga cikar cajin wayar salula zuwa karewarsa
"Baturan wayar salula kan rike caji sosai kuma an yi su ne domin aiki a yanayin zafi da bai wuce kima ba.
Yayin da suke kara zafi, da wahala suke samu su yi aiki yadda ya kamata,’’ in ji Dr Roz.
Abin da hakan ke nufi shi ne karfin batirin wayar zai kare da wuri, musamman ma saboda da wuya yake sanyi. Dr Roz ta kara da cewa mutane suna kara karfin hasken wayoyinsu na salula a lokacin da suke waje a cikin rana, hakan kuma zai shafi yadda ke aiki.
Konewar fuskar wayar salula
Idan ba ka lura da canjin fuskar wayarka ba, yanayin zafi zai yi masa mummunan tasiri.
"Idan tsohuwar waya ce, idan ta sami karamar matsala, zafi zai kara masa matsala,’’ a cewar Dr Roz.
Ta kara da cewa abubuwan da ke kare fuskar waya, sun fi rike zafi a ciki, wanda hakan ba shi da kyau a lokacin yanayin zafi.
Abin da ya kamata ku yi domin wayarku ta yi sanyi

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kar ka yawaita saka wayar a caji
"A lokacin yanayi na zafi, idan kana cajin wayar ka, kana kara zafi ne. Idan wayarka ta dade a wuta, za ta yi zafi sosai,’’ in ji Dr Roz.
Ajiye wayar salula wajen da ya dace
"Ajiye waya nesa da rana yana taimakawa sosai. Kar ka bar waya a cikin motarka, ka ajiye ta a inuwa yadda ya kamata. Idan so samu ne, ka sanya ta gaban fanka idan za ka iya.’’
Kar ka ajiye wayar salula a cikin haske
Wannan ya shafi ciki da kuma wajen wayar. Ka cire ta daga cikin rigarta sannan ka kashe dukkan manhajoji da ba za kayi amfani da su ba.
"Idan ba ku amfani da na’urar bayar da intanet ta GPS, to ku kashe shi. Saboda an ce idan kun rage yawan manhajoji da kuke amfani da su, to hakan kuma zai rage yawan wuta da wayar ke aiki amfani da shi, kuma hakan zai rage yawan daukar zafi da waya za ta yi,’’ a cewar Dr Roz.
Yanayin karancin wuta
Idan wayarka na amfani da wuta kalilan, to hakan zai sa ta dade ba tare da samun matsala ba.
"A wasu lokutan idan wayarka tana samun matsaloli, to ka kashe ta na dan wasu mintoci, saboda ta yi sanyi, sannan sai ka kara kunnata.’’
Ku guji amfani da firiji domin ajiye wayoyinku
"Kada ka sanya wayar ka cikin kankara, saboda hakan ba zai taimaka ba.’’
Canjin yanayin zafi ba shi da kyau ga wayoyin, kuma kankara yana sa ruwa ya shiga cikin wayar.
Dr Roz ta kara da cewa wayoyi na da injunan da aka kera su da shi domin taimaka musu kada su lalace, a lokacin yanayin zafi.’’







