Shawarwari bakwai kan yadda za ku yi amfani da wayarku

Asalin hoton, Getty Images
Shin a kowace rana kana ganin mutanen da ke ɓata a kan wayoyinsu? A yanzu mutane kan iya ɓata aƙalla sa'o'i bakwai suna shiga shafukan intanet a wayoyinsu.
Wannan adadi na sa'o'i ka iya zarta haka idan aikin da kake yi na buƙatar amfani da intanet.
Mafi yawanmu munakwashe lokaci mai tsawo muna amfani da wayoyin hannu wajen gudanar da aikinmu, ko kuma muna ɓata lokaci a kan na'urorin da suka haɗar da wayoyin hannu da kwamfutoci da sauransu.
Mun kasance abin zargi kan dogara da muka yi kan fasahohin zamani, kuma ana yawan yi mana gargaɗi kan hatsarin hakan kan lafiyar jikinmu da ta ƙwaƙwalwarmu.
Wani abin mamakin anan shi ne, mukan ƙaurace wa duniyarmu zuwa duniyar intanet domin guje wa damuwa.
To sai dai a can ɗin ma mukan waɗu da wasu matsaloli na lafiyar jikinmu da na intanet.
A matsayina na mahaifi na damu da irin matsalolin rayuwa da nake fuskanta wajen aikina da kuma yadda nake gudanar da iyalaina.
Na gudanar da wani bincike na ƙashin kaina, na sauya yadda nake amfani da wayoyina, har ma littafi na rubuta kan hatsarin da ke tattare da abin da na kira ''Illolin waya''. To sai a shekarun baya-bayan nan ne waɗannan illoli ke ci gaba da bayyana.
Wannan bincike da littafi da na rubuta, sun samar da wadataccen ilimi. Domin kuwa za su taimaka wajen nuna irin tarin matsalolin da ke tattare da fasahohin zamani musamman a kan ɗan'adam.
Yana da matuƙar muhimmanci mu fayyace cewa wayoyin hannu na da matuƙa muhimmanci, musamman shiga intanet, da ilimi da nishaɗi. To amma idan aka yawanta amfani da ita, akan samu ɓullar wata matsala ga lafiyarmu.
A ƙashin kaina na gano matsalolin yawan amfani da waya kamar, tsamin idanu da ciwon wuya, da rashin samun ingantaccen barci, da damuwa da ciwon hannu duka wɗannan na daga cikin alamomin da na gano cikin shekarun da suka gabata, da na samu sakamakon yawan amfani da waya.
Don haka idan kana fuskantar wasu daga cikin waɗannan matsaloli ko ka san wani da ke fama da wasunsu, ga shawarwarin da zan ba ku domin samun damar yin amfani da waya yadda ya kamata.
1. Samun ɗabi'ar lokacin nesanta daga wayoyi
Ku samu lokacin da za ku nesanta kanku daga wayoyinku, musamman a lokutan da bakwa buƙatar amfani da su, kamar cikin dare.
Ku sayi agogon da za ku iya saita 'alarm' da shi ( Don guje wa amfani da alarm din wayoyinku) sannan ku fitar da yawowin daga ɗakunan kwananku
Za ku fi samun ingantaccen barci idan ba ku duba wayoyinku cikin dare ba. Ku guje wa ɗabi'ar kallo da wayoyinku a lokacin da za ku kwanta barci.
Ku mayar da hankalinku kan abu guda a wannan lokaci, wanda shi ne barci, ba tare da yin wani abu da zai ja hankalinku ba, musamman kallon waya.
2. Ku saita adadin lokacin amfani da waya

Asalin hoton, Getty Images
Yawaita amfani da waya kan haddasa wa mutane ciwon kai. Yi amfani da intanet yadda ya kamata don yin wasu abubuwa kamar aike wa da saƙonnin murya, wanda zai ba ku damar aike wa da saƙonninku ba tare da kun ɓata lokaci mai yawa a kan wayoyinku.
3. Ku hana waya ɗauke muku hankali
Yawan ɗauke hankali kan haifar da damuwa ga gangar jiki da ƙwaƙwalwa. Ka kashe duk wasu saƙonnin da za su iya ɗauke maka hankali idan sun shigo maka.
Sanna ku ajiye wayoyinku a kan teburi.Ajiye wayoyinku a kusa da ku ko dasuna cikin baburashin, kai ko ma a kashe suke, ka iya cutar da barcinku.
4. Samun lokacin hutun amfani da waya da rana
Yawaita amfani da waya kan haifar da damuwa da tashin hankali, don haka yana da kyau a riƙa samun lokacin hutu daga amfani da wayar.
Don haka a lokacin hutu daga amfani da wayar yana da kyau mutum ya yi sassarfa, ko ya karnta littafi, ko ya hau keke, ko wasu abubuwan da ba zu iya yin amfani da waya ba a lokacin yin su.
5. Sauƙaƙa amfani da waya
Yawan amfani da waya kan haifar maka da matsalar tsamin idanu tare da cutar da ganinka. Ku guje wa kallon abubuwa ƙanana a cikin wayoyinku, idan sun kama dole ku kale a kwamfuta ta yadda za ku iya ƙara girmansu.
Ku rage hasken wayoyinku musamman da dare, sannan ku yi amfani da sauran manhajoji masu amfani.
Ku tabbatar hasken sikirin ɗin wayoyinku bai kai yadda zai kama idanunku ba.
6. Ku yi amfani da wayoyinku ta hanyar da ta dace
Ku yi wani shiri kan wayoyinku da kwamufutocinku da sauran na'urori ta yadda za ku yi amfani da su yadda ya kamata.
Wasu manhajojin za su taimaka muku wajen gudanar ayyukanku yadda ya kamata.
Ku sauke manhajar da ke auna muku lokacin da kuke ɓatawa a wayoyinku, hakan zai razanaku.
Za mu riƙa samun damar amfani da wayoyinmu yadda muke so idan muka zama masu ɗaukar matakai.
7. Ku zauna da kyau yayin amfani da na'urori
Zama da kyau yadda ya kamata kan taimaka wa lafiyarmu a lokacin da muke amfani da na'urori, domin kuwa hakan kai kawar mana da ciwon wuya da sauran ciwuka.
Ku zauna da kyau, sannan ku riƙa miƙewa a kai a kai, sanna ku riƙa motsa jika a kai a kai, ba tare da wayarku ba.
Ku mallaki rayuwarku ta intanet
Waɗannan shawarwari bakwai za su taimaka muku wajen samun damar iko da rayuwarku da intanet.
Ni a ƙashin kaina, ina yin barci tare da sassarfa, ta hanyar barin wayata a nesa da ni.
Magana ce ta ware wa intanet lokacin da ya kamata a ɓata a cikinsa da muka lokacin da ya kamata ku yi amfani da wayoyinku.
An fara wallafa wannan maƙala a wani shafin ilimi, sannan aka sake wallafa shi ƙarƙashin wata yarjejeniyar mai ɗauke lasisi.











