Yadda cutar ƙyandar biri ke galabaita ƙananan yara

Ansima

Asalin hoton, Glody Murhabazi

Bayanan hoto, Dukkan yaran Nzigire Kanigo sun kamu da cutar mpox, ciki har da Ansima mai shekara biyu.
Lokacin karatu: Minti 3

Ƙananan yara, a gabashin Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo ne suka fi fama da annobar kyandar biri, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cutar da ke buƙatar hankalin duniya.

A ƙasar ce mafi yawan waɗanda suka kamu cutar suke, sannan ta yi ajalin sama da mutum 450.

"Cutar ta fara kamar wasa. Wani ƙaramin ƙurji ne ya fito, sai mahaifiyarsa ta matse wani ruwa yana fita. Daga nan kuma sai wani ya ƙara fitowa bayan ɗan lokaci, kuma ƙurajen bazu a sassan jiki," a cewar Alain Matabaro, wanda ya bayyana ƙyandar biri ta kama ɗansa ɗan shekara shida Amani.

Ya fara murmurewa bayan shan magani na kwana huɗu a asibitin Munigi, kuda da garin Goma da ke gabashin Kongo.

Kaso 75 na waɗanda likitoci suka diba, yara ne ƴan ƙasa da shekara 10, a cewar Dr Pierre-Olivier Ngadjole da ke aiki da wata ƙungiyar agaji ta Medair.

Yara ƙanana ne cutar ƙyandar biri ta fi addaba, saboda rauninsu.

Dr Ngadjole ya kuma ɗora laifin ga cunkoson mutane a sansaninn ƴan gudun hijira da rikici a yankin ya raba da gidajensu.

Hanya ɗaya da cutar ke saurin yaɗuwa ita ce ta cuɗanya kuma yara a tare suke yin wasa, ba su damu da bayar da wata tazara ba, kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Za ku iya gani ko a gida, suna kwanciya ne tare a gado ɗaya, za ka iya ganin yara uku zuwa huɗu har biyar, dole cutar ta yaɗu kusan a kullum."

Tun watan Yuni, asibitin Munigi da ke bayar da maganin ƙurajen fata kyauta na fama da masu cutar 310. Kuma yanzu kullum ana kwantar da tsakanin mutum biyar zuwa 10.

Babu wanda ya mutu a wurin, kuma Dr Ngadjole na ganin saboda yadda mutane ke zuwa karɓar magani.

"Ina ganin yana da kyau a samar da magani kyauta musamman a wannan yanayin, hakan na nufin mutane ba za su yi tunanin kuɗi ba, suna zuwa da wuri."

Sai dai batun ya sha bamban a asibitin Kavumu da ke tazarar kilomita 80 da kudu maso yammacin Munigi

Marar lafiya 800 aka gani tun watan Yuni kuma takwas sun mutu - dukkaninsu ƴan kasa da shekara biyar.

Officials at the hospital in Kavumu say finding enough space for everyone is a big challenge

Asalin hoton, Glody Murhabazi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Wannan cutar ta haifar muna da fargaba cewa za ta shafe mu duka," in ji Josephine Sirangunza, wata da ke zaune a sansanin Mudja tare da ƴaƴanta biyar.

Ma'aikatan lafiya na kai ziyara sansanin Mudja kusa da tsaunin Nyiragongo, domin ilmantar da mutane kan abin da za su yi idan sun ga alamomin cutar, kamar taƙaita cuɗanya da mutane.

Ta ce ya kamata gwamnati ta bayar da tallafi na kayyyakin buƙata domin daƙile bazuwar cutar.

"Idan muka ga wasu na rashin lafiya, muna damuwa sosai kan yadda za mu kare kanmu."

Wannan ra'ayi ne irin na Bosco Sebuke mai shekara 52 da ke da ƴaƴa 10.

"An wayar muna da kai kan ƙyandar biri, amma muna cike da fargaba domin muna cunkushe a matsuguninmu. Muna barci cikin muhalli marar kyau, don haka hana yaɗuwar cutar abu ne mai wahala, in ji shi.

Sabon nau'in cutar da ya ɓarke a gabashin Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo, ya bazu a ƙasashe maƙwabta.

Kongo na fatan samun rigakafin cutar daga Amurka da Japan.

Mr Matabaro, mahaifin Amani da ke murmurewa daga ƙyandar biri, ya ce yana rigakafin cutar zai kawar da cutar.

Dr Ngadjole ya ce rigakafin wata hanya ɗaya ce ta daƙile bazuwar cutar.

"Hanyar da ta fi sauƙi ita ce ta samar da muhalli mai kyau. Idan muka inganta tsafta a muhallinmu da na al'umma, zai kasance cikin sauƙi a rage barazanar yaɗuwar cutar."

Ms Sirangunza ta ce “A faɗa wa shugabanni su kawo magani da sabulu da sauran abubuwan kariya domin kaucewa yaɗuwar cutar"

Taswira