Asalin kwalara da yadda za ku kare kanku daga kamuwa da cutar

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da damuna ta wannan shekarar ta 2025 ke shirin ban-kwana, alƙaluma na nuna cewa aƙalla mutum 300 ne suka mutu a sandiyar cutar kwalara, ciki har da mutuwar mutum 179 da gwamnatin jihar Zamfara ta sanar cewa sun mutu a jihar cikin mutum 12,052 da ake zaton sun kamu da cutar a watan Satumba na 2025.

A wani rahoto da hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a ƙasar (NCDC) ta fitar, ta ce aƙalla mutum 4,778 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar ta kwalara a Najeriya a tsakanin shekarar 2020 and 2024.

Sannan duba da yanayin damuwa, akwai yiwuwar cutar kwalara ta ci gaba da yaɗuwa tare da yin illa.

Mece ce cutar kwalara?

Ƙwayar cutar kwalara
Bayanan hoto, Ƙwayar cutar kwalara

Kwalara ƙwayoyin cuta ne da ke yaduwa ta hanyar ruwa, wadda ruwa ko abinci maras tsafta ke yaɗawa.

Kwalara na haifar da gudawa da amai, kuma tana saurin yin kisa idan har ba a ɗauki mataki a kan lokaci ba.

Waɗanda cutar ta yi wa tsanani za su yi fama da rashin ruwan jiki wanda zai kai ga haddasa babbar matsala kuma idan ba a yi gaggawar magani ba mutum na iya mutuwa.

A cikakken bayanin da CDC ta yi kan kwalara ta ce kusan mutum miliyan uku ke kamuwa da cutar duk shekara kuma tana kashe mutum 95,000 duk shekara a duniya.

Ana iya kamuwa da cutar ba tare da nuna wani alamu ba, amma kuma takan iya yin tsanani.

Alƙalumman CDC sun nuna cewa mutum ɗaya cikin 10 da suka kamu da cutar kwalara za ta iya yin tsanani da nuna alamu na amai da gudawa sosai da kuma mutuwar jiki.

Tarihin kwalara

Wani zane da ke nuna yadda ƙazanta ta taimaka wajen yaɗuwar cutuka a birnin Landan cikin shekarar 1852

Asalin hoton, ALAMY

Bayanan hoto, Wani zane da ke nuna yadda ƙazanta ta taimaka wajen yaɗuwar cutuka a birnin Landan cikin shekarar 1852

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a wajen ƙarni na 19 kwalara ta bazu a sassan duniya daga Indiya.

Miliyoyin mutane ne suka mutu a sassan duniya sakamakon ɓarkewar annobar sau shida.

WHO ta ce ɓarkewar annobar karo na bakwai ta samo asali ne daga Kudancin Asia a 196, ta bazu zuwa Afirka a 1971 da kuma a yankin Amurka 1991.

Ta yaya ake kamuwa da kwalara?

...

Asalin hoton, Getty Images

Mutum na iya kamuwa da cutar kwalara ta hanyar shan gurɓataccen ruwa ko abinci.

Kuma a lokacin annobar, wanda ya harbu na iya ƙara gurɓata ruwa da abinci.

Cutar kuma na iya bazuwa cikin sauri a yankunan da ba a ɗauki matakan tsaftace ruwan sha da magudanan ruwa ba.

Sai dai kuma Hukumar CDC ta ce yana da wahala cutar ta yaɗu daga wani mutum zuwa wani, don haka mu'amula da wanda ya kamu da kwalara ba ya cikin hatsarin kamuwa da cutar matuƙar za a ɗauki matakin wanke hannu yadda ya kamata.

Mutanen da ke rayuwa a wuraren da babu ruwa mai tsafta da rashin tsaftar muhalli sun fi hatsarin kamuwa da kwalara.

Alamomin kwalara

Alamomin kwalara sun haɗa da:

  • Gudawa (ba-haya mai ruwa sosai)
  • Amai
  • Rashin ƙarfin jiki
  • Ƙishin ruwa
  • Zazzaɓi
  • Jiri

Alamomin sukan ɗauki kwana biyu zuwa uku kafin su bayyana bayan mutum ya harbu da cutar. Wani lokaci yakan kai kwana biyar kafin bayyanar cutar.

Bayanan bidiyo, Me ya sa ake shirin ayyana cutar kwalara babbar barazana a Najeriya?

Ko akwai maganin kwalara?

Likitoci sukan gudanar da bincike ta hanyar ɗaukar samfurin ba-haya domin gano idan akwai ƙwayar cutar kwalara.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa CDC ta ce yawanci ana maganin cutar ne cikin sauƙi ta hanyar bayar da ruwan gishiri a madadin ruwan jiki da mutum ya rasa sakamakon amai da gudawa.

Likitoci suna ba da sinadarin ORS mai ƙunshe da gishiri da suga da ake zubawa cikin gorar ruwa mai tsabta lita ɗaya a bai wa wanda ya harbu da cutar ya sha. Ana amfani da wannan maganin a faɗin duniya.

Idan kuma cutar ta yi ƙamari, za a buƙaci a yi wa mutum ƙarin ruwa.

Idan kuma jariri ne ya harbu da kwalara, za a ba mahaifiyar shawara ta ci gaba da shayar da shi ruwan nono.

Hanyoyin kare kai daga cutar kwalara

Kamar yadda Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Najeriya ta bayyana, hanyoyin kare kai daga kamuwa da kwalara su ne:

  • Shan ruwa mai tsafta
  • Tsaftace muhalli
  • Zubar da shara a wurin da ya kamata
  • Tsaftar jiki ta hanyar wanke hannu da sabulu da ruwa mai gudana
  • Ƙaurace wa shan kayan zaƙi (Zoɓo ko Jinja) da babu tabbas kan tsaftar su
  • Ƙaurace wa shan kayan marmarin da ake sayarwa a kan titi ba tare da rufewa ba, musamman waɗanda aka fere kamar kankana da abarba
  • Guje wa cin abincin da ba a dafa yadda ya kamata ba

Mutanen da suka fi haɗarin kamuwa da kwalara

...

Asalin hoton, Getty Images

Mutanen da suka fi saurin kamuwa da cutar kwalara su ne:

  • Mutanen da ba su iya samun ruwa mai tsafta
  • Mutanen da ke rayuwa a wuri maras tsafta
  • Mutanen da ke rayuwa a unguwanni marasa tsari
  • Mutanen da ke samun ruwa daga rafuka ko wuraren da ruwan ya gurɓata
  • Mutanen da ba su wanke hannu a lokutan da suka kamata
  • Mutanen da rikici ya tarwatsa waɗanda ke rayuwa a sansanonin ƴan gudun hijira
  • Ƴan'uwan da ke kula da waɗanda suka kamu da kwalara
  • Ma'aikatan lafiya da ke kula da marsa lafiya ba tare da kariyar da ta dace ba

Matakan wanke hannu

Ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kare kamuwa daga cutar kwalara ita ce wanken hannu yadda ya kamata, ta hanyar amfani da sabulu da kuma ruwa mai gudana.

Mataki ɗaya

Asalin hoton, Breakthrough ACTION-Nigeria

Ya kamata a wanke hannu kafin fara girki da lokacin da ake girki da kuma bayan kammala dafa abinci.

A jiƙa hannu da ruwa a lokacin da za a fara wanke hannun.

...

Asalin hoton, Breakthrough ACTION-Nigeria

Ya kamata a wanke hannu bayan shan hannu ko musabaha da wani mutum na daban.

Bayan jiƙa hannu sai a shafa sabulu a ciki da bayan hannu.

Mataki na uku

Asalin hoton, Breakthrough ACTION-Nigeria

Daga nan sai a cuɗa ciki da wajen tafin hannu.

Ya kamata a wanke hannu kafin cin abinci da bayan kammala cin abinci.

Mataki na huɗu

Asalin hoton, Breakthrough ACTION-Nigeria

Bayan kammala cuɗa hannu sai a ɗauraye da ruwa mai tsafta wanda yake gudana.

A tabbatar an wanke hannu bayan kula da maras lafiya wanda ke fama lalurar amai da gudawa.

An fara wallafa wannan labarin ne a ranar 24 ga Yunin 2024.