Abu huɗu da ke iya haifar da mutuwar fuju'a

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa yawancin mutane sun yi amanna da cewa komai daren daɗewa wata rana su, da duk wani mai rai za su mutu amma akan shiga hali na kaɗuwa da ɗimauta idan wani na kusa ya mutu ba tare da tsammani ko kuma alama ba.
A mafi yawan lokuta an fi alaƙanta mutuwa ga waɗanda ke fama da cuta ko kuma waɗanda suka tsufa.
To sai dai ba kodayaushe ne hakan ke faruwa ba, domin akan samu matasa da yara da kuma jarirai waɗanda ke rasuwa.
To amma babban abin da ya fi tayar da hankali shi ne lokacin da mutum mai lafiya da kuzari ya faɗi ya mutu ba tare da nuna wata alamar kasancewa cikin matsala ba - abin da ake kira mutuwar fuju'a.
Dakta Adamu Mohammed, ƙwararren likitan zuciya a Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto ya ce duk da cewa a zahiri al'umma ba za su ga abin da ya yi sanadiyyar mutuwar wanda ya yi mutuwar fuju'a ba, amma zai iya yiwuwa ta samo asali daga wasu cututtukan da ba su bayyana alamominsu a zahiri ba.
Akasari abubuwan da suka fi haifar da mutuwar fuju'a na alaƙa ne da matsalar gazawar zuciya ko kuma rashin isasshen jini a cikin ƙwaƙwalwa.
Dakta Adamu ya yi wa BBC ƙarin haske kan wasu larurori da suke iya haddasa mutuwar fuju'a:
Rikicewar bugun zuciya
'Arrhythmias' wani yanayi ne da ke shafar bugun zuciyar ɗan’Adam. A irin wannan yanayi zuciya kan ƙara sauri ko kuma ta riƙa bugawa a hankali sosai.
Bugun zuciyar mutum kan ƙara sauri a lokacin da yake motsa jiki ko kuma ya ragu a wasu lokutan amma idan abin ya tsananta zai iya haifar da babbar matsala.
Abubuwan da kan haifar da mummunan sauyin bugun zuciya sun haɗa da shan miyagun ƙwayoyi, sauyi mai yawa a yawan sanadarin pH a jikin ɗan’adam, da matsalar zuciya mai muni da kuma matsalar saurin bugun zuciya.
Sai dai Dakta Adamu ya ce akwai mutanen da ake haihuwar su da matsalar saurin rikicewar bugun zuciya.
Ya ce "abu kaɗan sai ya sa bugun zuciyarsu ya rikice". Ya ƙara da cewa hatta damuwa wadda ba ta taka kara ta karya ba kan iya rikitar da bugun zuciyarsu, inda lamarin ke iya sanya wa zuciya ta ƙame, tare da daina bugawa.
"Da zarar zuciya ta tsaya lokaci guda za a samu mutuwa." in ji shi.
Rashin isar jini zuwa cikin zuciya

Asalin hoton, Getty Images
'Acute myocardial infraction' a Turance, na faruwa ne a lokacin da aka samu raguwar isar jini zuwa cikin zuciya, wanda kan haifar da ƙarancin iska a cikin zuciya da rage ƙarfin zuciya wajen tura jini ga sassan jiki.
Wannan matsala ce ke haifar da lalacewar sassan zuciya, lalacewa ta dindindin.
Wannan na ɗaya daga cikin manyan silar mutuwar fuju’a.
Wasu daga cikin abubuwan da suke haifar da wannan matsala sun haɗa da shan taba, da ciwon sukari, da hawan jini, da ƙibar da ta wuce kima, da rashin motsa jiki, da kaɗuwa da shan miyagun ƙwayoyi.
Bugun jini

Asalin hoton, Getty Images
'Cerebrovascular accident' wanda akan kira shi da ‘Stroke’ shi ne lokacin da jini ya kasa isa zuwa cikin wani ɓangare na ƙwaƙwalwa ko dai sanadiyyar toshewar jijiya ko kuma fashewar jijiyar. Wannan yanayi kan sanya wasu daga cikin ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa su mutu.
Rashin samun kulawa cikin gaggawa zai iya haifar da lalacewar ƙwaƙwalwa baki ɗayanta.
Wasu daga cikin alamun bugun jini sun haɗa da jiri, da rashin iya magana da kyau, da rashin fahimtar abin da wasu ke faɗa, da rashin gani da kyau da ciwon kai nan take.
Toshewar huhu

Asalin hoton, Getty Images
Wannan kan samo asali ne daga toshewar jijiya a wani ɓangare na jikin ɗan’Adam, musamman ƙafa, inda gundulmin kan tafi zuwa cikin huhu ya toshe hanyar ficewar jini ta cikin huhu.
Wannan kan haifar da mutuwar ɓangaren huhu da lamarin ya shafa, wanda hakan zai hana huhu ya samar da iska ga sauran sassan jiki.
Hakan na iya yin barazana ga rayuwa matuƙar ba a ɗauki mataki cikin hanzari ba.
Lamarin zai iya tsayar da bugun zuciya ko kuma rikirkita harbawar jini daga cikin zuciya.
Kashi ɗaya cikin uku na waɗanda ke samun kansu cikin wannan yanayi na mutuwa.
Alamun mutuwar fuju'a
Da yawa mutanen da kan fuskanci mutuwar fuju’a a mafi yawan lokaci ba su cika kokawa kan wata rashin lafiya mai tsanani ba.
Wasu kuma kan koka kan fuskantar ciwon ƙirji, ko numfashi sama-sama, ko bugun zuciya da sauri.
Shi ya sa masana lafiya ke ganin cewa ya kamata a riƙa lura sosai da mutanen da ke fuskantar larurori da suka shafi zuciya duk ƙanƙantar matsalar.
Yadda za a taimaka don kauce wa mutuwar fuju'a
Duk mutumin da ya gamu da daya da cikin matsalolin da ke janyo mutuwar fuju'a kamar yadda likita ya yi bayani a baya, to ba abin da yake bukata da ya wuce a garzaya da shi asibiti.
Sai dai kafin kaiwa ga asibiti ko samun likita da zai kula da shi, maras lafiyar na bukatar kulawar gaggawa ta farfado da aikin zuciyarsa wadda a sau da dama take tsayawa da aiki a yayin da mutum ya samu kansa a wannan yanayi.
Farfesa Kamilu Musa Ƙaraye, wanda likitan zuciya ne a asibitin koyarwa na Mallam Amnu Kano ya yi wa BBC bayani kan abin da ya kamata wadanda ke tare da maras lafiyar ya kamata su yi domin ganin nunfashin mutum ko zuciyarsa ba ta tsaya da aiki ba.
Likitan ya bayyana abin da ake kira a Turance kuma a takaice ''CPR'' (Cardiopulmonary resuscitation), inda wani da ya ke da kwarewa da wannan hanya zai rika danna kirjin maras lafiyar, akai-akai, domin taimaka wa zuciyar ta ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kai ga asibiti.










