Me mutanen da suka kusa mutuwa ke gani?

Asalin hoton, Christopher Kerr
- Marubuci, Alessandra Corrêa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
A watan Afrilun 1999, wani likitan Amurka mai suna Christopher Kerr ya ga wani al'amari da bai taɓa gani ba tsawon aikinsa.
Daya daga cikin marasa lafiyar da yake kula da su, na kwance a kan gadon asibiti, inda 'ya'yanta huɗu manya ke kewaye da ita, yayin da take kan gargarar mutuwa a lokacin da ta fara wasu abubuwa.
Majinyaciyar mai shekara 70, na zaune a kan gadon asibiti, a lokacin da ta rungumi kafaɗarta tana ayyana ta a matsayin jariri, ta riƙa kiransa Danny tare da rungumarsa da kuma sunbatar kafaɗar.
'Ya'yan nata ba za su iya bayanin abin da ke faruwa ba, saboda ba su ma son wani mai suna Danny a danginsu ba.
Kwana guda bayan haka, 'yar uwar Mary ta zo asibitin domin duba ta, inda ta bayyana musu cewa Mary ta taɓa haifar wani jariri da aka sanya wa suna Danny kafin ta haifi sauran 'ya'yan nata.
Raɗaɗin rashin jaririn ya yi mata zafi sosai har ya kai ga Mary ba ta so ma a yi maganar jaririn.
Kerr - wanda da a farko likita ne, da ya kware a fannin zuciya, ya samu digirinsa na uku a fannin lafiyar kwakwalwa - ya yi amfani da wannan dama wajen faɗaɗa iliminsa inda ya mayar da hankali wajen nazartar halin da mutanen da ke kan gargarar mutuwa ke samun kansi a ciki.

Asalin hoton, Plan Shoot / Imazins / Getty Images
'Kwanciyar hankali'
A yanzu shekara 25 bayan haɗuwarsa da Mary, Dakta Kerr ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masana ɗabi'un mutanen da ke kan gargarar mutuwa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce mutanen kan fara ganin abubuwan makonni kafin ranar mutuwarsu, inda kuma suke ci gaba da ƙaruwa a yayin da suke tunkarar lokacin mutuwar.
Dakta Kerr ya ce ya kwashe shekaru yana ziyartar mutane da dama waɗanda suke dab da rasa rayukansu tare da gani da yin magana da iyaye da 'ya'ya da kuma nazartar dabbobin waɗanda suka mutu, kamar karnuka ko kyanwowinsu.
Ga marasa lafiyar da ke gaskata abin da suke gani, hakan na sanya musu kwanciyar hankali.
Kerr ya ce majinyatan na shiga halin rashin tabbas a yayin da lafiyar tunaninsu ke raguwa.
To sai dai, likitoci da dama sun yi watsi da nazarin Dakta Kerr, suna masu cewa majinyatan na gane-ganen abubuwa ne, sakamakon damuwar da suke ciki.
Likitocin sun ƙara da cewa ana buƙatar gudanar da binciken kimiyya kafin a tabbatar da nazarin na Dakta Kerr.
A kan haka, Kerr ya fara binciken a Amurka a 2010, inda ya ƙaddamar da ƙuri'ar jin ra'ayin majinyan da ke fuskantar mutuwa dangane da abin da suke gani.

Asalin hoton, Christopher Kerr
Ana tantance duka majinyatan kafin a fara jin ra'ayinsu, domin tabbatar da cewa suna cikin hayyacinsu.
Kafin wannan binciken, mafi yawan rahotonnin da ake samu kan halin da majinyatan ke ciki, ana samunsu ne daga makusantansu, inda ake adana abubuwan da suke tunanin shi ne majinyatan ke gani.
An wallafa binciken a mujallun kimiyya ciki har da mujallar ''National Library of Medicine'', ta Sweden.
Har yanzu Kerr bai samu cikakkiyar amsar da zai yi cikakken karin bayani kan abin da mutanen ke gani ba, yana mai cewa abin da ke haddasa tunanin ba shi ne abin da bincikensa ya mayar da hankali ba.
"Batun cewa ban yi bayanin hanyoyin binciken nawa ba, ba zai karyata bincikena kan abin da waɗanda ke kan gargarar mutuwa ke gani ba," in ji shi.
A yanzu Kerr shi ne shugaban ƙungiyar da ke samar da kayan tallafi a Buffalo da ke jihar New York ta Amurka.
An buga littafinsa mai suna, 'Death Is But a Dream: Finding Hope and Meaning at a Life's End'', a shekarar 2020 yayin da aka fassara shi zuwa harsuna 10.

Asalin hoton, Getty Images
Ya tattauna da BBC kan binciken nasa da kuma ma'anar abin da ake nufi kan gargara.
Bayan kwashe waɗannan shekaru, me ka koya kan wannan binciken naka?
"Mutuwa na nufin sauye-sauye ciki har da wurin da ake zaune , da yadda muke kallon abubuwa da kuma abubuwan suka bambata rayuwa da mutuwa.
"Mutuwa na sa ka riƙa kallon abubuwa a yadda suke. Mutane kan mayar da hankali kan abubuwan da ke gabansu, da abubuwan da suke son cimmawa, da ke da alaƙa da su.
''Abin sha'awar shi ne, waɗannan sau da yawa suna dawowa ta hanyoyi masu ma'ana, waɗanda ke tabbatar da rayuwar da aka jagoranta waɗanda kuma ke rage fargabar mutuwa''.
"Abin da muke sa rai shi ne ƙaruwar tunani da damuwar da ake fuskanta, a yayin da ake tunkarar mutuwa''.
"Muna ganin mutanen da ke ayyana rungume masoyansu da gaske''.
Yaya wannan yanayi yake tsakanin mutane la'akari da bincikenka?
"A bincikenmu, kusan kashi 88 na mutanen da aka gudanar da nazarin a kansu, sun bayar da rahoton aƙalla ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa.
"Muna ganin ƙaruwar faruwar abubuwan a lokacin da mutanen ke fuskantar mutuwa."
"Amma mukan tambayi mutane a kowace rana, saboda akan samu bambancin amsoshinsu tsakanin ranaku.
"Tambayarsu a ranar Litinin, za ka iya samun mabambantan amsoshi fiye idan da a ce ranar Juma'a ce ka yi musu tambayoyin.

Asalin hoton, Getty Images
Ganin waɗanda suka daɗe da mutuwa
Mene ne taken binciken naka?
"Kusan kashi ɗaya bisa uku na marasa lafiya suna ba da rahoton abubuwa kamar tafiye-tafiye. Yawancin lokaci suna tunawa da mutanen da suke ƙauna kuma suka rasa su.
"Ganin [gane-ganen ] matattu na ƙaruwa yayin da suke dab da mutuwa. An kuma ce wannan shi ne abu mafi jin daɗi.
"Abin da suke gani yana da ban sha'awa. Suna mai da hankali kan mutanen da suke ƙauna da goyon bayansu, kuma waɗanda suka fi damuwa da su. Wannan yana iya zama iyaye, ko 'yan'uwa, kuma ba ɗayan ba.
"Kusan 12% sun bayyana abin da suke gani - a cikin tambayoyin - a matsayin ko dai ba su da tsaka-tsaki ko rashin jin daɗi. Rashin jin daɗi wasu daga cikin mafi sauyi ko ma'ana.
“Don haka, duk wata matsala da kuke da shi, galibi ana magance su cikin waɗannan abubuwan.

Asalin hoton, Getty Images
Mafarki
A wasu lokuta mafarki majinyatan ke yi, amma a wasu lokutan ba barci suke yi ba. Mene ne bambanci tsakanin biyun?
"Mun tambayi mutane ko suna barci ko a tashe suke, kuma masar da muka samu ya kai rabi da rabi.
"Mutuwa ta haɗa da barci da kuma abubuwan da tunanin ke haifarwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ka kuma yi aiki da ƙananan yara da ke kan cutar ajali. Me ya bambanta tsakanin mutuwar yara da manya?
"Ƙananan yara abin nasu na da sauƙi, saboda ba su da wata damuwa sosai. Ba sa iya bambance tsakanin tunani da gaskiya. Ba su kuma son mutuwa ba. Don haka suna gudanar da rayuwrsa ne ba tare da fuskantar wata damuwa ba.
"Za ka ga cewa sau da yawa suna da waɗannan abubuwan ta hanyoyi masu ban sha'awa da ban sha'awa kuma da alama sun san ma'anarsa da gaske.
"Sau da yawa, ko da ba su san wanda ya mutu ba, tabbas sun san dabbobin da ke kewaye da su, waɗanda za su "gani" tare da fayyacewa."

Asalin hoton, Getty Images
Iyalai
Wane tasiri hakan ke yi ga makusantan majinyatan?
"Mun wallafa takardu biyu kan wannan, ɗauke da ra'ayoyin mutum 750 da abin da suka gani, babban abin shi ne abin da ya yi wa majinyatan daɗi, shi ne kuma zai yi wa makusantansu daɗi.
''Mun yi nazari mai ban sha'awa, inda muka kalli hanyoyin damuwa. Mutanen da suka shaida irin waɗannan abubuwan ba sa damuwa da hanyoyin da suka fi lafiya, saboda yana siffanta tunaninsu da tunawa da su.
Kana da digiri na uku a fannin kimiyya, amma ka ce ba za ka nuna tushe bincikenka ba, wanda kuma shi ne hanyar dogaro na bainciken naka me yasa ka dauki wannna mataki a matsayinka na Dakta?
"E , hanya ce mai sauƙi.
"Akwai lokuta da dama da na shiada, kuma abin da na gani ya zarta a karyata shi.
"Abin da majinyatan ke gani abu ne mai sauƙi, idan akakwatantan da kai mai cikakkiyar lafiya''.

Asalin hoton, Getty Images
Ka ce ka fara bincikenka saboda sauran likitoci na bukatar ƙaddamar da bincike don gano shaida, amma aikinka ya ɗauki hankalin kafofin yaɗa labarai fiye da fannin lafiya. Ya kake kallon hakan?
"Na sha matuƙar wahala wajensamun matasan likitoci su fahimci abin da marasa lafiya ke fuskanta. Don haka, mun ci gaba da bayyana hujjojinmu, mun kuma wallaf bincikenmu cikin harnuna da domin ya samu karɓuwa da yabo.
"Ban fahimci cewa abin da na gano kuskure ba ne. Domin, lokacin da ya shiga cikin kafofin watsa labaru na yau da kullum, ya samu karɓuwa kuma ya zaga duniya."
Don haka, mutanen da ke ba da kulawa ba su damu da wannan ba, amma mutanen da suke samun kulawa, ko kuma kawai suna sha'awar mutuwar kansu, sun rungumi wannan aikin. Sabanin ban sha'awa da yake da shi."

Asalin hoton, Getty











