Shin da gaske cutar kyandar biri ta barke a Najeriya?

Asalin hoton, EPA
Cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta karyata jita-jitar da ake yadawa kan cewa cutar kyandar biri wadda aka fi sani da ''monkey pox'' ta mamaye wasu manyan jihohin Najeriya.
Cibiyar ''Nigeria Centre for Disease Control'' ta bayyana cewa suna ganin labarai kamar ''kyandar biri ta shiga Lagos da Ribas da Akwa-Ibom'' amma duka ba gaskiya bane kamar yadda hukumar ta bayyana.
Ta kuma ce tun bayan da aka samu bullar wannan cuta a Najeriya a 2017, tun daga lokacin ta ke sa ido kan kanana-kananan bullar cutar nan da can a fadin kasar.
Ta kuma yi karin haske inda ta ce ''cibiyar na bincike da kuma tattara alkaluman masu kamuwa da cutar a duk mako a fadin Najeriya. Muna nan muna kokarin shaida wa ma'aikatanmu na jihohi da su rinka kokarin sanar da mu idan aka samu bullar wannan cuta.''
Cibiyar ta ce a rahoton da ta ke wallafawa duk mako a shafinta na intanet, mutum uku ne ake zargi da kamuwa da cutar - biyu a Legas, daya a Ribas, kuma babu wanda ya mutu.
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta ce cutar kyandar biri cuta ce da ta fi addabar yammacin Afirka da kuma tsakiya.
A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar a ranar Juma'a, ta gargadi kafafen yada labarai da su guji saurin yada labaran da ba gaskiya ba.
Cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ce dai hakkin bayyana dokar ta baci kan cututtuka ko kuma ta bayyana barkewar cuta a kasar.










