Abubuwan da ba za ku iya shiga jirgin sama da su ba

Jirgin sama a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan taƙaddamar da aka samu tsakanin mawaƙin Najeriya Wasiu Ayinde da wasu ma'aikatan filin jirgin sama na Abuja, mutane da dama ke bayyana ra'ayinsu game da lamarin.

Lamarin ya ja hankalin mutane da dama bayan da aka ga bidiyon mawaƙin ya tare gaban jirgin sama da ke shirin tashi.

Sai dai wasu na cewa yayin da ake da dokoki da dole a bi a filin jirgi, amma su ma masu hawan jirgin na da hakkokin da suka kamata a kare.

Domin tantance irin abubuwan da suka kamata wanda zai shiga jirgi ya ɗauka da kuma wadanda ba su kamata ba, ga bayani, wanda muka samo daga kamfanin jirgin sama na United Nigeria Airline da kuma kamfanin jirgin sama na Netherlands, KLM.

Abubuwan da doka ta haramta a shiga da su jirgin sama a Najeriya

Wasiu Ayinde ya samu taƙaddama da ma'aikatan filin jiragen sama na Abuja lokacin da yake ƙoƙarin shiga jirgin ValueJet daga Abuja zuwa Legas

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, ...

A Najeriya, akwai abubuwa da dama wadanda doka ta haramta shiga da su cikin jirgin sama. Sun haɗa da:

Abubuwa masu fashewa, nakiya, garin alburushi, makami, abin kunna wuta, abin hada gam da kuma abin hada fenti.

Sauran su ne:

  • Abubuwan da ke iya tayar da wuta.
  • Abubuwa masu kaifi, kamar reza da wuƙa da ƙarfe mai tsini wanda zai iya huda fatar mutum wanda za a iya amfani da shi a matsayin makami.
  • Bindiga
  • Abu mai ruwa-ruwa wanda yawan shi ya zarce 100ml
  • Sinadarai masu guba
  • Guba ita kanta

Waɗanda aka haramta amma yanayi zai iya bari a shiga da su:

Dabbobi

Ba a amince wa fasinjojin jirgin sama su shiga cikin jirgi da dabbobi ba, sai dai idan akwai wani aiki da dabbobin za su yi.

Abinci

Abinci mai ruɓewa, kamar ƴaƴan itatuwa, amma akwai inda za iya bari dangane da dokar kamfanin jirgin.

Kudi

Duk da cewa ba haramun ba ne shiga da kuɗi cikin jirgi amma akwai yawansu da aka ƙayyade.

Idan kudin na da yawa sosai za a zargi wanda ke da su, wajibi ne sai mutum ya yi bayanin inda ya same su.

Kayan wasan yara masu batir

A wasu lokuta kamfanin jirgin sama zai iya haramta abubuwa masu amfani da batir kasancewar haramun ne a shiga jirgi da sinadarin lithium.

Bayani mai muhimmanci

Abin da aka haramta a wani wurin, zai iya yiwuwa wani wurin ba a haramta ba, hakan ne ya sa yake da muhimmanci matafiya su duba ƙa'idojin kamfanin jirgin da za su yi tafiya da shi gabanin zuwa filin jirgi.

Sai dai duk wani abu da Hukumar lura da sufurin jiragen sama ta duniya IATA ta haramta to haramun ne a ko ina.

Haka nan wajibi ne matafiyi ya bi dokokin da filayen jiragen sama suka gindaya ba tare da raini ba.