Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama

Ministan tsaron Ghana Dr Omane Boamah da na muhalli, Murtala Mohammed

Asalin hoton, FB/Multiple

Bayanan hoto, Ministan tsaron Ghana Dr Omane Boamah (Hagu) da na muhalli, Murtala Mohammed (Dama)
Lokacin karatu: Minti 1

Ministan tsaron Ghana Dr Omane Boamah da na muhalli, Murtala Mohammed tare da wasu mutum shida sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a yau Laraba.

Lamarin ya rutsa da ma'aikatan jirgin uku a hatsarin jirgin mai saukar ungulu wanda ya faru a yankin Ashanti.

Shugaban ma'aikatan ƙasar Ghana Julius Debrah wanda ya yi jawabi ga al'ummar ƙasar ya umarci da a sassauto da tutoci domin nuna alhini.

Tun da farko wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar da safiyar yau, ta nuna cewa an daina jin ɗuriyar jirgin - mai saukar ungulu - bayan katsewar sadarwarsa.

Rahotonni sun ce mutanen da ke cikin jirgin sojin - mai lamba Z9 - na kan hanyarsu ta zuwa garin Obuasi mai arzikin ma'adinai domin halartar wani taro na ƙasa lokacin da hatsarin ya auku.

Omane Boamah sanye da baƙar ƙwat da farar riga a ciki ɗaure da jan ƙyalle yana jawabia a gaban makirfo

Asalin hoton, Omane Boamah/Facebook

Hotunan da ke nuna ɓaraguzan jirgin sun karaɗe shafukan sada zumunta a ƙasar.

Tuni aka tura jami'an bayar da agajin gaggawa yankin domin gano jirgin.

Hatsarin jiragen sama abu da ya jima yana zama fargaba a zukatan ƴan ƙasar

Ko a shekarar da ta gabata ma wani jirgin soji ya faɗi a Yankin Yamma, kodayake babu rahoton rasa rai.

Sauran waɗanda suka rasu a hatsarin sun hada da jami'in tsara harkokin tsaro na ƙasar Ghana Alhaji Muniru Mohammed da mataimakin hukumar gudanarwar jam'iyyar NDC mai mulkin ƙasar Samuel Sarpong.

Ma'aikatan jirgin da suka rasu kuma su ne Squadron Leader Peter Babafemi Anala, da Flying Officer Manin Twum-Ampadu da kuma Sergent Ernest Addo Mensah.