Kwarewar Nketiah tana kara fitowa

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya yi amanar cewa Eddie Nketiah na kara kwarewa bayan da ya taimakawa Gunners suka kai zagaye na hudu a gasar cin kofin FA kamar Manchester City bayan da suka doke kungiyar Oxford United a filin wasan Kassam.

Nketiah ya zura kwallaye biyu a cikin mintuna shida bayan Mohamed Elneny ya zura kwallo ta farko a cikin ragar Oxford.

A yanzu dan wasan ya ci kwallaye biyar a wasanni shida da ya buga a baya baya nan.

Nketiah ya maye gurbin dan wasan gaba Gabriel Jesus wanda ya samu rauni.

" Ya nuna natsuwa sosai ," in ji Arteta. " Ya kware kwarai da gaske , musaman yadda ya ke gudu domin ya zura kwallo.

"Dan wasan gaba daya mu ke da shi kuma zai dauki tsawon watanni kafin Gaby ya murmure kuma wannan zai kawo mana cikas amma duk haka za mu yi amfani da ‘yan wasan da mu ke da su a halin yanzu ."

Arsenal wadda tana cikin kungiyoyin kwallon kafa da ke gaba- gaban a gasar firimiya sun fuskanci tirjiyya daga ‘yan wasan Oxford kafin daga bisani suka nuna mu su ruwa ba sa‘ar kwando bane..