Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lloris ya yi ritaya daga buga wa Faransa kwallo
Golan Faransa, Hugo Lloris ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa kwallo.
Matakin golan Tottenham din mai shekara 36 na zuwa ne makonni uku bayan Faransa ta sha kashi a hannun Argentina a wasan karshe na gasar cin kofin duniya.
“Na yanke shawarar daina buga wa Faransa kwallo tare yin tunanin na samu duk abin da nake so”, in ji Lloris.
A hirarsa da jaridar L’Equipe, ya ce “Ina tunanin ya kamata in yanke shawara kafin soma wasannin share fage na gasar cin kofin kwallon kasashen Turai.”
Lloris ya soma buga wa Faransa kwallo tun yana da shekara 21 a wasan sada zumunci tsakaninsu da Uruguay a watan Nuwambar 2008.
Ya buga wa kasarsa a wasanni 145 abin da ke nuna cewa ya kafa tarihi a Faransa.
Lloris ya rike matsayin kyaftin din Faransa sau 121.