NFF ta gabatar da sabon kocin Super Eagles Eric Chelle

Asalin hoton, NFF Twitter
Hukumar ƙwallon kafar Najeriya, NFF ta gabatar da sabon kocin Super Eagles, Eric Chelle ranar Litinin a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, Najeriya.
Chelle ya zama na 42 da zai horar da babbar tawagar ƙwallon kafar kasar, ya maye gurbin Augustine Eguavoen, wanda ya yi aikin riƙon kwarya.
Cikin waɗanda suka gabatar da kocin sun haɗa da shugaban hukumar ƙwallon kafar Najeriya, Ibrahim Musa Gusau da shugaban hukumar wasanni, Shehu Dikko da sakatare janar na NFF, Mohammed Sanusi da sauransu.
Chelle wanda ya buga gurbin tsare baya a lokacin da ya taka leda, ya karɓi aikin jan ragamar Super Eagles, bayan da ya ajiye aikin horar da MC Oran ta Algeria.
Mai shekara 47, ya kafa tarihin ɗan Afirka na farko ba daga Najeriya ba da zai horar da Super Eagles mai kofin nahiyar Afirka uku jimilla.
''Ina alfahari da na zama kociyan Super Eagles. Najeriya tana da tarihi da fitattun ƴan wasan tamaula a duniya kamar su Ikpeba da Amokachi da Amuneke da Yekini da Oliseh da Eguavoen da Finidi da West da Obi Mikel da Babangida," in ji Chelle.
Haka kuma kociyan ya kara da cewar zai mayar da Super Eagles buga salon kai hare-hare da yawa a wasanninta.
Chelle zai yi aiki tare da Hadi Taboubi a matakin mataimaki da Thomas Gornourec mai kula da koshin lafiyar ƴan wasa da Jean Daniel Padovani mai horar da masu tsare raga.
Aikin farko da zai fara shi ne jan ragamar Super Eagles ta ƴan wasan da ke taka leda a gida wato CHAN a gasar kofin Afirka da za a yi a Uganda da Kenya da kuma Tanzania
Daga nan zai ja ragamar babbar Super Eagles a sauran wasannin shiga gasar cin kofin duniya da za a ci gaba tun daga cikin watan Maris.
Chelle ya taka leda a Faransa a ƙungiya da ta haɗa da Valenciennes da Châteauroux daga nan ya shiga aikin horar da ƙwallon kafa.











