Abin da ya sa aka sauya wa kadoji 1,000 wurin zama a India

    • Marubuci, Daga Pramila Krishnan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Dan jarida
    • Aiko rahoto daga, BBC Tamil

Wata cibiyar ajiye kadoji a Indiya, na shirin mayar da kadoji 1,000 zuwa wani wurin adana namun daji mai nisan kilomita sama da dubu mallakin hamshakin biloniya Mukesh Ambani.

A shekara da ta gabata, masu kula da gandun daji suka amince na mayar da kadoji daga garin Madras da ke kudancin jihar Tamil Nadu zuwa wasu cibiyoyin adana su a yammacin jihar Gujarat. An mayar da kadpoji sama da 300 zuwa Gujarat ya zuwa yanzu.

Jami'an lura da wurin ajiye kadojin sun ce ana son mayar da su wani wuri ne saboda fada a junan su sakamakon yawa da suka yi.

''Saboda yawan su, suna lalata daruruwan kwayaye a kowace shekara,'' a cewar Nikhil Whitaker, wani mai lura da cibiyar a birnin Chennai. ''An dauki matakin mayar da kadojin zuwa wurin adana namun daji ne domin samar musu isasshen wurin rayuwa,'' in ji Nikhil.

A tsawon shekaru da suka gabata, masu lura da kadojin na mayar da su zuwa wurare masu inganci da kuma wurin adana namun djai a fadin Indiya. Sai dai, wannan ne karon farko da aka mayar da kadoji da yawa zuwa wani wuri.

Wurin adana namun dajin mai fili eka 425 da aka samar shekara uku da suka gabata a birin Jamnagar na birnin Gujarat, ya bayyana a cikin sabon rahoto cewa za a samar wa kadojin isasshen wuri da kuma abinci.

An kafa cibiyar ajiye kadojin na birnin Chennai a 1976, inda ake ajiye nau'in su guda uku masu suna - muggers da saltwater da kuma gharials.

Cibiyar na da kadoji sama da 40 kuma burin su shine kare su saboda su ƙara hayayyafa domin sake su cikin gandun daji don ci gaba da rayuwa.

Wani umurnin gwamnatin tarayya na 1994, shi ne ya dakatar da yunkurin sake kadoji zuwa gandun dazuka, a cewar Mr Whitaker. Tun bayan nan, wurin ajiye kadojin ya rika mayar da wasu daga lokaci zuwa lokaci zuwa wurin ajiye namun daji da dabbobin dawa.

Yayin da gandun dazuka ke kokarin ƙarewa inda wurin ajiye namun daji kuma baya samun daukar kadoji da yawa, hakan ya sa wuraren kai su na ƙarewa, in ji jami'ai.

Jami'ai a cibiyar sun ce za a dauki kadojin cikin akwatuna zuwa garin Jamnagar a cikin ababen hawa masu matsakaicin yanayi.

''Tun da ya kasance sau daya ake bai wa kadoji abinci a kowane mako, muna basu kafin a fara tafiyar,'' in ji Mr Whitaker.

Masu fafutukar kare muhalli, sun nuna shakku kan yunkurin mayar da kadojin zuwa wani wuri a matsayin hanyar rage yawansu a cibiyar. Wani mai rajin kare dabbobi P Kannan, ya ce tun da ajiye su za ayi a kebabben wuri, matsalar cunkoson su ba zai ragu ba.

''Babu wata hanya ta magance matsalar, sannan kuma ba zai yiwu ba a ajiye kadoji maza da mata a wuri daya na tsawon lokaci saboda za su fada tsakaninsu,'' a cewar Mr Kannan.

BBC ta tuntubi hukumomin ajiye namun daji na jihar Gujarat, don jin irin matakai da suke dauka domin sanya ido kan yawan kadoji da suke da su, amma babu wani martani ya zuwa yanzu. Sakataren kungiyar kula da muhalli da kuma dabbobi, S Jayachandran, ya ce maimakon mayar da su zuwa wani wuri, kamata ya yi Indiya ta ƙara bude wuraren kula da dabbobin daji. ''Idan akwai isasshen wurin da kadoji za su yi rayuwa, ba wani dalili da zai sanya a mayar da su zuwa wurin ajiye namun daji.''