Autan Na Aisha ya buge Rabe Shagon Ebola a damben Maraba

Damben Gargajiya

Rabe Shagon Ebola ya yi rashin nasara a hannun Autan Na Aisha a damben safe a Marabar Nyanya a jihar Nasarawa, Najeriya.

Tun farko Wazirin Labaran ɗan Gwamba ya gwangwaje Rabe da kiɗan Ebola, sannan ya washe Autan Na Aisha Guramaɗa.

Dama 'yan wasan biyu sun ɗaure hannunsu sai suka faɗa fili, nan da nan Anas alkalin wasa ya ɗaga hannuwansu cewa sune wasa na gaba.

Suna taka dambe a turmin farko Rabe ɗan damben Kudu ya dunga kai kora ga Autan Na Aisha, wanda ya dunga fita daga filin wasa.

A turmi na biyu ne Rabe ya samu rauni a hanunsa na hagu da yake kai bugu da shi, nan da nan aka kai masa taimakon agaji har hanunsa ya koma yadda yake.

Damben Gargajiya

Mun ɗauka za a raba wasan sai Rabe Bahagon Ebola ya ce zai iya ci gaba da dambe, nan take Idris Bamɓarewa ya kore fili domin ci gaba da dambe.

'Yan wasan sun samu kuɗi daga wajen magoya baya, daga nan aka shiga turmi na uku - a nan ne Autan Na Aisha ya fita daga Fili, shi kuwa Rabe ya bi shi daga nan sai ga Shagon Ebola a kasa.

Da farko Kudawan sun ce ba kisa ba za a zagaya da Autan Na Aisha ba, amma daga baya komai ya lafa aka zagaya da ɗan damben Guramaɗa.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga su ne na Garkuwan Kurma da Garkuwan Dunan Bata jemuba, waɗanda suka yi turmi biyu masu kyau.

Wani canjaras da aka buga shi ne tsakanin Ɗan Butsalle da Bahagon Ali Yaro, Dogon Inda da Shagon Bahagon ɗan Fandam da na Autan Autan da Jan Idon Guramaɗa.

Shi kuwa Shagon Basiru ya buge Shagon Bahagon Balan Gada da wani babban damben da aka yi ba kisa tskanin Ɗan Aliyu na Arewa da Shagon Aisha.