An kama amaryar da ta 'kashe' mijinta ta gudu lokacin tafiyar cin amarci

A ranar 11 ga watan Mayu ne aka yi bikin auren Sonam da Raja

Asalin hoton, IYALIN Raghuvanshi

Bayanan hoto, A ranar 11 ga watan Mayu ne aka yi bikin auren Sonam da Raja
    • Marubuci, Geeta Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Delhi
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ƴansanda a Indiya sun ce wata amarya da ta yi ɓatan-dabo bayan an gano mijinta da aka yi wa mummunan kisa a lokacin tafiyar cin amarci ta miƙa kanta, kuma a yanzu haka ana tsare da ita.

Tun farko iyalan ma'auratan sun yi zargin cewa ita ma amaryar an kashe ta ne ko kuma an yi garkuwa da ita, inda suka yi ta fafutikar ganin an sako ta.

A yanzu ƴansanda na zargin amaryar mai suna Sonam Raghuvanshi, mai shekara 25 a duniya, ita ce ta ɗauki wasu ƴan daba suka kashe mijinta mai suna Raja mai shekara 30 a duniya a lokacin da suka yi tafiyar cin amarci zuwa jihar Meghalaya da ke arewa maso gabashin ƙasar ta Indiya.

A yanzu an kama wasu ƙarin mutum huɗu.

Mahaifin amaryar, Devi Sigh ya kare ƴarsa tare da cewa "ba ta da hannu a lamarin, ba za ta iya yin wannan aika-aika ba."

Sabbin ma'auratan waɗanda ke zaune a birnin Indore da ke jihar Madhya Pradesh sun yanke shawarar zuwa Meghalaya domin shan amarci ne saboda labarin da suka ji na cewa jihar na da kwazazzabai masu ban sha'awa, kamar yadda ɗan'uwan Raja, Sachin Raghuvanshi ya shaida wa BBC kafin kama amaryar.

A ranar 11 ga watan Mayun da ya gabata ne aka gudanar da bikin aurensu a birnin Indore inda iyalan dukkanin ma'auratan suka yi maraba da bikin.

"An sgirya aurensu ne wata huɗu da suka gabata kuma dukkaninsu sun yi murna da lamarin sannan babu wani rikici tsakaninsu kafin, da kuma bayan ɗaura auren," kamar yadda ɗan'uwan angon ya bayyana.

Ma'auratan sun bar gida ne a ranar 20 ga watan Mayu. Sai dai ba a sake jin ɗuriyarsu ba bayan kwana hudu.

Ƴansanda da masu aikin ceto da kuma mutanen yankin sun shiga aikin neman ma'auratan. Masu ceto sun riƙa shiga surƙuƙi da ramuka a ƙoƙarin neman ma'auratan, sai dai hukumomi sun ce ruwan sama da hazo sun zama ƙalubale gare su.

Bayan mako ɗaya an tsinci gawar Raja wadda ta fara ruɓewa, inda aka yi masa yankan rago sannan aka yi awon-gaba da lalitarsa da zoben zinare da kuma sarƙarsa ta wuya. Sai dai ba a ga amaryar ba sama ko ƙasa.

Iyalan ma'auratan sun matsa ƙaimi wajen ganin an gano ta, inda suka zargi jami'an ƴansanda da gazawa wajen aiki.

A Juma'ar da ta gabata iyalan sun rubuta wa Firaministan Indiya, Narendra Modi takarda suna neman a matsa ƙaimi wajen gano Sonam.

Yadda aka gano Sonam

Iyalan ma'auratan sun ce amaryar da angon duk sun yi farin ciki a lokacin auren nasu wanda na zumunci ne

Asalin hoton, IYALIN Raghuvanshi

Bayanan hoto, Iyalan ma'auratan sun ce amaryar da angon duk sun yi farin ciki a lokacin auren nasu wanda na zumunci ne

Sai dai a safiyar ranar Litinin, baturen ƴansanda na Meghalaya ya ce Sonam ta miƙa kanta ga ofishin ƴansanda a gundumar Ghazipur da ke jihar Uttar Pradesh.

Daga baya a lokacin ganawa da manema labarai ƴansanda sun ce an kama mutum hudu da ake zargi da hannu.

Duk da cewa bai yi cikakken bayani ba amma ya bayyana amarya Sonam a matsayin "babbar wadda ake zargi".

Mahaifin amaryar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa Sonam ta samu kanta ne a bakin wata hanya a garin Ghazipur a cikin dare, inda ta ari wayar salula ta kira ɗan'uwanta wanda shi kuma ya sanar da ƴansanda.

Ya ce bai samu magana da ƴar tasa ba amma yana da yaƙinin cewa "ta samu wata hanyar tserewa ne daga hannun masu kisan" kuma ya dage kan cewa "ba ta da hannu" a lamarin.

Ya kuma zargi ƴansandan da "kitsa labarin kisan" sannan ya bukaci ministan harkokin cikin gida Amit Shah ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin fayyace gaskiya.