Ƴan Syria da ke komawa gidajensu na fuskantar barazanar nakiyoyin da aka binne

    • Marubuci, Heba Bitar and Lina Shaikhouni
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Idlib, Syria
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ayghad bai taɓa tunanin cewa mafarkinsa na komawa gonarsa ka iya zama wani bala'i ba.

Ya riƙa zubar da hawaye a lokacin da yake nuna mana hoton mahaifinsa, wanda ke murmushi a tsakiyar bishiyoyin zaitun a gonarsa da ke lardin Idlib a arewa maso yammacin Syria.

An ɗauki hoton shekara biyar da suka wuce, watanni kafin dakaru masu alaƙa da tsohuwar gwamnati su ƙwace ƙauyensu da ke kusa da birnin Saraqeb.

Birnin ya kasance muhimmin ɓangare ga ƴan adawar Syria na kusan shekaru, kafin sojojin hamɓararriyar gwamnatin Bashar al -Assad su ƙaddamar da hare-hare kan ƴantawaye a lardin Idlib a ƙarshen shekarar 2019.

Dubban mutane ne suka bar gidajensu a farkon 2020, yayin da dakarun Assad suka ƙwace iko da mafi yawan wuraren da ƴantawayen ke iko da su a arewa maso yammacin ƙasar.

Ayghad tare da mahaifinsa na daga cikin waɗanda suka tsere daga gidajen nasu.

"Dole muka fice daga gidajenmu, saboda ƙazancewar yaƙi,'' kamar yadda Ayghad ya bayyana, yayin da hawaye ke kwarara daga idanunsa.

''Da fari mahaifina bai so ya fita daga gidansa ba. Ya so ya mutu a mahaifarsa.''

Ayghad tare da mahaifinsa sun jima da haƙura da komawa gida, amma a lokacin da dakarun ƴantawaye suka ƙwace iko da ƙauyensu a watan Nuwamban 2024, sun sake sabunta fatansu na komawa gida, wani abu da ya zame musu da-na-sani.

"Mun so komawa gida tare da ci gaba da noma gonarmu,'' in ji Ayghad.

"Mun tafi ne a motoci biyu daban-daban. Mahaifina ya bi wani titi da zai kai shi birnin Idlib. Kuma sai da na ce kada ya bi titin, amma ya dage. Daga ƙarshe motarsu ta taka nakiya ta tarwatse."

A lokacin da abin da ya faru, nan take mahaifin nasa ya mutu.

Ba mahaifi kaɗai Ayghad ya rasa a wannan rana ba, ya kuma rasa babban abin da ke kawo wa gidansu kuɗin shiga.

Babbar gonarsu mai girman murabba'in mita 100,000 - wadda ke cike da bishiyoyin zaitun da suka kai aƙalla shekara 50 - a yanzu an ayyana ta a matsayin wuri mafi hatsarin samun nakiyoyi.

Aƙalla mutum 144 ciki har da ƙananan yara 27 ne suka mutu sakamakon fashewar nakiyoyin da aka binne a lokacin yaƙi, tun bayan hamɓararar da gwamnatin Bashar al-Assad a farkon watan Disamba, a cewar Halo Trust, wata ƙungiyar duniya da ta ƙware wajen lalata nakiyoyi da sauran abubuwan fashewa da aka binne.

Hukumar tsaron fararen hula ta Syria ta shaida wa BBC cewa da dama daga cikin waɗanda nakiyoyin suka kashe, manoma ne da masu gonakin da ke ƙoƙarin komawa gidajensu don ci gaba da sana'o'insu bayan faɗuwar gwamnatin Assad.

Fashewar abubuwan da aka binne a lokacin na barazana ga rayuka a Syria.

Barazanar ta kasu kashi biyu. Na farko abubuwan fashewar, kamar bama-bomai da gurneti.

Hassan Talfah, wanda ke shugabantar hukumar tsaron fararen hular da ke jagorantar aikin tone ababen fashewar, ya ce aikin ba shi da wani ƙalubale mai yawa saboda ana iya ganin abubuwan fashewar a kan ƙasa.

Hukumar tsaron fararen hular ta ce tsakanin 27 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Janairu ta samu nasarar tono abubuwan fashewa 822 a arewa maso yammacin Syria.

Kashi na biyu da ke barazana ga rayuka a Syria- wanda kuma nan ne inda barazanar take a cewar Mista Talfah shi ne manyan nakiyoyin da aka binne.

Ya ƙara da cewa dakarun tsohuwar gwamnati sun dasa dubban ɗaruruwan irin waɗannan nakiyoyin a wurare da dama a ƙasar, musamman a gonaki.

Mafi yawan mace-macen da aka samu a Syria tun bayan faɗuwar gwamnati Assad, sun auku ne a tsoffin filayen daga, a cewar hukumar tsaron fararen hular, kuma mafi yawan waɗanda suka mutu maza ne.

Mista Talfah ya kai mu wurin da aka fi binne nakiyoyin. Motarmu na biye da tasa da tazara mai nisa, a kan wata hanya maras faɗi kuma maras kyau. Ita ce kaɗai mafi lafiya da zai kai ka wurin.

A gefen hanyar, ƙananan yara na ta guje-guje. Hassan ya faɗa mana cewa yaran na cikin iyalan mutanen da suka dawo wurin a baya-bayan nan.

Sai dai ya ce suna cikin hatsarin nakiyoyin.

Bayan mun sauka daga motarmu ya nuna mana wani shinge daga nesa.

"Wancan shi ne wurin da ya raba iyakar wurin da sojojin gwamnati ke iko da shi da wanda ke hannun 'yantawaye a yankin Idlib,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa dakarun Assad sun binne dubban nakiyoyi a wurin har zuwa bayan shingen domin hana 'yantawaye kutsawa.

Wurin da ke kewaye da mu a baya muhimman gonaki ne. Amma a yau sun zama saura, babu alamar shuka sai nakiyoyin da muke iya hangowa ta hanyar amfani da na'urori

Yayin da rundunar tsaron fararen hular ba ta da ƙwarewar tona waɗannan nakiyoyi, abin da kawai jami'anta suke yi shi ne kange wuraren tare da saka alamomin da ke nuna cewa wuraren na da hatsari, domin gargaɗi ga jama'a.

Suna kuma saka rubutun ''Hatsari - Akwai nakiyoyi a nan gaba'' alamar gargaɗi, a jikin tsoffin katangu da gidajen da ke kusa da wurin.

Sukan kuma shirya gangamin wayar da kai ga mazauna wurin kan shiga wuraren da suka kangen.

A kan hanyarmu ta dawowa, mun yi kiciɓis da wani manomi mai shekara 30 wanda bai jima da komawa yankin ba, ya shaida mana cewa wani ɓangaren gonar na danginsu ne.

"Mukan shuka alkama da auduga a wasu lokutan, amma yanzu ba za mu iya shuka komai ba, kuma matsawar ba ma noma gonar nan ba za mu ci gaba da zama cikin talauci, '' in ji Muhammad wanda yake bayani cikin fushi.

Hukumar tsaron fararen hular ta ce a cikin wata guda ta gano tare da killace gonaki kusan 117 da suke zargin an binne nakiyoyi a ciki.

Ba su kaɗai ba ne ke aikin tono nakiyoyin, to amma da alama babu haɗin kai tsakanin ɓangarorin da ke aikin.

Babu wasu cikakkun alƙaluma da ke nuna yawan wurin da aka binne nakiyoyin, amma ƙungiyoyin duniya irin su Halo Trust sun bayar da ƙiyasi.

"Duk wani wuri da sojojin Syria suka zauna akwai hatsarin samun nakiyoyi a kusa da wurin domin suna amfani da su a matsayin dabarun kariya,'' in ji Mista Darmain O'Brien shugaban Halo Trust a Syria

"A wurare irin su Homs da Hama, akwai unguwannin da gaba ɗaya sun ruguje ko sun lalace. Don haka duk wanda ya yi yunƙurin komawa domin sake gina su ko lalata su, to dole ya lura da yiwuwar samun abubuwan fashewa''.

Mista O'Brien ya jaddada cewa akwai buƙatar ƙasashen duniya su yi aiki tare da sabuwar gwamnatin Syria domin inganta ayyukan tono ababen fashewar.

"Abin da muke buƙata daga masu bayar da tallafi shi nen kuɗaɗe, da za mu iya faɗaɗa aikinmu, ta hanyar ɗaukar karin ma'aikata da ba su horo da sayen na'urorin da za mu inganta ayyukanmu'', in ji shi.

A yanzu haka aikin tono abubun fashewa da wayar da kan mutane kan hatsarin abubuwan ya zama aikin ƙashin kai na Mista Talfah. Shekara 10 da suka wuce ya rasa ƙafarsa a lokacin kunce wani bom da aka tona.

"Bana fatan kowane farar hula ko abokin aikina ya fuskanci irin matsalar da na faɗa,'' in ji shi.

"Ba zan iya bayyana farin ciki da nake ji ba, a duk lokacin da na tono wani abu da zai zama baranaza ga rayuwar fararen hula.''

Matsawar ƙasashen duniya da al'ummar Syria ba su haɗa kai wajen kawar da hatsarin da nakiyoyin ke yi wa fararen hula, musamman ƙananan yara ba, to za su ci gaba da zama cikin hatsari.