Mece ce makomar sansanonin sojin Rasha a Syria?

    • Marubuci, Pavel Aksenov
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Defence Correspondent, BBC News Russian
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaba Vladimir Putin ya kasance mai goyon bayan shugaban Syria da aka hamɓarar Bashar al-Assad tun ma kafin ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar a shekara ta 2011.

Tun watan Satumban 2015, aka jibge dakarun sojin Rasha da dama a ƙasar, domin taimakawa gwamnatin Assad kare kanta a yaƙi da ƴan tawaye waɗanda a lokacin suka yi ta dannawa zuwa babban birnin ƙasar.

Sansanonin sojojin Rasha da ke Syria waɗanda suka kasance masu girma sun kasance a birnin Tartous da kuma na sojojin sama da ke Hmeimim, mai nisan kilomita 20 a kudu maso gabashin birnin Latakia.

Yanzu Assad ya tsere ya bar Syria kuma gwamnatinsa ta faɗi - a yanzu kafofin yaɗa labaran Rasha sun cika ta aza ayar tambaya kan makomar kayayyakin soji, jiragen ruwa da ababen hawa da kuma dakaru 7,500.

Yayin da kiyasi ya bambanta kan ainihin yawan jami'ai da kuma kayan aiki da ke can Syria, maganar gaskiya ita ce Rasha tana cikin matsala - me za ta yi, da kuma yadda za ta kare kadarorinta a cikin yanayi da ba a san me zai faru ba.

A 2017, Moscow da Damascus suka rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta shekara 49 da ta bai wa Rasha damar amfani da sansanonin soji a Tartous da Hmeimim, har zuwa 2066. Sai dai, a yanzu yana da wuya a yi hasashen cewa ko sansanonin za su ci gaba da kasancewa karkashin ikon Rasha.

Rasha ta bayyana cewa ba ta tsara ci gaba da amfani da sansanonin biyu ba.

A ranar Litinin, sakataren yaɗa labaran shugaban Rasha, ya bayyana cewa Moscow za ta tattauna kan makomar sansanoninsu da ke Syria karkashin sabon jagoranci a Damascus.

Idan za a yi duba ga kalaman Peskov, hakan na nuna cewa Rasha ba ta yanke hukunci kan makomar sansanonin sojinta ba da ke biranen Tartous da Latakia, don haka za ta iya shirin kwashe dakarunta.

Shirin kwashe sojoji

Wannan ba aiki bane mai kaɗan. A ɗaya gefen, sojojin Rasha 7,500 sun kunshi masu ɗauke da makamai da dama da kuma kayan yaƙi, musamman waɗanda ke sansanin sojin sama a Hmeimim.

Kayayyakin sun kunshi motoci masu sulke da tsarin makamai masu linzami da kuma sauran abubuwa. Idan suka yi niyyar kwashe dakarun da kuma kayayyakin, abin zai janyo hankali.

A shekarun baya, rahotanni sun nuna cewa kayayyakin sojojin Rasha da ke Syria sun haɗa da manyan tankokin yaƙi.

Idan har za a kwashe tankokin su ma, to sai an yi amfani a An-124, ɗaya daga cikin manyan jirage a duniya, ta hanyar amfani da sansanin sojin sama na Hmeimim.

Idan Rasha ta fara aikin kwashe sojojinta cikin gaggawa daga Syria, hakan zai ɗauki amfani da ɗaruruwan jirage na An-124 da kuma Il-76 a cikin kankanin lokaci.

A ɗaya gefen, amfani da hanyar ruwa ta sansanin sojoji da ke birnin Tartous shi ma ba mai sauki bane.

Yayin da jiragen ruwa za su iya ɗaukar jami'ai da kuma kayayyaki da dama, ba za su iya bi ta garuruwan Bosphorus da kuma Dardanelles na ƙasar Turkiyya ba, da ya ratsa tekun Bahar Rum.

Bayan kaddamar da mamaya kan Ukraine da Rasha ta yi, Turkiyya ta rufe hanyar ga jiragen ruwan yaƙi na Rasha da Ukraine karkashin tsarin taron Montreux.

Rufe hanyar na nufin cewa ko da Rasha ta samar da jiragen ruwa domin kwashe dakarunta daga birnin Tartous, sai sun ɗauki hanya mai tsawo ta tekun Mediterranean, da ƙasar Gibraltar da kuma faɗin Turai sannan zuwa ko tekun Baltic ko kuma tashoshin jiragen ruwa da ke arewaci zarcewa ta Norway da kuma tekun Barents.

Idan Rasha ta yanke shawarar kwashe sojojinta daga Siriya, aikin zai lakume makudan kuɗaɗe da kuma kasancewa mai girma.

Me rasa sansanonin Syria ke nufi ga Rasha?

Sansanonin soji a Syria na da muhimmanci ga Rasha ba wai ga mara wa gwamnatin Assad kaɗai ba.

Sun tabbatar da kasancewar sojojin Rasha a Gabas Ta Tsakiya da kuma taimakawa wajen kai jami'ai da kayayyaki zuwa Afrika, inda Rasha ke samun gagarumin goyon baya a ƴan shekarun nan.

Gwamnatin Rasha ta hakikance cewa kayan sojinta da ke birnin Tartous ba za a ce masa babban sansani ba - kuma bai fi karfin jirgi ɗaya ba.

Hakan kuma ya ƙara nuna kasancewar sojojin ruwan Rasha a tekun Mediterranean.

Sansanin sojin sama na Hmeimim yana da muhimmancin gaske, inda ya zama wuri mai muhimmanci ga dukkan ayyukanta a Afrika, ciki har da sojojin hayar Rasha na Wagner.

Idan Rasha ta samu tattaunawa da sabon gwamnati a Syria don ci gaba da iko da sansanonin, yarjejeniyar za ta zama ta daban.

Gwamnatin Bashar al-Assad ta dogara kacokan kan Rasha da kuma sojojinta da ke ƙasar. Yanzu, Moscow za ta buƙaci bayar da wani abu na daban domin samun goyon bayan Damascus.

Ana ganin aika dubban dakaru a 2015 zuwa Syria domin taimakawa Assad a matsayin hanyar tabbatar da matsayin Rasha na mai karfi a duniya.

Kasancewar Rasha a Gabas Ta Tsakiya, shi ne kalubalen Putin na farko daga ƙasashen yamma da kuma iko a faɗin tsohuwar tarayyar Soviet.

A wani lokaci, ya zama kamar Rasha ta cimma burinta a Syria. Yanzu, alfanun sojoji da kuma hulɗar diflomasiyya na tsawon shekaru da Rasha ke bai wa Syria na cikin kila-wa-kala.