Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Houthi sun ce Amurka 'ta ji tsoro' kuma babu tsagaita wuta da Isra'ila
- Marubuci, David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Wani babban jami'in ƙungiyar Houthi ya yi watsi da iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump, cewa an kashe shugabannin ƙungiyar lokacin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta, inda ya ce Amurka ce ta ji tsoro.
"Abin da ya sauya shi ne matsayar Amurka, sai dai matsayarmu ba ta sauya ba," in ji babban mai shiga tsakanin Mohammed Abdul Salam - kamar yadda ya faɗa wa gidan talabijin na Al-Masirah da ke karkashin ikon Houthi.
Oman mai shiga tsakani ta ce Amurka da Houthi sun amince "ba za su ƙara kai wa juna hare-hare ba", bayan shafe makonni bakwai Amurka na kai hari Yemen don mayar da martani ga harin makami mai linzami da Houthi ta kai tekun Bahar Maliya.
Abdul Salam ya kuma ce yarjejeniyar ba ta kunshi batun kawo karshen kai wa Isra'ila hare-hare ba, bayan hare-haren ramuwa da Isra'ilar ta kai Yemen a makon nan.
Ya ce goyon bayan da suke bai wa al'ummar Falasɗinawa a Gaza ba za ta sauya ba.
Ƙungiyar mai samun goyon baya daga Iran na iko da yawancin yankin arewa maso yammacin Yemen tun 2014, lokacin da suka hamɓarar da gwamnatin da duniya ta amince da ita da ke Sanaa, babban birnin ƙasar - abin da ya janyo ɓarkewar yaƙin basasa mafi muni a ƙasar.
Tun watan Nuwamban 2023, ƴan Houthi sun yi ta kai hare-hare kan gomman jiragen ruwa a tekun Maliya da tekun Indiya. Sun kuma nitsar da jiragen ruwa biyu da ƙwace wasu sannan suka kashe ma'aikatan jirgi huɗu.
Ƙungiyar ta ce tana kai hare-haren ne don goyon bayan Falasɗinawa a yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza, ta kuma yi iƙirarin cewa - duk da ba a tabbatar ba - cewa tana far wa jiragen ruwa da ke alaƙa da Isra'ila, Amurka da kuma Birtaniya ne kaɗai.
Ƴan Houthi ɗin ba su tsagaita kai hare-haren ba duk da aika jiragen yaƙin ƙasashen yamma zuwa tekun Maliya da na Indiya a bara.
Ranar 15 ga Maris, Trump ya ba da umarnin tsara farmakin soji kan Houthi da kuma yin barazanar cewa zai shafe ƙungiyar a doron ƙasa.
A karshen watan Afrilu, sojojin Amurka suka far wa shingayen Houthi sama da 800 ciki har da cibiyoyinta na tsara hari, makaman kakkaɓe hare-hare da kuma cibiyoyin ajiye makamai. Sun kuma ce hare-haren sun kashe ɗaruruwan mayaƙan Houthi da shugabanninta da dama", sai dai ba ta bayyana sunayensu ba.
Hukumomin Houthi sun ce hare-haren sun kashe gomman fararen hula, sai dai sun ruwaito samun jikkatar wasu daga cikin mambobinsu.
A fadar White House ranar Talata, Trump ya sanar da cewa ƙungiyar Houthi ta ce "ba su da niyyar sake yin faɗa".
"Ba su son yin faɗa, kuma za mu mutunta hakan sannan za mu dakatar da kai hare-haren bama-bamai, kuma an kashe shugabannin ƙungiyar," in ji shi. "Sai dai, abu mafi muhimmanci za mu amince da kalamansu."
"Sun ce ba za su ci gaba da kai wa jiragen ruwa hare-hare ba kuma hakan shi ne dalilin abin da muke yi."
Daga bisani, ministan harkokin wajen Oman Badr Albusaidi ya rubuta a shafin X cewa: "a nan gaba, babu wani ɓangare da zai kai wa wani hari, ciki har da jiragen Amurka a tekun Maliya da kuma mashigar Bab al-Mandab, abin da zai ba da damar shige da fice cikin tsanaki da kuma wanzuwar kasuwanci a duniya."
Mohammed Abdul Salam ya bayyana ranar Laraba cewa kalaman Trump na nuna "irin fushin da Washigton ke ciki bayan gaza kare jiragen ruwan Isra'ila daga hare-hare".
Ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "yarjejeniyar ba ta shafi Isra'ila ba".
Ita ma Isra'ila ta kasance tana kai hare-hare kan ƴan Houthi tun watan Yulin 2024 - a matsayin martani ga ɗaruruwan hare-haren makamin linzami da kuma na jirage marasa matuki da sojojin Isra'ila suka ce ƙungiyar ta kai wa ƙasar daga Yemen.
An ƙaƙƙaɓe yawanci daga cikinsu, sai dai Houthi ta kai wani harin makamin linzami kusa da filin jirgin saman Ben Gurion na Isra'ila ranar Lahadi, abin da ya janyo jikkatar mutum shida.
Harin ya janyo Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare ta sama har sau biyu.
Harin na farko ranar Litinin ya faɗa kan tashar jiragen ruwa na Hudaydah da ke tekun Maliya, inda aka ruwaito lalata wuraren ajiye kayayyaki da kuma inda jirage ke tsayawa.
Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Houthi ta ce an kashe mutum huɗu.
Ranar Talata, Isra'ila ta kai hari filin jirgin sama a Sanaa da kuma tashoshin lantarki da dama.
Majiyoyi sun faɗa wa Reuters cewa an lalata wasu jirage uku, wuraren bincike kafin shiga jirgi da kuma sansanin soji. An kashe mutum uku, a cewar ma'aikatar lafiyar ƙasar.
"Na faɗa a yawan lokuta cewa duk wanda ya kai wa Isra'ila hari zai ɗanɗani kuɗarsa," in ji Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.