Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hatsarin mayar da martanin Houthi ga harin Amurka da Burtaniya a Yemen
Masana sun yi gargadin cewa harin da kasashen Burtaniya da Amurka suka kai kan kungiyar Houthi a Yemen, zai iya janyo karuwar tashin hankali a yankin da kuma hauhawar farashin mai.
Amurka ta ce ta kai hare-hare ta sama da ta ruwa a wurare 16 na Houthi da suka hada da cibiyoyin bayar da umarni da wuraren ajiye makamai da wuraren da kungiyar ke kare sararin samaniya.
Firaiministan Burtaniya, Rishi Sunak, ya ce harin ta sama ya biyo bayan makonnin da aka shafe mayakan Houthi na kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasashen duniya a bahar maliya, yana mai bayyana hare-haren kasarsa a matsayin "na kare kai ne."
Sai dai kungiyar Houthi wadda ke samun goyon bayan Iran, da ke ikirarin kasancewarta gwamnatin Yemen, na ci gaba da nuna turjiya.
Kakakin sojin kungiyar, Yahya Sarea ya ce ba za a bar hare-haren Amurkar da na Burtaniya su wuce haka ba tare da daukar mataki ba.
Shugaban Houthi, Abdel-Malek al-Houthi ya ce "yanzu suka fara kai hare-hare kan jiragen ruwan da ke da alaka da Isra'ila”.
A watan Nuwambar shekarar 2023 ne mayakan Houthi na Yemen suka kaddamar da hare-hare kan jiragen ruwa masu daukar kwantenoni da ke wucewa ta bahar maliya.
Sun ce suna kai harin ne don nuna goyon baya ga kungiyar Hamas, wadda ta kai hari Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, tare da kisan 'yan Isra'ila 1, 200 ta kuma yi garkuwa da wasu 240.
Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa a kan Zirin Gaza, inda ta kashe Falasdinawa fiye da 23,000.
Kimanin kashi 20 cikin dari na jiragen ruwa masu daukar kwantenoni na duniya ba sa bin tekun bahar maliya, wanda ke kai wa ga mashigin Suez da Bahar Rum zuwa nahiyar Turai.
A maimakon haka sai sun yi kewaye, su bi ta karshen kudancin nahiyar Afrika.
Editan BBC na kasa da kasa, Jeremy Bowen ya ce da wuya kai hare-hare ta sama a karo daya ya kawo karshen hare-haren 'yan Houthi.
“Kasar Saudi Arabia ta yi wa 'yan Houthi ruwan bama-bamai a Yemen a shekarar 2015 zuwa lokacin da aka cimma tsagaita wuta, fiye da shekara guda da ta wuce. Harin bama-bamai baya ba su wani tsoro,” In ji shi.
Yana mai cewa tuni yakin Gaza ya bazu a yankin, Mr Bowen ya kara da cewa idan an dakatar da mayakan Houthi, kungiyoyin masu dauke da makamai da Iran ke goyawa baya da ke Iraqi da Syria za su iya samun kwarin guiwar kai hare-hare kan dakarun Amurka.
Adam Clements, wani tsohon jami'in sojan Amurka wanda ya yi aiki a Yemen, ya ce "baya jin cewa hare-haren da aka kai Yemen zai kai ga cimma burin hana mayakan Houthi ci-gaba da kai harin.
"Kungiyar Houthi ta dade tana yaki da dakarun kawancen da Saudi Arabia ke jagoranta, kuma kungiyar ta samu kwarewa wajen boye kayayyakin da take samu da kuma raunin da ta samu," In ji shi.
Mataimakin shugaban cibiyar (RUSI)ta Amurka, Malcolm Chalmers, ya ce zai yi mamaki idan 'yan Houthi basu mayar da martani ba, inda ya yi gargadin cewa hakan zai iya janyo fito-na-fito a yankin.
Hare-haren da Amurka da Burtaniya suka kai kan kungiyar Houthi ya kuma janyo karin damuwa kan shigar Iran kai tsaye yakin Israila da Gaza.
Lokacin da Burtaniya ta sanar da aniyarta na kai hari kan Houthi a makon jiya, wasu kafafen watsa labarai na Iran da ke da alaka da dakarun juyin-juya-hali sun yi saurin bayar da rahotannin kai wani jirgin ruwa na yakin kasar tekun bahar maliya, a cewar Kayvan Hosseini da ke aiki da sashen BBC na Iran.
Sai dai ana kallon wannan mataki a "matsayin wani abu da aka saba gani" maimakon barazanar soji ta gaske.
“Yiwuwar samun babban tashin hankali tsakanin Iran da kawancen Burtaniya da Amurka har yanzu babu shi sosai” A cewarsa.
Sai dai fargabar karuwar hare-hare a yankin ya sa farashin gangan danyen mai ya tashi.
A wannan shekarar a karon farko ana sayar da kowane ganga a kan dalar Amurka 80.
Hare-haren Houthi a kan bahar maliya ne kawo yanzu, amma masu sharhi sun nuna damuwar cewa idan lamarin ya shafi mashigin Hormuz, zai iya janyo babban tasiri a kan farashin mai da kuma yadda ake kai shi wurare.
Ana amfani da mashigin Hormuz wajen kai gangan danyen mai miliyan 20, wanda ya yi daidai da kashi 20 cikin dari na man da ake amfani da shi a duniya, a cewar masana na bankin ING.
Haka kumahare-haren sun tilastawa jiragen sauya hanyar da suke bi zuwa komawa bi ta Cape of Good Hope na Afrika, wanda ya kai nisan kilomita 6,000 kuma yake daukar karin kwana 10 zuwa mako biyu.
An yi kiyasin cewa sauya hanyar na janyo kara kashe dalar Amurka miliyan daya ($1m ko fam 790,000) a duk tafiyar da jirgin ruwa zai yi daga nahiyar Asia zuwa nahiyar Turai, yayin da lamarin kuma ya haifar da karin kudin inshora da rage abubuwan da ake daukowa saboda nisan tafiyar.