Abin da ya sa har yanzu 'baƙin halittu' ba su zo duniyar bil'adama ba

Asalin hoton, Getty Images
Duniya ƙaramin wuri ne a cikin makeken sararin samaniya mai cike da biliyoyin taurari, wanda hakan ke ɗora ayar tambaya, shin mu kaɗai ne halittu masu rai a cikin wannansarari ko kuwa akwai wani yanki da wasu halittun ke rayuwa?
Mene ne muka sani game da rayuwar wasu halittu a wajen Duniya?
Masana da dama na cewa, ko da babu wata shaida kai tsaye, akwai yiwuwar wasu baƙin halittu suna nan.
Misali, cikin dandazon taurari na Milky Way ɗinmu – ɗaya daga cikin curin dandazon taurari biliyan 200 – akwai taurari kimanin biliyan 300. Rana ita ce babban tushen rayuwarmu a Duniya.
Masana kimiyya kuma na ci gaba da gano duniyoyi suna juyawa a kusa da waɗannan taurarin, wanda ake kira duniyoyin waje, wato 'exoplanets.
"Muna da tabbacin cewa akwai su kuma suna nan," in ji masana kimiyyar sararin samaniya, Dr. Maggie Aderin-Pocock. "Komai lissafi ne"

Asalin hoton, Getty Images
Fasahar da muke da ita yanzu tana ba mu damar bincikar waɗannan duniyoyi na nesa tare da samun cikakken bayani.
Masana suna amfani da na'urar hangen taurari ta 'telescope' domin duba sinadaran da suke cikin taurarin da duniyoyi ke juyawa a kusa da su. Wannan ake kira da 'spectroscopy'.
Muhimmin abu shi ne gano duniyoyi masu sinadaran da suka yi kama da na duniyar bil'adama – ma'ana akwai yanayi a wasu wurare da zai iya yiwuwa ana rayuwa kamar tamu duniyar.
Alamomin suna da ƙarfafa gwiwa. "Muna da labarin ɗaruruwan duniyoyi da za su iya kasancewa akwai masu rayuwa a ciki," in ji Farfesa Tim O'Brien daga Jami'ar Manchester ta Burtaniya.
"Kusan tabbas – cikin shekaru goma masu zuwa – za mu gano duniyar da zai yiwu ana rayuwa a cikinta."

A baya mutane sun yi imani cewa rayuwa na iya wanzuwa ne kawai a duniya da ke nesa da tauraro yadda ya kamata, domin samun adadin haske da zafi da ya dace.
Amma an gano cewa idan har rayuwa na iya wanzuwa a Duniya , tabbas ya nuna cewa watan da taurari ma na iya ɗaukar rayuwa.
Wannan ba yana nufin za su yi kama da halittu kore na fina-finai ba, amma yana nuna cewa rayuwa na iya wanzuwa kuma a rayu.
Masana sun ce, ko da akwai yuwuwar rayuwa a wajen duniya, zai yi wahala baƙin halittu su kansance kamar mutane.
Farfesa O'Brien ya ce: "Yawancin tarihin rayuwa a Duniya rayuwa ce mai sauƙi.
Shin za mu iya samun baƙin halittu daga sararin samaniya?
To, idan ba mu kaɗai ba ne, hakan na nufin za mu iya samun baƙin halittu daga sararin samaniya kenan? lamarin na da wahalar sha'ani.
Da wuya a yi imanin cewa babu wata rayuwa da ta kai matakin tafiya tsakanin taurari, amma har yanzu ba mu ga hakan ba.
Dakta Aderin-Pocock ya ce, "Matsalar mu ita ce muna da misali guda na rayuwa kawai – wato rayuwa a Duniya."
Amma wannan ba yana nufin haka zai kasance a ko'ina ba.
Misali, idan ka rayu kusa da tauraro mai aiki sosai, kana iya rayuwa a ƙarƙashin ƙasa, wanda zai hana ka aika saƙo kenan.

Asalin hoton, Robert Gendler/Science Photo Library/Getty
Za a iya cewa matsalar ita ce ba mu magana a harshe iri ɗaya da su — a kimiyyance.
Tun daga shekarar 1960, masana suna amfani da na'urar hangen taurari da jin ƙara don neman siginal daga baƙin halittu da ke rayuwa a wajen duniya, amma hanyoyin da za su iya aika saƙo da yawa ne, don haka ba za mu iya jin komai ba.
Ko da muna amfani da irin wannan na'uarar, nisan sararin samaniya na iya sa saƙon ya ɗauki dubban shekaru kafin ya isa.
A cikin wani aiki da ake kira da 'Breakthrough Listen' a Jami'ar California, Berkeley, ana bincikar taurari miliyan ɗaya mafi kusa, har ma da taurari dake tsakiyar Milky Way, nisan hasken shekaru 25,000.
Wannan yana nufin idan akwai baƙin halittu da ke rayuwa a wajen duniya , zai iya ɗaukar dubban shekaru kafin mu ji daga gare su.
Tafiya mai nisa
Tafiya tsakanin taurari ba zai yiwu nan ba da nan. Za mu iya aika saƙo da haske, amma jiragen sararin samaniya ba sa iya yin wannan tafiya.
Ko da a ce baƙin halittu na da nasu fasahar, ba lallai suna son zuwa duniyarmu ba. Hakanan, samun haɗuwa da su na buƙatar sa'a da lokaci mai kyau.
Tun da ɗan'adam yana duniya kimanin shekaru 300,000 kenan, ba mu da masaniya ko baƙin halittu sun taɓa zuwa duniyarmu ko za su zo nan gaba ba, bayan mutane sun ƙare a duniya.











