Everton ta sanar da korar kociyanta Sean Dyche

Sean Dyche

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Everton ta kori kociyanta, Sean Dyche kamar yadda ƙungiyar dake buga Premier League ta sanar ranar Alhamis.

Hakan ya zo ƴan awanni tsakani da Everton za ta kara da Peterborough a zagaye na uku a FA Cup.

Everton ta sanar cewar kocin matasanta ƴan kasa da shekara 18, Leighton Baines da ƙyaftin Seamus Coleman za su ja ragamar ƙungiyar a matakin riƙon ƙwarya.

Ƙungiyar da rukunin Friedkin ya mallaka, zai fara neman sabon kocin da zai maye gurbin Dyche - ana ta alakanta Jose Mourinho da aikin na Goodison Park.

Lokacin da Fredkin ya sayi ƙungiyar a cikin Disambar 2024, ya sanar cewar yana tare da Dyche ya gamsu da rawar da yake takawa.

Everton tana ta 16 a kasan teburin Premier League da tazarar maki ɗaya tsakani da ƴan ukun karshe, wadda take da ƙwantan wasa da Liverpool.

Rabonda Everton ta ci wasa tun bayan doke Wolverhampton a farkon watan Disamba a Premier, wadda ta yi wasa biyar a jere ba tare da nasara ba.