Yadda ake samun ƙaruwar mutanen da ke yin mutuwar kaɗaici a Japan

Wata dattijuwa tana tafiya a cikin Tokyo

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Hafsa Khalil
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Kusan mutum 40,000 ne suka mutu su kaɗai a gida a wata shidan farko na 2024, kamar yadda wani rahoton ƴansanda ya nuna.

Daga cikin waɗanda suka mutu ɗin, akwai kusan 4,000 da ba a gane sun mutu ba sai bayan sama wata ɗaya, sannan akwai waɗanda sai bayan kusan shekara ɗaya aka samu labarin mutuwarsu, kamar yadda Rundunar Ƴansandan ƙasar ta bayyana.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Japan ce ƙasa da ta fi yawan tsofaffi a duniya.

Rundunar ta ce tana sa ran fitar da wannan rahoton, yanayin yadda dattawan ƙasar suke rayuwa, su mutu su kaɗai ba tare da an sani ba zai ƙara fitowa fili.

Bisa la'akari da wata shidan farkon wannan shekara ta 2024, ƙididdigar ƴansanda ta nuna cewa an gano mutum 37,227 da suke rayuwa su kaɗai waɗanda kuma suka mutu ba tare da wani a kusa da su ba, sannan kashi 70 cikin ɗari na irin masu yin wannan mutuwa sun kasance ne masu shekara 65 zuwa sama.

Duk da cewa kusan kashi 40 na waɗanda suka mutun, an gano ne a cikin yan kwanaki, rahoton ƴansandan ya gano cewa kusan mutum 3,939 ba a gano su ba sai bayan kusan wata ɗaya, sannan kusan 130 ne suka mutu, amma ba a gano ba, sai bayan kusan shekara ɗaya.

Mutum 7,498 ne suka mutu a tsakanin shekaru 85 zuwa sama, sai kuma mutum 5,920 waɗanda suke tsakanin shekaru 75 zuwa 79. Haka nan an gano gawarwakin mutum 5,635 waɗanda ke tsakanin shekaru 70 zuwa 74.

Kamar yadda talabijin na Japan, NHK ya ruwaito, ƴansanda za su miƙa rahoton ga hukumomin gwamnati domin duba lamarin.

Tun a farkon wannan shekarar, Cibiyar Bincike ta Population and Social Security Research, ta ce yawan dattawan da suke mutuwa (tsakanin shekara 65 zuwa sama) da suke rayuwa su kaɗai zai iya kai miliyan 10.8 zuwa shekarar 2050.

Ana hasashen adadin mutane masu zama su kaɗai a ƙasar zai kai miliyan 23.3 a bana.

A watan Afrilu, gwamnatin Japan ta gabatar da wani ƙuduri da zai magance matsalar zaman kaɗaici da ya daɗe yana ci wa mutane tuwo a ƙwarya a ƙasar, wanda ba zai rasa nasaba da yawan mutane dattijai a ƙasar ba.

Japan ta daɗe tana ƙoƙarin yaƙi da yawaitar dattawa a ƙasar, amma aikin na neman ya gagari kundila.

A bara, Firaiminista Fumio Kishida ya ce ƙasar na neman shiga halin ha'ula'i saboda ƙarancin haihuwa.

Haka ma ƙasashe da suke maƙwabtaka da Japan suna fama da irin wannan matsalar.

A 2022, adadin mutanen China sun ragu a karon farko tun shekarar 1961.