Yadda ƙasashen Asiya ke kashe maƙudan kuɗi don bunƙasa haihuwa

Asalin hoton, Getty Images
A yayin da raguwar haihuwa ke zama wata babbar barazana ga wasu ƙasashen yankin Asiya.
Gwamnatocin ƙasashe a yankin na kashe biliyoyin daloli a ƙoƙarinsu na magance matsalar.
A shekarar 1990, Japan ta fara fito da wasu tsare-tsare da za su ƙarfafa wa ma’aurata gwiwwa domin haifar yara masu yawa.
Makwabciyarta Koriya ta Kudu ta fara nata shirye-shiryen a farkon shekarun 2000, yayin da gwamnatin Singapore ke da nata tsare-tsaren tun a shekarar 1987.
Haka ita ma ƙasar China, wadda ta fuskancin ƙarancin haihuwa a ƙasar karon farko cikin shekara 60 ta bi sahun makwabtan nata a ƙoƙarin bunƙasa yawan al’ummarta.
A yayin da abu ne mai wuya a iya ƙiyasin ainihin kuɗaɗe da waɗannan tsare-tsare ke laƙumewa.
A baya-bayan nan, shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol ya ce ƙasarsa ta kashe fiye da dala biliyan 200 cikin shekara 16 da ta kwashe tana ƙoƙarin bunƙasa yawan al’ummarta.
Duk da wannan ƙoƙari a shekarar da ta gabata yawan jararin da ake haihuwa a ƙasar ya ragu da kashi 0.78.
A ƙasar Japan kuwa, wadda ta fuskancin raguwar haihuwa a shekarar da ta gabata zuwa jarirai 800,000.
Firaministan ƙasar Fumio Kishida ya alƙawarta ninka kuɗn da ƙasar ke kashe wa a ɓangaren tsare-tsaren bunƙasa haihuwa zuwa dala biliyan 59.2.
Sama da abinda ƙasar ke samu daga arzikin da ake sarrafawa a cikin ƙasar.
Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa ƙasashen da ke yunƙurin bunƙasa yawan al’ummarsu ta hanyar haihuwa ya ninka ƙasashen da ke son rage yawan al’ummarsu ta hanyar haihuwa.
Me ya sa waɗannan ƙasashe ke buƙasa yawan jama'arsu?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A sauƙaƙe shi ne, samun yawan al'umma zai sa a samu mutanen da za su yi ayyukan domin samar da kayayyaki, lamarin da zai taimaka wajen samun bunƙasar tattalin arziki mai yawa.
Haka kuma yawan al'umma zai taimak wa gwamnati wajen samun kuɗin haraji masu yawa.
Haka kuma a mafi yawan ƙasashen Asiya yawan tsofaffi na ci gaba da ƙaruwa.
Japan ce ke kan gaba a wannan fanni, inda kusan kashi 30 na al'ummar ƙasar 'yan sama da shekar 65 ne, inda sauran ƙasashen yankin ke biye mata.
Idan aka kwatanta da Indiya, wadda a baya-bayan na ta zarta China a yawan jama'a a duniya.
Fiye da ɗaya bisa huɗu na al'ummar Indiya 'yan shekara 10 zuwa 20 ne, abin da ake ganin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar a nan gaba.
''Rashin bunƙasar yawan al'umma zai kawo cikas ga fannin tattalin arziki, idan kuma aka samu cewa masu yawan shekaru na ƙaruwa a ƙasa, hakan zai sa a kasa taimaka wa tsofaffin'', in ji Farfesa Xiujian Peng ta Jami'ar Victoria.
Mafi yawan matakan da ƙasashen yankin ke ɗauka domin bunƙasa yawan al'umominsu iri ɗaya ne.
Waɗanda suka haɗar da biyan iyayen kuɗaɗen alawus, da bai wa yaran da suka haifa tallafin karatu kyauta, da tallafin raino, da sauƙaƙa musu biyan haraji, da ƙara yawan hutun da ake ba su a wajen aiki.
Shin kwalliya na biyan kuɗin sabulu?
A cikin gomman shekaru da suka gabata alƙaluma daga ƙasashen Japan da Koriya da Singapore sun nuna cewa yunƙurinsu na bunƙasa yawan al'umominsu ba ya cimma nasarar da suke buƙata.
Ma'aikatar kuɗin Japan ta wallafa wani bincike da ke nuna cewa tsare-tsaren da ƙasar ke yi basa samun nasara.
Matakin da ita ma Majalisar Dinkin Duniya ke ganin haka yake.
"Tarihi ya nuna cewa tsare-tsaren da ƙasashe ke yi wajen bunƙasa yawan al'umominsu, inda ake yi wa iyaye mata ihsani domin su haifi jarirai masu yawa, matakan ba sa aiki,'' kamar yadda Alanna Armitage mai kula da asusun kidaya ta Majalisar Dinkin Duniya ta shaida wa BBC.
Ƙasashen yankin Asiya na sahun baya a wajen bunƙasar jama'a kamar yadda rahoton ƙungiyar WEF ya nuna.
Amma babban abun dubawa shine yadda za a samo kudaden da za a iya kaddamar da wadannan matakai, musamman a kasar Japan wadda ita ce kasar da ta cigaba da aka fi bi bashi a duniya.
cikin mataken da ake tuannin dauka a kasar Japan sun hada da sayar da wadansu kadarorin gwamnati, wanda hakan za kara ma gwamnatin nauyin bashi, ko a kara kudin haraji ko kuma kara kudin da mutane ke biya na inshora.
Matakin farko zai kara takura tattalin arzikin al'uamma nan gaba, a inda sauran mataken kuma za su kara sa ma'aikata su shiga wani mawuyacin halin, kuma hakan na iya sa su gujewa haihuwa.
Amma a cewar Antonio Fatás, wani farfesan tattalin arziki da ke jami'ar INSEAD dole ne gwamnatoci su dauki wadannan matakan ko da kuwa ba su yi aiki ba.
"Yawan haihuwa bai karu ba, amma idan aka samu karancin tallafi fa? Mai yiwuwa ba za ma a kai haka ba." A cewrasa.










