Yadda Musulmai a Japan ke fafutikar neman wurin binne ƴan’uwansu

Asalin hoton, getty images
- Marubuci, By Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Al'ummar Musulmi a Japan 'yan tsiraru ne, sun kasance kimanin 200,000 ne kawai a cikin al'ummar ƙasar fiye da miliyan 120.
Kashi 99 cikin 100 na 'yan ƙasar Japan ƙona gawawwakinsu ake yi bisa ga al'adar addinin Buddah ko Shinto, don haka musulmai suna cikin tsaka mai wuya. An haramta ƙona gawa a Musulunci kuma Musulmi kan binne gawawwaki cikin sa'o'i 24.
Ana tilasta wa wasu iyalai yin jigilar gawarwakin ƴan uwansu na tsawon ɗaruruwan kilomitoci domin yi musu jana'iza. "Ko da tunanin cewa zan iya ƙona wani na kusa da ni yana hana ni baccin dare," in ji Tahir Abbas Khan, wanda ya fara zuwa Japan a 2001 don yin digiri na uku.
Malamin jami'a haifaffen Pakistan yanzu ya zama ɗan ƙasar Japan kuma yana aiki a yankinsa inda ya kafa ƙungiyar musulmi ta Beppu.
Fafutika ta tsawon lokaci
Dr Khan ya ce ba wai yana cike da damuwa kan abin da zai faru da gawarsa ba, sai dai yana cikin tashin hankali ganin tsananin ciwo da wasu ke ciki.
"Jana'iza ce abu na karshe da za ka yi wa mutum. Idan na kasa yi wa ɗan’uwana ko abokina jana'iza yadda ya kamata, ba zan iya ci gaba da rayuwa cikin jin dadi ba."

Asalin hoton, TAHIR ABBAS KHAN
An kafa masallaci na farko a yankin Oita Prefecture da ke kudancin tsibirin Kyushu a 2009 sai dai har yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin samar da makabartar binne mamata na al'ummar Musulmi da suka kai 2,000 a yankin.
Mohammed Iqbal Khan ya je Japan ne daga Pakistan a shekarar 2004, tare da matarsa. Ya fara sana'ar sayar da motoci a kusa da Tokyo, inda daga bisani ya koma zuwa birnin Fukuoka da ke makwabtaka.
Lokacin da matarsa ta yi ɓari a shekarar 2009, babu makabartar musulmi a unguwarsa.
"Mun ɗauki gawar a cikin karamin akwati muka sanya shi a cikin mota muka nufi Yamanashi wanda ke da nisan kilomita 1000," in ji Iqbal, yana bayyana irin halin abin da ya faru. "Abokai huɗu ne suka raka ni, mun tafi a mota har har zuwa wajen."
Musulmi da Kiristoci duka na amfani da makabartar Yamanashi da ke tsakiyar ƙasar Japan, har ma da sauran tsirarun addinai na ƙasar da ke da kashi daya na al'ummar ƙasar.
"Na so in kasance tare da matata a irin wannan lokaci na raɗaɗi amma hakan bai yiwu ba," in ji Iqbal. "Abin yana da wahalar gaske."
Cunkushewar titi
Ƙungiyar Dr Khan ta sayi fili kusa da makabartar Kiristoci a Beppu. Mutanen da suka mallaki filin da ke gefensa ba su bayar da 'takardar shaidar kin amincewa' ba amma al'ummar da ke zaune a kusa da wurin da nisan kilomita uku sun nuna rashin amincewarsu.
"Sun ce binne gawawwakin zai gurɓata ruwan karkashin ƙasa da kuma ruwan tafkin da ake amfani da shi wajen ban ruwa," in ji Dr Khan.

Asalin hoton, TAHIR ABBAS KHAN
Babu wani abu da ya sauya a cikin shekaru bakwai, wanda ya tilasta wa mambobin al'umma su nemi wasu hanyoyi.
Dr Khan ya ce wasu musulmi 'yan ci-rani sun mayar da gawawwakin 'yan uwansu gida. Ya ƙara da cewa yayin da wasu da ke fama da ciwon kansa, wadda ake hasashen za ta yi ajalinsu, ke yanke shawarar komawa kasashensu na karshe kafin mutuwa ta riske su.
Sai dai, jigilar gawawwaki zuwa gida ya ƙunshi tanadin cikakkun takardu kuma babu makawa yana jinkirta binne mutane.

Asalin hoton, RYOKO SATO
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan ba zaɓi ba ne ga Ryoko Sato, ƴar ƙasar Japan da ta musulunta, wanda kuma ke zaune a tsibirin Kyushu.
"Wasu suna cewa, ku koma ƙasarku idan ba ku bi dokokin Japan ba. Wasu kuma sun ce a kai gawar zuwa ƙasashe maƙwabta inda ake bayar da izinin binnewa," in ji ta.
"Mijina yana zaune a ƙasar Japan fiye da rabin rayuwarsa. Ya samu shaidar zama ɗan Japan da daɗewa kuma yana biyan haraji kamar yadda haifaffen Japan ke yi.
"Zuriyarsa za ta ci gaba da zama a Japan to a ina kake ganin ya kamata gawarsa ta kasance bayan mutuwarsa?"
Sato ta ce "batun al'ada" shi yake adawa da binne mutane.
"Wasu mutane suna tunanin binnewa kamar wani abu ne mai ban tsoro ko da yake ba sabon abu ba ne cikin al'ummomi da suka gabata a Japan," in ji Sato.
Ta halarci wajen ƙona gawawwaki da dama amma ta kuduri aniyar cewa tana son a binne ta ne idan ta rasu.
"Idan ana kiran batun binnewa da son rai, akalla bari in zama mai son kaina."
Amma Shinji Kojima, kwararre a fannin ilimin zamantakewa a Jami'ar Ritsumeikan Asia Pacific, jami'a ɗaya da Dr Khan yake, ya ce dalilan suna da sarkakiya. Ya yi bincike kan lamarin kuma ya shawarci ƙungiyar Musulmi ta Beppu.
Dakta Kojima ya shaida wa BBC cewa "Batun a nan shi ne ba wai ko kai musulmi ne ko akasin haka ba. Sanin yadda siyasar al'ummar yankin ke aiki da samun sahihiyar hanyar sadarwa ko haɗin kai ne ke tabbatar da sakamakon."
"Yawancin mutane, kama daga Jafanawa waɗanda ba musulmi ba, sun fuskanci adawa a tarihi."
Samun mafita
Dr Khan ya ce akwai makabartu na Musulmi 13 a Japan, wanda ya kunshi wani sabo da aka samar a baya-bayan nan a birnin Hiroshima, mai tafiyar sa'a uku.
Iqbal ya raka masu makoki zuwa wurin. "Hiroshima na da dukkan abubuwa da muke buƙata. Muna da wuraren samun ruwa domin wanke jikunanmu kuma al'ummar yankin na samar mana da abinci," in ji shi.

Asalin hoton, TAHIR ABAS KHAN
Dr Khan ya yi kira ga mambobin majalisar dokokin ƙasar, ma'aikatun da abin ya shafa da kuma hukumomi da su taimaka wajen magance matsalar.
Yanzu, hukumomin yankin sun samar da fili mai wuraren binne mutane 79 ga al'ummar Musulmi a Beppu.
"Wannan ba wai batun addini ba ne, hakki ne na ɗan'adam," in ji shi. "Ba mu tambayar wani abu a kyauta. A shirye muke mu biya, sai dai inda matsalar take shi ne samun izinin binnewa."
Ya ce sauran ƙananan al'ummomi irin Yahudawa da kuma Kiristoci ƴan ci-rani daga Brazil su ma suna fuskantar kalubale.
"Mafitar da ta dace ita ce samun makabartar addinai daban-daban a faɗin Japan."
Sai dai, da wuya gwamnatin ƙasar da ta shiga cikin lamarin ganin cewa ta bar wa hukumomin yankin su magance matsalar wanda har kawo yanzu suka kasa.
Amma Dr Khan ya ce ba zai hakura ba. "Ba za mu ƙona gawa ba. Ba za mu yi hakan ba. Za mu yi duk abin da ya kamata wajen binne gawawwaki."










