Mataki uku da gwamnonin PDP suka ɗauka a taron da suka yi

Asalin hoton, Bauchi State Government
Yayin da babbar jam'iyyar a dawa ta PDP a Najeriya ke ƙoƙarin ɗinke ɓaraka da rashin jituwa a shugancinta, kungiyar gwamnonin jam'iyyar ta ɗauki wasu matakai.
A taron da suka gudanar ranar Talata a Abuja ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar, Sanata Bala Mohammed, sun yanke shawarar ɗage taron kwamatin gudanarwa na ƙasa da aka tsara yi ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba.
PDP ta kwana biyu tana fama da rikici da kuma yunƙurin gano bakin zaren. A ranar 14 ga watan Oktoba ƙungiyar gwamnonin ta yi irin wannan zama tare da samar da maslaha bayan ɓangarori biyu a jam'iyyar sun dakatar da juna.
Tun da farko, wani ɓangare ya sanar da dakatar da sakataren watsa labarai na ƙasa na jam'iyyar, Debo Ologunagba, da mai ba da shawara kan harkokin shari'a, Kamaldeen Ajibade.
Sai kuma wani ɓangaren ya sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar na riko, Umar Damagun, tare da naɗa Yayari Mohammed a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Bayan taron ne kuma gwamnonin suka sanar da soke dakatarwar da aka yi wa Damagum da ma sauran waɗanda aka dakatar baki ɗaya, sannan suka buƙaci kowa ya koma muƙaminsa a cigaba da aiki.
A wannan karon, gwamnonin sun cim ma matsaya uku da ɗaukar matakai kan batutuwa kamar yadda wata sanarwar bayan taro ta nuna:
Na farko: An ɗage babban taron kwamitin gudanarwa na ƙasa wato National Working Committee (NWC) na jam'iyyar, wanda aka shirya gudanarwa ranar 24 ga watan Oktoba.
Yanzu sun amince a gudanar da taron ranar 28 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Na biyu: An ɗauki matakin ɗage taron ne domin bai wa jam'iyyar damar gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.
Suna fatan "'yan jam'iyyar za su haɗa ƙarfi da ƙarfe don samun ƙarfin kada jam'iyyar APC mai mulki a jihar", in ji sanarwar.
Na uku: Taron ya yi kira ga mambobin jam'iyyar su hada kai domin tunkarar ƙalubalen da suke fuskanta na "ƙoƙarin raba kan su da marassa kishin cikinsu ke yi".
A cewarta, taron ya kuma nemi 'yan jam'iyyar "su guje wa yin kalaman da za su iya kawo matsala a shirin PDP na ci gaba da zama babbar jam'iyyar adawa da kuma shirin ƙwace mulki a 2027 daga hannun APC".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Baya ga gwamnonin, taron dai ya samu halartar 'yan kwamitin amintattu na jam'iyyar, da kungiyar tsofaffin gwamnonin jam'iyyar da kuma shugaban 'yan jam'iyyar a majalisar wakilai.
Wannan na zuwa ne bayan rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP ya ɗauki sabon salo, musamman yadda Ministan Abuja Nyeson Wike da ke fafata neman iko da gwamnonin jam'iyyar a jihohinsu.
Ko a makon nan, bangaren Wike sun yi dirar mikiya jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar, kuma wasu 'ya'yan jam’iyyar a jihar suka nuna goyon bayansu gare shi sakamakon shirinsa na tallafa musu da kuɗaɗe da kuma kayan abinci a ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Masu sharhi kan lamuran siyasa kamar Farfesa Kamilu Sani Fage na ganin alamu sun nuna Wike yana so ne gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a PDP a zaɓen 2027.
"Saboda haka suna neman wanda zai mara masa baya ne daga arewa domin suna so a mayar da takarar PDP kudancin Najeriya," in ji shi.










