Shirin sirri na mayar da wasu ƴan Afghanistan Birtaniya ya samu cikas

Asalin hoton, SOPA Images via Getty Images
Dubban ƴan Afghanistan ne suka koma Birtaniya ƙarƙashin wani tsari na sirri, wanda aka kafa bayan da wani jami'in ƙasar ya saki bayanan sirrinsu bisa kuskure.
A watan Fabrairun 2022, aka fallasa bayanan sirrin ƴan Afghanistan kusan 19,000 waɗanda suka nemi buƙatar komawa Birtaniya bayan da Taliban ta ƙwace iko da mulki.
Gwamnatin Birtaniya da ta gabata ta gano batun fallasa bayanan a watan Agustan 2023, lokacin da wasu daga cikin bayanan suka bayyana a shafin Facebook.
An sake samarwa mutanen da aka saki bayanansu wani matsuguni na daban watanni tara bayan faruwar lamarin, inda ƴan Afghanistan 4,500 suka isa Birtaniya zuwa yanzu.
Ana sa ran wasu dubbai kuma na hanya, sannan an kiyasta cewa za a kashe kuɗin da ya kai dala biliyan 1.1.
Sai dai an ɓoye wurin da za a mayar da su bayan da gwamnatin Birtaniya ta samu umarni daga kotu.
Sai dai an ɗage hakan a yanzu - ga abin da muka sani kan tsarin, da bayanan da aka fallasa da kuma abin da ya biyo baya.
Ƴan Afghanistan da ke fuskantar barazana
Bayan karɓe iko da Kabul da Taliban ta yi a watan Agustan 2021, an bayyana cewa mutanen da suka yi wa gwamnatin Birtaniya aiki lokacin rikici a Afghanistan na cikin barazanar aiwatar da hukuncin kisa a kansu - ko kuma yin ramuwa - daga wajen Taliban. Har yanzu ana ganin irin wannan barazana tana nan.
Gwamnatin Birtaniya ta kirkiro da wani tsari na mayar da waɗanda ke cikin barazana zuwa Birtaniya.
Lamarin ya kai ga ɗiban ƴan Afghanistan 36,000 zuwa Birtaniya, sai dai an soki tsarin a shekarun da aka kaddamar da shi, inda wani kwamiti da gwamnatin Birtaniya ta kafa don duba lamarin ya gano cewa abu ne na "bala'i" da kuma "yaudara".
Yawancin waɗanda suka yi aiki da Birtaniya a fannoni daban-daban - ko kuma iyalansu - na can a Afghanistan har yanzu, kuma suna cikin fargabar abin da zai faru da su.
Bayanan da aka fallasa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An fallasa bayanan ne a watan Febrairun 2022, lokacin da wani jami'i da ke aiki da dakarun Bitaniya na musamman mai shelkwata a Landan, ya aika sakon email bisa kuskure ɗauke da bayanan ɗaukacin mutanen da suka nemi buƙatar koma Birtaniya ta wannan tsari.
Jami'in da ya fallasa bayanan bisa kuskure na ƙoƙarin taimakawa wasu mutane ƴan kalilan da suka nemi buƙatar komawa Birtaniyar, lokacin da ya aika ɗaukacin bayanansu zuwa ga wani a Birtaniya.
Daga nan ne wanda aka tura wa bayanan ya ƙara yaɗa su - suna ɗauke da sunaye, wurin zama har da bayanai kan wasu iyalai da ke cikin barazanar Taliban - zuwa ga wasu mutane, ciki har da mutane a Afghanistan.
Wannan ya kunshi sojojin Afghanistan 600 da wasu iyalai 1,800 waɗanda ke Afghanistan.
Gwamnatin Birtaniya ba ta da masaniyar fitar bayanan har sai Agustan 2023, lokacin da aka gargaɗe su cewa wani mai amfani da shafin Facebook na wallafa bayanan da aka fallasa a shafukan sada zumunta.
A 2024, wani alkali a Birtaniya ya yanke hukuncin cewa "zai iya yiwuwa" cewa wasu daga cikin mutane da suka kalli bayanan da aka fallasa a wani shafin Facebook "masu kutse ne daga Taliban ko kuma suka yi maganar da waɗanda ke alaƙa da Taliban".
An ɓoye batun fitar bayanan na tsawon shekaru uku, kuma an faɗa wa mutanen da aka fitar da bayanansu ne ranar Talata.
Gwamnatin Birtaniya ba ta tabbatar da cewa ko an hukunta jami'in da ya fallasa bayanan ba, inda wani mai magana da yawun gwamnatin ya ce ba za su ce uffan kan mutane ba.
Jami'ai sun ce mutumin ba ya kan mukaminsa lokacin da ya saki bayanan.
Tsarin mayar da ƴan Afghanistan Birtaniya na sirri

Asalin hoton, SOPA Images via Getty Images
Bayan fallasa bayanan, gwamnatin Birtaniya ta kirkiro da wani tsari na sirri, domin ɗaukar waɗanda ake da bayanansu zuwa Birtaniya - wanda aka saka wa suna Afghanistan Response Route.
Wannan ya laƙume kuɗi da ya kai dala miliyan 535 zuwa yanzu - kuma ana sa ran za a ƙara kashe dala miliyan 535 zuwa dala miliyan 603.
Kusan ƴan Afghanistan 4,500 ne suka koma Birtaniya zuwa yanzu, sannan yayin da aka rufe tsarin yanzu, za a bai wa waɗanda aka yi wa alkawarin komawa Birtaniya damar yin haka.
Wannan na nufin cewa, ƙarin ƴan Afghanistan 2,400 ne za su koma Birtaniya.
Hana fallasa bayanai
A 2022, tsohon sakataren tsaron Birtaniya Ben Wallace, ya nemi buƙata, kuma ya samu a wajen kotu - wadda ta ba da uamrnin hana fallasa ko ƙwarmato bayanan ƴan Afghanistan waɗanda ke karkashin tsarin.
Wallace ya kalubalanci cewa dole ne a ɗauki tsauraran matakai domin bai wa gwamnati lokaci ta yi "duk abin da ya kamata domin taimakawa waɗanda aka saka cikin barazana ta hanyar fallasa bayanansu".
Hana fallasa bayanan ya sa tsarin ya ɓoye (bayanan da aka fallasa) har na tsawon shekara uku da rabi, inda sai zuwa ranar Talata da aka ɗage hakan.
Wannan irin umarni yana cike da tsarkakiya saboda tasirin da yake da shi kan kafofin yaɗa labarai da ke ruwaito batun, kuma alkalin da ya ɗage batun hana fallasa bayanan ya ce ya yi haka ne saboda lamarin ya janyo "gagarumar matsala wajen ƴancin faɗan albarkacin baki".
Neman buƙatar komawa Birtaniya cikin 'gaggawa'
Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta buƙaci soke batun neman izinin komawa ƙasar da wani ɗan Afghanistan ya yi, bayan da ya wallafa wasu daga cikin bayanan da aka fallasa a shafin Facebook, kamar yadda BBC ta gano.
Mutumin ya wallafa sunayen mutum tara cikin waɗanda aka fallasa bayanansu, sannan ya kuma ce zai saki sauran daga baya.
Hukumomin Birtaniya sun bi diddigin mutumin inda suka buƙaci ya sauke bayanan, tare da yi masa tayin cewa za a sake duba bauƙatar da ya yi na son komawa ƙasar cikin gaggawa.
BBC ta gano cewa mutumin yana Birtaniya a halin yanzu, bayan sake amincewa da buƙatarsa ta son koamawa ƙasar da aka yi. An yi imanin cewa ba a tuhumarsa da aikata wani laifi kan abin da ya yi.
Majiyoyin gwamnati kusa da tsarin sun shaida wa BBC cewa mutumin ya yi amfani da batun wallafa bayanan mutanen ne domin samun damar shiga Birtaniya.
Ma'aikatar tsaron ta ki cewa uffan kan abin da mutumin ya aikata har ma da komawarsa Birtaniya.
Ta kuma ki cewa komai kan waɗanda ke fuskantar barazana daga Taliban bayan fallasa bayanansu tsawon shekaru da faruwar lamarin.
Sakataren tsaron ƙasar John Healey ya faɗa wa BBC cewa "ba zai iya tabbatar wa ba" cewa ko babu ɗan Afghanistan da aka kashe sakamakon fallasa bayanan, sai dai ita ma Taliban babu wani ƙarin bayani da ta yi.







