Yaushe za a magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, wanda ya nuna cewa an samu ƙaruwar rashin aikin yi a ƙasar da kashi 5.4 a wata ukun farko na shekarar 2024, na ci gaba da ɗaga hankalin mutane a faɗin ƙasar.
Sabon rahoton na nufin an samu ƙarin mutum 300,000 a kan miliyan biyar ɗin da ake da su a ƙarshen shekarar 2023 marasa aikin yi a faɗin ƙasar, wanda hakan ya haifar da cecekuce tsakanin mutane a daidai lokacin da ake fama da tsananin rayuwa a Najeriya.
A watan Agusta ne matasa a Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa, inda dubban matasa suka fito titunan ƙasar suna nuna rashin jin daɗinsu kan yadda tattalin arzikin ƙasar da nasu tattalin arzikin ya taɓarɓare.
Bayanan da hukumar ta fitar sun nuna cewa birane ne suke da kashi 6 cikin 100 na marasa aikin yi, inda kuma yankunan karkara ke da kashi 4.3 kamar yadda rahoton hukumar ya nuna a ranar Talata.
Rashin aikin yi na nufin adadin waɗanda ba su da aikin yi, sannan suke fafutikar neman aikin yin.
Me ke jawo rashin aikin yi a Najeriya?
Sanannen abu ne matasan Najeriya na fama da rashin aikin yi, lamarin da ke ƙara fitowa fili duk lokacin da aka fitar da gurbin ɗaukar ma'aikata a ƙasar.
Sai dai a lokuta da dama, wasu masu aikin yin, sukan shiga cikin masu neman wani aikin, wanda hakan ya sa yake da wahalar gaske gane wanda ba shi da aiki da asalin zauna gari banza, duk da cewa a ƙididdigar ta NBS, akwai rahoton waɗanda suke aikin da ba shi biya musu buƙatu.
BBC ta tuntuɓi masanin tattalin arziƙi kuma malami a kwalejin kimiyya da fasaha a Kano, Malam Lawal Habib Yahaya, wanda ya ce akwai abubuwa da dama da ke jawo matsalar rashin aikin yi a Najeriya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Mafiya girma su ne yadda tattalin arzikin ƙasa yake samun koma-baya. Idan tattalin arzikin ƙasa yana taɓarɓarewa, sannan masana’antu na samun cikas, ko dai suna durƙushewa ko samun cikas wajen sana’anta kayayyakin da suka dace wato waɗanda ake buƙata," in ji shi.
"Sannan ba su sayar da kayayyakin da suka yi a cikin gida sai dai su kai ƙasashen waje. Irin waɗannan matsaloli dole za su sa kamfanoni su rage ma'aikata."
Masanin ya ƙara da cewa rashin albashi mai kyau ma na taimakawa wajen ƙara rashin aikin yi.
"Idan ya kasance albashin da ake biya na aikin ya yi kaɗan matuƙa, wato za a iya cewa aikin ya yi arha da yawa ke nan. Idan aka ce ya yi arha, ana nufin albashin bai taka kara ya karya ba, zai sa ma’aikata da yawa su gwammace gara rashin aikin yi," in ji shi.
Ya kuma bayar da misalin yadda ma'aikata a biranen Najeriya da dama kamar Abuja Abuja suke ajiye aiki saboda yadda albashinsu yake ƙarewa a kuɗin mota kawai, ba ma a maganar kuɗin cin abinci da sauran buƙatun rayuwa.
"Wannan ma yana jawo rashin aikin yi domin mutane suna barin aikinsu saboda aikin ba shi biya musu buƙata. Wato yana da kyau a fahimci cewa rashin aikin yi da tattalin arziki tare suke tafiya. Shi ya sa cigaban ƙasa yake dogara kacokam a kan yanayin yadda mutane ke samun aikin yi sannan suke samun biyan buƙata daga aikin, sannan masana'antu su riƙa sana'anta kayayyaki."
Masanin ya ce hakan ne zai haɓaka tattalin arzikin ƙasar, "kayayyaki su wadata, farashi ya sauka, sannan rayuwa ta gyaru".
Yaushe za a fita daga wannan tarkon?
Yawanci idan ana batun matsala, hankali yakan koma ne kan batun yadda za a iya magance ta.
Game da yadda za a magance matsalar rashin aikin a Najeriya, Malam Lawal Habib Yahaya ya ce ya danganta ne da yanayin shugabancin ƙasar.
A cewarsa: "Waɗannan abubuwan da na faɗa a baya, su ne ya kamata a gyara. Ya kasance albashin da ake biyan ma’aikata yana ƙaruwa, wato ya zama kuɗin da suke samu yana biya musu buƙata.
"Sannan a inganta tattalin arzikin ƙasar, ya zama ana sana'anta abubuwa. Idan tattalin arziki ya inganta, dole komai zai inganta."
To ko a ɓangaren ƴan ƙasa akwai abin da ya kamata su yi? Masanin ya ce yawanci matsalolin rashin aikin na da alaƙa ne da taɓarɓarewar tattalin arziki, kuma nauyin yana kan gwamnati ne.
"A tare suke tafiya. Idan ɗaya ya ƙaru, ɗayan ma zai ƙaru. Su ƴan ƙasa kamar raƙumi ne da akala," in ji shi,
"Idan gwamnati ta yi abu mai kyau masana'antu za su sana'anta kayayyaki, sannan sauran harkokin tattalin arziki za su haɓaka."











