Mai albashin N150,000 da ya ajiye aiki a Abuja saboda tsadar kuɗin mota

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan sanar da ƙarin sabon farashin kuɗin man fetur a Najeriya da kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya yi, ƴan Najeriya ke ta kokawa dangane da sabon matsin rayuwa da suka sake tsunduma a ciki.

NNPCL dai ya sanar da ƙarin naira 280 a kan farashin litar mai wadda a baya ake sayar da kowacce a kan naira 617, inda yanzu sabon farashin ya koma naira 897 a kowace lita.

Babu ko shakka sabon ƙarin ya shafi yanayin farashin zirga-zirgar jama'a, inda wurin da a baya mutum zai je a kan naira 500 a Abuja yanzu sai an biya naira 700 zuwa 750.

'A yanzu kam na haƙura da aure'

Nuhu Aminu Nuhu, injiniyan gine-gine ne a Abuja wanda ya yanke shawarar ajiye aikinsa da wani kamfani sakamakon tsadar kuɗin mota da ya lissafa.

"Ina zaune a Katampe da ke Abuja inda kullum nake tafiya zuwa Apo Resettlement. A kullum ina kashe naira 2,500 ban da kuɗin abinci. Kuma albashina bai wuce 150,000 ba a wata. Idan ka lissafa sai ka ga to nawa zai rage maka bayan kuɗin mota da na abinci'', in ji shi.

"Hakan ne ya sa kawai na gwammace ajiye aikin nan na nemi mafita. Allah ya sa ma yanzu ba ni da aure kuma na haƙura da yin aure bisa la'akari da abin da ke ƙasa." In ji Injiniya Nuhu.

Dangane da sana'ar da injiniya zai yi nan gaba ya ce "ni yanzu zan nemi karatu da aiki a ƙasashen da tsadar rayuwarsu ba ta kai tamu ba. Na san dai kowace ƙasar na fama da tsadar rayuwa amma tamu ta daban ce."

'Na ajiye aikina, zan nemi wani a intanet'

Shi ma Injiniya Ashraf wani mai aikin ne a kamfanin gine-gine a birnin na Abuja wanda ya ajiye aikinsa saboda tsadar man fetur a makon nan.

"Albashina naira 80,000 ne. Ina zama a Apo sannan ina zuwa aiki a Mabushi kullum. Ka ga idan ka duba sai ka ga kwata-kwata babu riba.

Da BBC ta tambayi Ashraf ko me zai yi tunda ya daina aikin da yake yi yanzu? Sai ya ce "ai akwai ayyukan da mutum zai yi yana zaune a gida. Tunda ni injiniyan gini ne akwai damarmaki a kafafen sada zumunta da za ka samu aiki ka yi a biya ka ba tare da ka hau mota ba."

Ya kuma ƙara da nuna takaicinsa cewa "yanzu a Najeriya sai ka rasa ina hankalin shugabanninmu ya tafi. Kullum al'amarin ƙara ƙwace musu yake yi."

Me hakan ke nufi ga ƙasa?

..

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Lawal Habib, malami ne a tsangayar nazarin ilimin tattalin arziƙi a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano, wato Kano Polytechnic, kuma mai sharhi kan harkokin tattalin arziƙi ya shaida wa BBC cewa " wannan babbar barazana ce ga ƙasa saboda duk lokacin da aka ce abin da zai ragewa ma'aikaci bayan biyan haraji da kuɗin sufuri bai kai abin da zai samu sauran abubuwan buƙatar rayuwa ba kamar abinci da sauransu to akwai matsala.

Masanin ya ƙara da lissafa wasu illoli da ajiye aikin ƙananan ma'aikata kamar haka:

  • Cin hanci da rashawa za su ƙaru
  • Za a samu ƙarin marasa aikin yi
  • Tattalin arziƙin ƙasa mai alaƙa da ayyukan yi na ƴan ƙasa zai yi ƙasa
  • Ayyukan ɓata-gari da na ta'addanci za su ƙaru

Sai dai kuma ya bayar da shawarwari kamar haka;

  • Ya kamata gwamnati ta yi wani abu dangane da farashin mai
  • Gwamnati ta daina ƙara haraji ga kowa da kowa maimakon masu arziƙi
  • Sannan gwamnati ta ɗauki matakan sama wa naira daraja
  • Gwamnati ta fito da hanyoyin samar da ƙere-ƙere a cikin gida domin fitarwa waje

Rahotanni dai na nuna cewa ma'aikata da dama musamman masu ƙaramin aiki sun haƙura da ayyukan da sai sun hau abin hawa za su je.

Da dama sun sauya ayyukan da ko dai wanda za su yi a unguwanninsu ko kuma ayyukan da za a yi ta intanet, inda kuma wasu ma kan ajiye ayyukan nasu ba tare da sanin me za su yi ba.