Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya: Wane ne talaka?

Bayanan bidiyo, Ranar yaki da talauci

Alkaluman hukumar ƙididdiga ta Najeriya na baya-bayan nan na cewa akwai mutum miliyan 133 da ke fama da talauci a kasar, kimanin kashi 63 na adadin 'yan Najeriya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da NBS ta wallafa a kan talauci ta fuskoki da yawa a shekara ta 2022.

A cewar rahoton, idan aka duba fuskokin da ake la'akari da su, na talauci akwai rashin ingantaccen ilimi da tsaftar muhallali da tsaftataccen ruwa da wutar lantarki da kula da lafiya da sauransu.

Rahoton ya ce adadin talakawan da ke arewacin Najeriya ya kai miliyan 86.1, yayin da miliyan 47 suke a kudancin ƙasar.

r

Yadda ake gane talaka

r

Asalin hoton, Google

A 2018, Bankin Duniya ya ce duk mutumin da ba zai iya kashewa kansa $1.90 kwatankwacin naira 2,500 to yana cikin talakawa.

Amma a wani sabon rahoto da ya wallafa a 2022, ya ce an sake fasalin ma'aunin talaucin tun bayan ɓarkewar annobar korona da kuma yaƙin Rasha da Ukraine.

Kuɗaɗen ƙasashe da dama darajarsu ta ƙarye, an samu ƙarin yunwa da talauci dalilin waɗannan abubuwa biyu.

An samu hauhawar farashin makamashi tsadar abinci da kuma kuɗaɗen da ake kashewa wajen yaƙi da sauyin yanayi.

A watan Nuwambar 2022, Bankin Duniya ya sauya ma'aunin zuwa $2.15 kwatankwacin wajen naira 3,500, wanda hakan ke nufin duk wanda wai iya kashewa kansa wannan kuɗi na cikin talakawa.

Ya zuwa 2019 akwai matalauta miliyan 648 a faɗin duniya, wani adadi mai sare gwiwa, a yaƙin da ake yi da talauci a duniya.

r

Dabarun kaucewa talauci

r

Masana na cewa talauci abu ne da ba za a iya kauce masa ba baki ɗaya, kamar yadda ba za a iya kawai da arziƙi da wadata ba cikin al'umma.

Sai dai suna bayar da wasu 'yan shawarwari da za su iya rage tsunduma cikin matsanancin talauci.

Na farko dai dole ne ku kauce wa kashe kudi kan abubuwan da ba su zaman wajibi ba.

Wani sabon dinkin mako-mako, da ciye-ciyen da babu gaira babu dalili,dole ne a bar shi. Idan mutum ba hakan ba, to ko nawa mutum ke samu ba za su zauna ba.

Na biyu kuma, a kama sana’a, idan an yi rashin sa'a kana cikin waɗanda ba su aikin yi, a nemi sana’ar yi komin kankantarta a fara.

A bangaren gwamnati kuwa, dole ne ta fito da wasu tsare-tsare da za su rage yawan kudin da mutane ke kashewa a kullum, kamar rage farashin kayan masarufi da kuma tsadar zirga-zirga, da kuma samar da ayyukan yi ga al'uma.